😥😥 *BIYAYYA* 😥😥
~NA~
*MUNEEBA*
*Wattpad*👉🏻 @fatimamuneera001
*TRUE LIFE STORY*
*2💞3*
Tundaga ranar Ahlam Bata sake sa ganin yusif see Bayan sati daya se gashi lokacin Ahlam na tareda faruk gaba daya Basu Lura da Yusif ba se ganin shi sukai akansu faruk ya tsaya Yana kallon yusif Dan be taba ganin shi ba se yau Kallon rashin fahimta Duka suke binsa dashi yusif ya mikawa faruk hannu suka gaisa ya wuce cikin gidan ita dai Ahlam Bata kula Shiba seda ya wuce faruk yake tambayar Ahlam take fada Masa ai abokin Yaya Habib ne shidai faruk seyaji jikin sa Duka yayi sanyi Haka suna Gama Hira faruk ya tafi Ahlam zata shiga ciki kenan Sega yusif da murmushi ya kale ta kanwata ya fada Yana gyra tsayuwa shi Ina wuni shine abinda Ahlam ta fada amsawa yayi se kuma ya Fara magana Ahlam na yarda kinada Wanda kike so but mu cigaba da zuminci mu kawai, tohm Uncle yusif nagode ta wuce cikin gidan
Zaune take a part dinsu ta rafka uban tagumi tana tunanin rayuwa taji maman ta na Ahlam yau bazaki wurin ammin nakk bane tun daxu take yo aike gyrawa tayi ta kwnta jikin kujera tace eh anjima zank dake Ahlam yarinya ce bame son yawan magana ba Dan Koo Hira kake son yi karka yi da ita Dan daga uhmm se eh se Aa shikenan maganar ta ga zurfin ciki da take dashi Dan in Abu na damun ta ko zaka Burma Mata wula a ciki da kyar zata fada ma Haka halin ta yake tun tana yarinya sedai akwai yawan kuka Dan Abu karami seya sa ta kuka Haka rayuwa ta cigaba yusif duk ran Friday seya zo su gaisa da Yan gidan Kuma in ya tashi zuwa Haka ze tahowa da jikokin gidan tsaraba irin su chocolate, sweet,buscuit dadai sauran su Kuma Haka yake zuwa gaida mlm kabiru da hajiya Hauwa(Ammi) harda hajiya kareema (maman Ahlam) Duka Mata gidan ma Kuma indai ze tafi se ya Dan musu hasafi in ya tashi tafiya Kuma Ahlam ta rako shi har bakin motar shi.
Faruk ne tsaye da jaka rataye a wuyan shi Ahlam gefen shi se kuka take zeyi tafiya ne zuwa India daga wurin Aikin su aka turashi karo course shine yaxo Mata sallama kuka kawai takeyi yayi rarashi Amna Taki shiru seda taji yace ya fasa tafiyar sanan tayi shiru tana goge hawayen fuskar ta tace A'a yaje Allah ya kiyaye tana Nan tana jiran shi murmushi yayi me Kara Masa kyau yace toh mezan kawo Miki girgiza Kai tayi tace kai din kawai nake so ka ji kaki ji ka gani kaki gani Kar wata ta kwce min Kai Haka dai sukai sallama ya tafi Yana daga Mata hannu ita Kuma ta kasa hadiye kukan ta kawai ta shige gida da gudu Tai part din Ammi a Palo ta Sami ammin na Jan carbi ta fada jikin ta tana kuka, waya taba min Yar lelena Nan ta fada Mata faruk ya tafi India Nan fa Ammi ta shiga rarashi suna haka yayan ta Al_Amin ya shigo shima ya zauna suka dinga rarashin ta har tayi shiru
Yusif ne Bayan sun Gama gaisawa da Yan gidan Duka yasa aka Kira Masa ahlam suka gaisa bayan sun gaisa ne yaketa zolayar ta akan faruk ita Kam sedai tayi murmushi ta sunkuyar da Kai toh ni Zan tafi ya fada Yana wani killer smile tana shiga ciki aka Aiko baban ta na kiranta hijab ta zura ta nufi dakin baban nasu da sallama ta seta ga Yaya habib da Duka matan gidan nasu kowa ita yake kallo gefe ta samu ta zauna hade da dukar da kanta kasa baban ne ya Fara magana Ahlam Allah ya Miki albarka jiya iyayen yusif sunzo mum Gama magana akan auren ku keda shi dan har sun kawo goron gaisuwa munsa Rana Nan da wata biyu jin maganar tayi ta kasa daukar kwkwlwarta bibiyu ta Fara gani kafin tace ni Alhajin mu bani na Aiko shi ba fa ni ba son shi nake ba kauuu!!!!! Taji saukar Mari akan kumatunta Yaya habib ya sakar Mata shi, ke har mu Zaki maida Kanan mutane ki turo shi Kuma kice bake kika turo shi ba toh nufin ki Nina turo shi ya Kuma sakar Mata wani Marin a dayan kucin nata
Muneera
Don't forget to
#vote
#comment
#like
![](https://img.wattpad.com/cover/183113220-288-k189115.jpg)
YOU ARE READING
BIYAYYA
Short Storylabari ne kan wata yarinya data tashi cikin so da kwnar Yan uwa Wanda kaddara guda daya ta tarwatsa Mata farin cikin ta