*😥😥BIYAYYA😥😥*
~NA~
*MUNEERA*
*True life story*
Wattpad 👉 fatimamuneera001
*INA TAYAKI MURNA KAMALA LITTATIN KI SAHIBA🥳🥳(UMMU NABIL) GA IRIN TA NAN ALLAH YA KARA BASIRA, KAZAKA DA KWRIN IDO ALLAH YASA MU AMFANA DA ABINDA KIKA RUBUTA*
*6💞7*
Rike kuncinta tayi tana kallon yusuf hade da kwla me Kuna data fito daga idonta kallon tsana ya bita dashi Yana fadin Ranar Dana Fara ganin ki Ahlam ranar naji na Fara sonki Sedai Kash da na tareki da maganar Kika watsa min 'kasa a Ido kikace Baki sona Kika nuna min 'kiyaya karara Ranar banyi bacci ba saboda abinda kikayi min Ahlam a ranar naji cewa kamar na mutu Rana ta biyu da muka hadu se naganki da wani wanda ko ba'a Fada ba soyaya ce a tsakanin ku lokacin Dana ganku Kika nuna halin ko in kula agareni Bayan na fada Miki inason ki Ranar na dawo gida a hargitse sakamakon kishin ki da nake na sanar da mahaifiya ta, ta karfafa min gwaiwa kan na hukunta ki saboda ban taba neman Abu narasa ba Ahlam!!!! Ya fada tsawace kinyi kuskure Kuma yanzu Zaki girbi kuskuren ki Kuma yanzu karki tsamanin inason ki ko daya *NA TSANE KI* Ahlam Aida na dauka da nakai kudin auren ki Zaki 'ki yarda da maganar iyayen ki sedai se Naga ashe KE yarinya ce me *BIYAYYA* seki ka yarda Wanda shine kuskuren da Kika taba tafkawa babba a rayuwar ki Ahlam Kuma karki tsamanin sasauci a taredani da mahaifiya ta ki shirya yin bauta. Tunda ya Fara magana Ahlam take kuka Tama girgida kaikai
Innalihahi wa'ina illahi raji'un shine abinda ta iya rafkawa ta Kali Yusuf tace a Koda yaushe koma me zaka min Zan maka *BIYAYYA* kamar yarda nayiwa iyayena Kuma kome zaka min Kar ka manta da Allah na ganin mu Kuma yanajin mu Zan dauki auren ka A matsayin kaddara ta Kuma jarabawa daga mahalici na uncle Yusuf......... Shiru tayi saboda wani Marin daya Kara Mata shi har guda biyu a fuska Wanda seda numfashi ta ya dauke na seconds sanan yace bakida damar magana banza wawiya kawai Yana Gama fadar haka ya fice daga dakin hade da banko kofar zubewa tayi a wurin tana fadin Nashiga uku ni Ahlam Allah nagode maka daka jarabe NI da wanan jarabawa ya rabbi ka bank juriyar cin wanan jarabawa taka kuka take kamar ranta zai fita Idon ta yayi bulu bulu ya kumbura saboda tsabar kuka ta Mike tsaye jiki ba kwri tayi toilet din cikin dakin ta tsaya ta wanke fuskar ta sanan ta Dora alwala, sallah tayi ta Dade Akan daduma kafin ta tashi ta hau kan gadon tana tunanin faruk din ta yanzu dashi ta aura da ba abinda zesa....shiru tayi data tuna ita matar Aure ce be kamata tayi tunanin wani ba gyra kwnciya tayi tana tunani har bacci yai awan gaba da ita Kiran sallah Asuba ne ya tashe ta inda cikin ta taji kamar an Mata sata cikin sa saboda tsabar yunwar da takeji da kyar take tafiya ta fito tangamemen katon palon Wanda ta bishi da kallo tana tunanin Ina ne kichen kallon steps din tayi ita kadai tace may be a Nan ya kwna Allah ka Kare ni daga sharin sa Dana mahaifiyar shi Nan ta shiga laluben kichen din har ta karasa ciki fridge ta bude Nan ta hango fresh milk a ciki da sauri ta dauka saboda jikin ta har karkawa yake saboda yunwa kafa Kai tayi ta Fara Sha seda ta Sha kusan rabi sanan ta sauke Se lokacin ta dawo hayyacin ta store din kichen ta bude shinkafa Yar hausa ce buhu daya se wake se galan din Mai se Kuma borkono a gefe hade da kayan Magi tsayawa tayi tana kallon su Ashe duk abinda take Yusuf nakallon ta se ji tayi yace yess wanan sune abincin ki su Zaki dinga ci banza kawai Zan temaka garin masara ya biyo baya sanan gaba daya Yan Aikin gidan Nan na sallame su KE Zaki dinga yin komi kina jina shiru tayi Bata bashi amsa ba ya kuma maimaitawa itadai kanta a 'kasa batace komi wani mugun naushi ya Bata a kumatu Wanda Bata San lokacin da ta saki ihuu ba sanan ya jawo gashin kanta ya daga kanta sama Yana fadin kinji ko Baki ki saboda tsabar azaba kasa magana tayi ya Kuma maimaitawa kinji ko Baki jiba ya fada Yana Kuma Jan gashin nata, da kyar ta it's cewa naji uncle Yusuf sanan ya saki Mata kanta Yana wata irin shu'uma dariya,a wahalce ta fito daga kichen din tana tafiya da kyar ta shige toilet ta Fara wanka seda ta gagasa jikin ta sanan ta fito ta dauko wata white din atampa ta me ratsin blue ta saka ta daura dankwali duk da ba abinda tasa a fuskar tata hakan be Hana fito da ainahin Kyaunta ba fitowa ta Palo keda wuya taji Sallama maman uncle Yusuf har kasa ta tsuguna ta gaida ta wani dogon tsaki taja tana yatsine fuska tace tunda Baki zo ba Nina zo itadai Ahlam kanta a 'kasa batace komi ba tace mama ki zauna wani mugun kallo ta watsa Mata tace KE har kin Isa kice na zauna tou baxama nazoyi ba dama so nake kizo ki gyra min part dina yanzu toh mama ganinan ta fada still kanta na kasa maman nashi ta Kuma kallon ta tace Simi Simi dake munafuka kawai
Muneera
Don't forget to
#Vote
#comment
#share
YOU ARE READING
BIYAYYA
Short Storylabari ne kan wata yarinya data tashi cikin so da kwnar Yan uwa Wanda kaddara guda daya ta tarwatsa Mata farin cikin ta