*KUNCIN RAYUWAH*
_Kukan yah'mace😢_*Sainah✍*
*DEDICATED TO:BILLY S FARI*
*BABI NA BIYU*
Cikin matsanancin tashin hankali marar misaltuwa take duk'e tana zubar da hawaye masu d'acin gaske Wanda kullum aikinta kenan gamida da nasani marar iyaka, firgigit ta zaro ido gamida saurin tashi tana goge idanuwanta sakamakon tab'atan da akai ,
Kallonta take sosai gamida sa gudan hanninta tana goge Mata hawayen dake zuba daga idonta kana tace'," kuka kike ko anty NADAH? saurin girgiza Kai tai alamun aa
Murmushi tasaki gamida juya baya tace," anty NADAH kenan kinsan iya tsawan lokacin da nazo nan na taddaki kina kuka ,wai miyasa kika kasa yarda dani anty NADAH? Plx and plx anty NADAH kitaimaka kivani labarinki koda zan iya baki wata gudunmawa mana, kodai baki yarda dani bane
Da Sauri nada tajawo hannunta gamida fad'ar sorry azrah bawai naqi baki labarina bane ,labarina babu abinda ke cikinshi illah _*BAKIN CIKI GAMI DA ZAZZAFAR KUNCIN RAYUWA*_ Dana Shiga ina tsoran infad'a maki halin dana jefa kaina ne kema kizo kitsanan gamida zubar da hawaye
Da sauri wadda takira da azrah da girgiza Kai tana mai zubarda hawaye tace'" Bazan tab'a tsanarkiba anty NADAH, bakomi azrah namaki alqawarin Insha Allahu duk sadda Bani aikin kome ke kuma baki zuwa skull zanbaki labarina mai cike da tarin haushi da bak'inciki zakisan wacece ni cewar NADAH
Kai azrah ta girgiza alamun gamsuwa gamida kama hannunta tace" tun d'azu umma ke kiranki taji shiru shine nalek'o inga ko kina baya kina tunanin da kika saba kuma ko da nazo na taddaki acikin abinda nai tunanin hakan gamida sakin murmushi itama murmushin nada tasaki gami da fad'ar," Natuba nabari agafarceni ,dariya azrah tasaki tace," yanxu dai tai wurin Kiran momy later mahad'e tom ta ansa mata tare da ficewa
Matashiyar matace wadda bazata wuce shekaru 37 aduniyaba zaune saman 3seater kallo d'aya nai ma matar na tabbatar tana cikin daular arzik'i domin ko kayan jikinta abinda kallone gata kyakkyawa sankowa k'in Wanda ya rasa.
Da sallama tashigo gamida duk'awa har k'asa tace Hajiya gani,wani wulak'antaccen kallo taje feta dashi Wanda yai sanadiyyar da nadah ta maida idanu wanta ak'asa, Ina kika Shiga tun d'azu inata kiranki cewar matar da nada takira da hajiya, cikin sauri nadah ta ansa dah inata waje zanyi wanke-wanke ne, tsaki hajiyar taja gamida mik'ewa tace shegiya tsintacciyar mage Wanda haryau bamusan usulintaba," Maza kije kikwaso kayan wankin nan kimaza kije kiyisu kuma 20mnt nabaki ki tabbatar kingama acikinsa inba haka ba yau saikin bar gidan nan tana gama fad'ar haka ta watsa Mata wata wulak'antacciyar harara kana ta wuce
Da sauri ta mik'e gamida sharar kwallah zuwa kwaso wankin jin ance za'akoreta,Wai momy miyasa kikewa nadah haka ne Dan Allah,duk wahalar da take agidan nan har wanki saikin bata baccin akwai masu maki Dan Allah momy kibari ni wallahi banjin dad'in abinda kike mata duk da tana mai aikinki gamida turo baki
