PAGE THREE

56 7 1
                                    

*KUNCIN RAYUWA*
        _{Kukan yah'mace_}😢

MALLAKAR:👇
*SAINAH Ummun meenal ce🌸✍🏻*

*WHATPADD: Ummunmeenal*

*Intelligent Writer's Associations✍.*
      *{Onward 2gether}*

*Dedicated to: BILLY S FARI*

  '''Ina bawa d'aukacin mabiyana hakuri akan dan tsaikon da ake samu na wannan labarin
  Hakika d'an adam baya rabuwa da uzururruka ko kuma gazawa ta fuskar rayuwa, yau da gobe kuma ta wuce kome.
  Kuyi hakuri akwai ayyuka da yawa akaina anma duk Sadda nasamu time zaku ganni cikin Aminci, Nagode da soyayyarku gareni kusani ina girmama kowace kalmarku agareni.'''

*Page 3*
Yanayin da take wankin kanshi zaka gane cikin sauri takeyin shi" da sauri tajuyo da fuskarta jin antab'ata , "Dariya axrah ta kyalkyale da ita gamida fad'ar," Uwar tsoro daga d'an tabaki harkin tsorata nidai maza juyo intayaki wankin kafin momy tafito, Zaro ido waje Nada tayi tace" rufan asiri inbaso kike yau inbar gidan nan ba tare da hawaye na gangarowa afuskarta, "kallonta sosai azrah tayi sai kuma tasaki murmushi tare da d'an dungurin nadah kana tace uwar kuka kedai kuka baya maki wahala, "murmushi itama nada tayi tace hmmm axrah kenann kana taci gaba da wankinta, "Duk yadda nada taso hana azrah tayata wanki anma tak'i saida ta tayata suna yi suna fira yayin da nadah sai addu'ar zuci take Allah yasa kada momy tafito taga azrah tasa hannu a wankin

   Cikin ikon Allah kuwa harsuka gama momy bata lek'oba, Suna d'aurayar k'arshene azrah tace bari nadawo koda tatafi tana dawowa saigata shak'e da flat da indomie wadda taji kayan had'i sai k'amshi ke tashi

  Gashi Anty nadah kici! nasan bakici komiba kikama aikin nan cewar azrah, "Murmushi nada tasaki gamida fad'ar ayyah my azrah sai da nasha tea kanan anma tunda har hannunki ya girka aidole inci ansa tayi ta zauna tarema suka fara ci sunayi suna fira har wankin ya bushe suka linke kana azrah tace Anty nada na tafi d'aki inyi bacci danni nan ko islamiyya baza niba yau ba. domin yauce ranar alk'warinmu na zaki gayamun wacece KE ,,

    Sosai gaban nadah yafad'i! dajin maganar da azrah tataso mata da',ita anma sai ta fuske karki damu azrah insha Allahu zakiji labarina anma inaso kiman....ke uwar me kike yine har yanzu baki gama aikin Dana sakiba ne? muryar momyce ta daki  dodan kunnan su, "Tuni nada tai gaba hartana tuntub'e
Azrah kuwa gun momynta tai tana xuba mata shagwab'a kai momy kefa kikacemun zagi babu kyau anma gashinan ke kinayi harara ta gallah mata alamun chapter da sukai daxu har yanxun tana fushi da'ita itako azrah tana fahimtar haka saima taci gaba da maqalqaleta tana haba ummana farinciki zuciyatah kiyi hak'uri kinji murmushi kawai momy tayi tajawo hannun azrah sukai gaba abinsu

Billy POV
  Cikin tsananin azaba da radad'in da jikinta ke mata tasamu tamik'e tana d'inshigi idanuwanta babu abunda suke illah xubar da hawaye gamida magana wadda natabba tar da tayi nisa cikin rud,'uwa ,, "Miyasa zakimun haka, Miyasa zaki je inda ba'ara'ayinki, Miyasa zaki tunkari mutumin da yafi tsanarki fiye da kowa da komai aduniya wayyo zuciyatah bakimun adalciba Dan Allah kitaimaka kikawomin mafita tare dasa hannuwanta guda biyu tana dukan kujera sai kuma tai zumbur tamik'e tanufi inda habibinta yabi bayan yagama jibgarta _{Baak'ar soyayya}_ rabbi kaimana tsari da ita Amin

    Koda ta tura d'akin kwance ta taddashi yagama jibga amanshi yana kwance yana sauke ajiyar zuciya ga idanuwan shi sun koma jawur kamar gautah, "Da sauri ta k'arasa wurinshi tare da "tab'ashi tace " Habibi lafiyarka kuwa wani mugun kallo ya jefeta dashi Wanda ya hassadar da kad'awar cikinta anman duk da haka tadaure da niyar k'ara tallaboshi "tuni jijiyoyin wuyarshi suka mik'e  baisan lokacin da ya cafkota ba yajefa akan gado yabi ya danne
   Tuntana kuka tana wuntsila wutsila tana bashi hak'uri har k'arfinta ya k'are saida ya murjeta San ranshi kana yaje fota  abakin k'ofar d'akinshi gamida fad'ar kigodewa Allah yau ba'ad'aure na maki ba fare da rufe ganbun d'akin bamm

    Kuka take sosai gamida rarrafawa tayi hanyar dakin ta domin tsaftace jikinta Dan inda Sabo Billy tasaba da irin wannan rayuwa ta gidan habibinta


             ❣❣❣❣❣
*Inafatan wannan shafin ya k'ayatar daku? Kuyi k'ok'arin ajemun mutunta karku kamar yadda nake aje maku Kalmar girmamawata akoda yaushe ngd*
 

#vote
#share
#comment
#like
#IWA
















*Mamyn khairat✍*

KUNCIN RAYUWAHWhere stories live. Discover now