*😥😥BIYAYYA😥😥*
~NA~
*muneera*
Wattpad👉🏻fatimamuneera001
*Allah ya jikan ki Aunty Allah yasa kin huta*
*33💞34*
Da sauri Ammi ta karasa dakin ganin yarda Ahlam take ba karamin firgitata yayiba da sauri tayo waje inda tai karo da yaya Abubakar ba shiri tace ya dauko mota sega hajiya babba temakawa mata sukai aka kai Ahlam motar suka nufi asibiti da sauri likitocin suka ciki da ita wanda ba abinda take se sallati da kiran sunan faruk din ta sun shafe kusan Awa uku a tsaye Amma Ahlam bata haihu ba waya Ammi ta dauka ta kira maman faruk ta sanar mata a firgice tace gata nan dan tunda Ahlam ta samu ciki ta ajiye komai da take ji dashi koda maman faruk tazo seda suka kara Awa 2 Ahlam bata haihu ba Wanda hakan yasa hankalin kowa ya tashi dr din yace suna son magana da mijin ta Amma tuni maman faruk tace likita baya garin Amma me kuke bukata sa hannu muke bukata dan se an mata CS nan Ammi tace abubakar yasa hannu yana sawa aka shiga da Ahlam wani dakin wanda duk suna tsaye akazo aka wuce da ita duka seda suka zubda mata kwla basu fi rabin Awa da shiga ba sega nurses sun fito da yara guda biyar😳 3 maza 2mata suka mikawa su Ammi suna fadin ta sauka dan murna maman faruk har kwla tayi abinda ze bawa me karatu mamaki shine gaba daya biyar (5) din lafiya su lau gasu kamar yan 1 hajiya babba ce tai kokarin tambayar Ahlam din nan sukace itama tana lafiya bacci takeyi An fadawa Faruk ba shiri ya dawo lokacin da yayi tozali yan 5 din seda yaji kwla lalai mahakurci mawadaci gaba daya yaran dashi suke kama, kamar su daya kafin lokaci kankani asibitin ya cika da jama'a ana kallon yaran yan 5 kowa mamaki yake *(kar ku manta labarin true life story kuma a gaske ma Ahlam yara biyar ta haifa a lokaci 1)* jama'a har wanda Ahlam bata sansu ba tun a asibiti aketa musu gift ga yan jarida se tururuwar zuwa suke daukar rahoto lokacin sallama beba Aka sallami Ahlam ta dawo gida kwna 4 da haihuwar sega governor da tawagar sa sunzo ganin Ahlam din da yan 5 dinta ga gift daga governor din na kula da yaran kyautar 10million ya musu kan su kula da yaran godiya sukai sosai sanan ya tafi gift kuwa su Ahlam har rasa inda zasu saka kaya sukai ga yaran suna samun kulawa a wurin Ammi da mama da sauran matan gidan jarida kuwa ba jarida da baa buga hoton yaran ba haka ma gidajen radio da TV. wanan kenan
Shekara shida ba haihuwa yusuf ya kamata kuje asibiti a duba waye me matsala a cikin ku kai ko ita yarda za'a samu masalaha abin maman yusuf ce zaune takewa yusuf maganar nan Amsa mata yayi washe gari suka shirya shida matar shi sukaje Asibiti gaba daya akace musu basa haihuwa daga ita harshi bawanda ze haihu basu da kwan haihuwa innalillahi wa'ina illahi raji'un shune abinda yusuf ya fada tabbas Alhakin Ahlam ne ke bibiyar sa haka suka tashi suka taho a hanya ya siya jarida yana komawa gida yaja jarida a page din farko yaga ansa *wata mata ta haifi yan biyar*Budewa yayi ya fara karantawa inda yaga Ahlam rike da yaran kafin ya gama karantawa yaji mamanshi na kwla masa kira ajiyewa yayi ya shiga nuna masa TV take tana kwla girgida kai yayi yace eh mama nima yanzu nagani Ahlam ta haifi yan ...Se kuma yayi shiru kwla na fitowa daga idonsa
Yau ta kama suna gidan Malam Kabiru ya cika makin da jama'a anzo dan taya Ahlam murna anyi taro lafiya an tashi lafiya Ahlam da faruk sun koma gidan su da faruk ya gina musu a nan kano mahaifiyar faruk bata gajiya da neman yafiyar Ahlam wanda Ahlam din har kunya takeji
5years later
Yara ne maza uku kabir wanda suke kiransa da Ameer se sadik wanda suke kiransa mu'alim se hafiz se mata biyu hauwa wace suke kiranta da mama se khadija wace suke kiranta Baby zaune suke suna karatu Wanda Ameer shike koya musu assignments suka ji sallama daga kai sukai suka kalli wanda yake shigowa dan basu san shiba shida wata tsohuwa a gefensa Ameer ne ya fara gaida su sanan sauran suka gaida su, suka basu wuri a palon nasu suka zauna baby da take sarkin karambani ce taje ta kawo musu ruwa mama kuwa da take miskila bata fiye son magana ba tace musu momyn tana zuwa suka Amsa da toh wata babbar mace naga ta fito itada wani matashi daka gansu kasan cikin kwnciyar hankaki suke ga katon ciki dake jikin matar wace ba kowa bace se hajiya Ahlam da masoyin ta faruk a gefe wanda suka rike da ita tana tafiya da kyar suka zauna se lokacin ta kalesu bakowa bane illa yusuf da mamanshi zubewa sukai suna neman yafiyar Ahlam wanda Ahlam din ta mike da kanta ta je ta tayar da maman yusuf ta zaunar da ita tana fadin mama ni nariga da na dade da yafe muku Allab ya yafe mana baki daya suka Amsa da Ameen su yusuf suka tashi suka fice cike da kwdayin irin rayuwar da Ahlam suje da iyalanta suna fita Ahlam ta fara nakuda nan sukai hspl da ita ba jimawa aka fito da yara guda 2 da Ahlam ta haifa wanda faruk ana fada masa yai sujada yana godiya ga Allah💃🏾
Iyalan sun kasance cikin so da kaunar junansu duk abinka baka isa kace basa burgeka ba kullum cikin godiya ga Allah suke
Kassssshhhhhhh Anan biro na ya tsaya cak na juya zan tafi Ahlam ta kirani tace muneera najiya tace kicewa masu karanta labarin nan namu mun gode 😍Allah saka munga sharhin su nace inshaa Allah na juya na fice daga gidan ina wagen su
*ALHAMDULLILAH ANAN NA KAWO KARSHEN LITTAFIN BIYAYYA WANDA NAYIWA BA DAI DAI BA YA YAFE MIN ABINDA NAYI DAI DAI ALLAH YA BIYANI ABINDA NAYI KUSKURE ALLAH YA YAFE MIN 🙏🏻*
*muneera
YOU ARE READING
BIYAYYA
Cerita Pendeklabari ne kan wata yarinya data tashi cikin so da kwnar Yan uwa Wanda kaddara guda daya ta tarwatsa Mata farin cikin ta