3💜💚💛💙❤️
Sirrin wasu gayun...
💜❤️💛💙💚® zuwairat (ummumaryam)
3️⃣
Free page
Har suka hau adaidaita aka ajiye Maryam nana bata Kara ce mata komai ba,
"Sai munyi waya..." Maryam ta fada mata Tana sauka daga adaidaita amma ko inda take nana bata kalla ba balle ya amsa mata wai ita she's angry because if what she told her that's absolutely true.A yau kam su sufwan sun samu yar kwanciyar hankali Sanin da akwai abinda family dinsu zasu ci for three to four days, suna zaune a bakin titin unguwar su bayan sallah magrub suna jiran ishai usman yace
"Gobe dai zamu huta da néman aiki kou?.. Tunda muna da yan chanzi a jikin mu..." Mai karasa ba sufwan ya kalleshi yace
"Lallai ma...ai wannan struggle will continue har ranar da Allah ya bamu abinyi..ai in Banda abinka kasan bamu ga zama ba..." Sufwan ya fada idanuwanshi kan titi yana kallon cars dake wucewa,
"Wannan gaskiya né...we're not going to give up har sai mun samu abinyi...and am sure Allah zai taimaka mana..." Habib yafada cikin sanyinmurya, usman dake sauraron su ya kalli wata expensive car dake passing by yace
"Wai are we going to get here?.." Ya fada idanuwanshi kan motar, su sufwan kallon motar da yake kallon sukayi habib yace
"Hmmm da wuya...wayan nan yaya manyan mutane né....ba kowa ke kawowa wannan level ba a rayuwa..wani ma bai Sanin dadin duniya har ya koma ya Allah..." Bai karasa ba sufwan yace
"Kai Allah ya sauwake...we will make it...we will surely make it..." Yafada sounding confident and strong,
"Dazun halin da na tadda mama ya tada min hankali...Wallahi inda bamu dawo da wuri ba da bansan halin da zata shiga ciki ba..." Habib ya fada kaman zaiyi kuka, ajiyan zuciya yana tunanin irin shakuwar dake tsakanin habib da mahaifiyar shi, she cares and advice him, she always pray and appreciate duk abinda ya shigo dashi gidan, amma he's own case is different, mahaifiyar shi na tunanin shi ya Dora kanshi kan talauci, she blames him for all the misfortune dake faruwa a gidan, ko nawa zai kawo bata taba tambayar Ina ya samo shi ba indai zai kawo shikenan, babu adua ko yabo, all he gets is insults and rejection, dazun ma duk Kayan daya Kai bata ajiye mashi abinci ba, when he asked Ina nashi Abincin sai tace
"Nasan kana da sauran kudi nan jikinka da yawa..kaje Chan waje ka sayi abinci kaci..." He was not surprised saboda ba yaune farkon ba, duk sanda ya kawo wani Abu gida tou shi bai samu, sai tace tasan da akwai da yawa ya kawo kadan, he just thankful she brought him into this miserable life, he wish he he will see the day he's mother will open her mouth and bless him, the day she will appreciate him even if it's for a second, har ya mance rabon da ya ga murmushin mahaifiyar shi, the last time he remembered was when he was still growing up amma tunda ya girma ta ke Dora mashi laifin talaucin da suke ciki, Yanzu cikin unguwar ko keke aka saya sai tayi mashi tass wai he's mate are becoming responsible amma Banda shi, kawai yasan shi da abokanshi are suffering amma he suffers more than them saboda hantara da tsana da mahaifiyar shi take nuna mashi, inda bai Kama daita sai yace ba ita ta haifeshi ba saboda the way she treats him is so out of words,
"Hmmmm duniya kenan...wacce ta haifeka ma ta kika saboda talauci balle wasu?.." Yafada cikin sanyinmurya, ahankali usman dake zaune kusa dashi ya dafa shoulder dinshi yace
"Haba ka Bari mana...we will surely make it...babu gudu babu ja baya ...nothing will stop us from making it...ko da kidnapping me mun dingayi..." Yafada in a funny way, duk dariya sukayi, baki habib ya Kama yana kallon wasu yanmata guda hudu da suke wucewa, they all know their faces, yanmatan gidan alhaji Ibrahim né, duk sun fita daban da yanmatan unguwar, duk unguwar babu Wanda ya ishesu kallo Balle su gaisa dashi, dukda gari yayi duhu suna kallon how beautifully dressed they're, they are beautiful and elegant,
"Yaran marowaci..." Usman ya fada yana kallon yaran dake tafiya duk cikin su babu wacce ta Kai 20,
"Ko Ina zasu?.." Habib ya fada yana kallon su ko kiftawa baiyi
"Oho masu...." Sufwan ya fada not paying attention to them, habib kura masu Ido to yayi without blinking yana cewa
"Yanzu irin wannan basu ganin mu matsayin mazaje kou?.." Dariya sufwan da usman sukayi Sannan usman yace
"Inda kasan yanda suke kallon mu da bazakayi wannan maganar ba...nasan kallon wasu banzaye suke mana,,," Bai karasa ba sufwan yace
"Ubansu né banza...Ni Wallahi basu burgeni...haushinsu ma nakeji...mutane sai shegen girman Kai da jiji da Kai...Wallahi tunda nake ban taba ganin sunyiwa kowa magana ba..." Yafada sounding angry, dariya habib yayi yace
"Ni Wallahi in da za'a bani dukkan su so nake...duk aikatasu zanyi cikin dare daya... " Yafada sounding naughty, dariya usman yayi har da buga kafa kasa while shi kuma sufwan ya sake sakin wani tsokin yana cewa
"Muji da yunwa dake damunmu..let's forget about them..." Yafada Sam face dinshi babu walwala dariya habib yayi yana cewa
"Ai dole Ai maganar mata...ai duk namiji yana bukatar su...nor matter how poor he is...Yanzu tsakanin ka da Allah Baka bukatar su?.." Habib ya tambayi sufwan, tsoki sufwan yaja ya Mike yana kakkaba bombom dinshi without saying a word, duk bin shi sukayi da kallo, habib dai kurawa yanmatan dake tafiya Ido yayi babu abinda yake tunani sai in da zai samu kudi Yanzu sai ya auri daya daga cikinsu ya moreta ya kuma ci ubanta saboda yanda ubansu yake wulakantasu cikin unguwar,
"Hmmm inama zan samu kudin balle hakan ya faru..." Yafada cikin ranshi yana mikewa.

YOU ARE READING
Sirrin wasu gayun
Misteri / ThrillerIt's story about greedy rich people, greedy ladies and guy with no jobs