💔❤❤❤❤❤💔
*ƘUNCIN RAYUWAH*
💔❤❤❤❤❤💔MALLAKAR:👇
*SAINAH Ummun meenal ce🌸✍🏻**WHATPADD: Ummunmeenal*
*Intelligent Writer's Associations✍.*
*{Onward 2gether}**DEDICATED TO: BILLY S FARI*
*Da sunan Allah Mai rahma mai jin ƙai.*
*Ina roƙon Allah (S.W.A) ya sanya abin da zan rubuta ya zama alkhairi da alfanu atsakanina ni da ku*_Kuna ina masoyan Sainah? Gani na sake zuwar muku cikin wani salo na daban, labarin da yake tafe da ƙuntatawa, sadaukarwa, haɗe da yaudarar da ke tarwatsa ko wani sa rai da tabbacin Nagartar ɗa Namiji, acikin rayuwar mace. Maza ku ɗauko faya-fayan da zaku baja kolinku acikin labarin, ku kuma magantu acikin sa da ra'ayin ku. Ni kuma zan ajiye muku Kalmar *GIRMAMAWATA,* acikin ko wani shafi._
Na sadaukar da wanan safin kyauta gareki UmNass marbuciyar *HANYAR BAUCHI* ubangiji Allah yasaka maki da mafificin Alkhairi Allah ya iya maki abunda baki iyawa kisani *SAINAH* natare dake adukkan shafin da rayuwa zata buɗe maki🤝🏻
*BABI NA FARKO* (page 1)
Yarinya ce wadda ashekaru bazata wuce shekara sha tara (19) aduniya ba, duƙe gaban mahaifiyar ta cikin shesshekar kuka take faɗar "Woyya Allah na! Ummi nah karki kashe ni, ki tsaya ki saurari kalamaina koda ba zaki yarda da abun da baki na zai furta ba, amma ina so kiji da kunnen ki, kar kiga laifina ni kaɗai daga baya kiyi dana sani."
"In saurari mi *SADEEYAH* ? kin riga da kin zubar da mutuncin gidan nan da naki a idon duniya, wallahi Allah baki da abun da zaki cemin na yarda dake, Uhm dana sani kuma ta nawa kike buƙatar nayi? Bayan kin zama ta farko data zo da mummunan sauyi agaremu." share hawayen da suka wanke mata fuska tayi, cikin muryar ta da take futa da ƙunci taci gaba da magana "Kitafi SADEEYAH na yafeki duniya da lahira." tana gama faɗar haka ta yada iccen dake hannun ta tashige ɗaki cike da danasani akan ƴarta Sadeeya.
kuka take wiwi tana faɗar," Kiyi haƙuri Ummi nah! wallahi Allah nayi nadamar tafka wannan babban kuskure mafi ƙƴama damuni arayuwa ta, kar ki gujeni, kece abu mafi muhimmanci da soyuwa agareni, idan kika guje ni wallahi rayuwa ta zata ƙara tagayyara fiye da wadda nake ciki yanzu." faɗuwa ƙasa tayi tana shure-shure tamkar wata zautacciya, tun ana jiyo sautin kukan ta har muryarta ta dashe.
Da sauri ta banko ƙofar ɗakin cikin tsananin fushi take faɗar, "Baki ga komi ba Sadeeya, yanzu kika fara yin kuka. Dan haka Sadeeya ki tashi kibar gidan nan tun kafin in zamo ajalinki, ko kuma in tsine maki kibi duniyar da hujja, tunda dama ita kikasa agaba."Cikin tsanani firgici da faɗuwar gaba ta ɗago fuskar ta wadda take wanke da hawaye, tana kallon Mahaifiyar ta mafi soyuwa agareta tace "Ki taima keni, ki taimaki rayuwata Ummi nah! Ki cire kalmar tsinuwa agare ni, ki nema min yafiya da sassaucin wahalar da kike hasko min agaba. Wallahi zan bar gidan nan yanzun, bazan iya jure kalmar aibatawa daga gare ki ba, balle kuma kalmar tsinuwa agare ni, domin daki tsineman na ƙara lalewa gara nabar ki batare da kin furta kalmar la'anta agareni ba." tana gama faɗar haka tamiƙe tare da kallon mahaifiyar ta tace," Ina sonki Umminah! Ina matuƙar ƙaunar ki azuciya tah! Kece jigon ko wani jin daɗi da walwalata, amma yau dole tasa zan rabu dake, ina roƙon Allah ya sanyaya miki zuciyar ki, ya baki ikon aika min da Addu'ar kariya da shiriya daga gare shi." tana gama faɗar haka tafice aguje daga gidan.
Uwa da ɗah sai Allah, tana ganin fitar SADEEYAH tuni ta zube a ƙasa tana kuka tamkar ƙaramar yarinya. Badan dole ba mi zai sa ta yanke alaƙa da tausasawar dake tsakanin ta da ƴarta mafi soyuwa azuciyar ta, hannayenta ta ɗaga sama cikin murya mai rauni ta fara Addu'a "Ya Allah ka kare min Sadeeya aduk inda zata, Allah ka zama gatan ta, ka kare ta da aikata wata sabuwar baɗaƙala acikin duniyar ta." tana ƙarasa faɗa taci gaba da kukan ta.
YOU ARE READING
KUNCIN RAYUWAH
Short StoryKuna ina masoyan Sainah (Ummun meenal)? Gani na sake zuwar muku cikin wani salo na daban, labarin da yake tafe da ƙuntatawa, sadaukarwa, haɗe da yaudarar da ke tarwatsa ko wani sa rai da tabbacin Nagartar ɗa Namiji, acikin rayuwar mace. Maza ku ɗauk...