Ahlallai azrah nikike gayawa haka akan munafukar yarinyar cen to wallahi kifita idona idan ina ma waccen tsintacciyar Abu tunkafin ranki ya b'aci ,kuka tasaki gamida cewa Bari dady yadawo wallahi saina gayamai tsaki momyn tasaki tace kindad'e baki kigayamai ba munafuka aini saboda kema na keson ma in koreta Dan tunda tazo nan gidan naga kina nanik'e mata ,bazanyi sake talalata mun keba kamar yadda talalata kanta ba Dan da alamu yarinyar kamar wannan tagudo daga gidansu to duk tak'are ba'abin arzik'i ta aikata acenba, Allah yashiryamu azrah tace gamida sakai tafice tana mai jimamin miyasa momy kewa nadah haka
*****
Zaune take taci kwalliya sai zuba k'amshi take, time to time tana duba agogon dake mak'ale acikin tanga meman falon ganin har 11pm tayi tatashi tana sintiri acikin falon gamida addu'a Allah ka karemun mijina aduk inda yake, Allah kasa duk inda yake yanzu Yana cikin farinciki da k'oshin lafiya, Allah kadawomin dashi lafiya ,sai kuma tafara zubar da hawaye tare da furta Allah kasawa mijina *SONAH* Koda kad'anne acikin zuciyarshi, tana cewa Amin taji alamun bud'e k'ofa da sauri tanufi wajenshi gamida fad'arr sai dai tun kafin ta ida k'arasawa taji warin giya ya buge Mata hanci duk da haka ida k'arasawa tai gamida fad'ar sannu da zuwa,wata uwar harar ya zabgamata yace,"mayya kina nan zaune baki barciba ko?kina jirana ke mai maiji
ainaji kina cewa Allah yasa insoki bak'ar munafuka,
sai kuma ya ida isa ga kujera ya zaune Yana mai wani irin kallo Wanda da alamu giyar da yasha tafara aiki ,saikuma yamik'e ya isa ga dining d'in dake shak'e da foodflask da ban daban yana masu kallon tashanci
Matsowa tai kusa dashi tace,"sorry habibi muje Kai wanka kana ,saukar mari taji har guda ukku, banace karki sake cemun habibi waike wace irin mayyace da kink'i fita daga rayuwata sai kuma ya zube asaman kujerar dining d'in hawaye na zuba a'idonshi yace wallahi Billy Bazan tab'a sankiba har inkoma ga mahaliccina Dan Allah kije kicewa Abba kinfasa zama dani da sauri tafara zubarda hawaye tana mai girgiza Kai alamun bazata iyaba ,cikin kuka tace ka gafarceni zayyad wallahi Sanka dashi aka haifeni Bazan iya rayuwa bayan baka ba," Bell taji tako ina yana Shiga jikinta Yana fad'ar wallahi saikin barni tunda ba mahaifa d'aya muka zauna ba Saida yai Mata lilis kana yajefar da bell d'in gamida rarrfawa yai hanyar d'akinshi🌷🌷🌷🌷🌷
_Gani dai acikin sabuwar tafiya mai d'auke da sark'akiya da rashin tabbas da cin amana ta kowane b'angare gamida d'unbin darasi acikinsa.sai dai bansaniba ko hakan yafara tasiri agareku? Idan nasamu kimantawa da dafifi dan ra'ayin kanku zan k'ok'arta na aje maku wannan kalmar ta *GIRMAMAWA* akowane shafi_
#Comment
#Share
#Vote
#IWA*Maman khairat✍*
YOU ARE READING
KUNCIN RAYUWAH
Short StoryKuna ina masoyan Sainah (Ummun meenal)? Gani na sake zuwar muku cikin wani salo na daban, labarin da yake tafe da ƙuntatawa, sadaukarwa, haɗe da yaudarar da ke tarwatsa ko wani sa rai da tabbacin Nagartar ɗa Namiji, acikin rayuwar mace. Maza ku ɗauk...