BIYAYYA

1.3K 92 4
                                    

*😥😥BIYAYYA😥😥*


~NA~

*muneera*

NOTE; *GASKIYA INAJIN DADIN COMMENT DIN KU, KUMA YANA SANI NISHADI SEDAI MATSALA 1 DA KUKE MAGANA KAN AZABTAR DA YUSUF YAKEMA AHLAM KARKU MANTA LABARIN TRUE LIFE STORY NE 😭NI KAINA DA NAJI LABARIN SEDA NAYI KUKA😭 SOSAI SABODA ABINDA YUSUF YAYIMA AHLAM KUMA WANAN YA KAMATA YA ZAMA GARGADI GA 'YAN MATA WA'ANDA IN ANCE ANA SON SU, SUKE FITOWA DIRECT SUNUNAWA MUTUM BASA SON SHI WANI MA BA MUTUM BANE WANI KUMA MUGU NE ZE MAKA ABIN A KIYAYE TOH KU CIGABA DA BIN MUNEERA DAN KUNJI KULLIN DAKE CIKIN LITTAFIN NAN*

*12💞13*

Jin maganganun Ahlam kamar zasu fasa masa kai ita kuwa cigaba tayi da fadin yarda ka tsane ni wallahi nima haka na tsane ka bana sonka duk abinda kake min ina jurewa ne saboda *BIYAYYA* da nakema iyayena kaima kuma zan maka saboda ka girme ni kuma kai mijina ne tana gama fadin hakan   shige dakin ta a gije kuka tayi me isarta sanan ta rarashi kanta toh kodai ta gudu ta huta toh inta gudu ina zata? ita da bata taba barin garin kano ba? inta gudu ya mahaifiya ta zata ji inta samu labarin ta gudu? can dai ta kawar da tunanin saboda wani kugi da cikinta yayi saboda tsabar yunwar da takeji amai taji ya taso mata ta shige toilet da gudu ta fara kwra amai kuma aman Na komi bane se ruwan da tasha ta jigata sosai ji tayi tama hakki sama sama ta jawo kafar ta da kyar ta fito palon har lokacin Yusuf yana zaune yana dane dane a laptop din shi ace mutum kwna 2 ba abinci ai dole ta fada wani hali karasowa tayi tana zuwa tsakiyar palon ta fadi timm kamar mataciyya da gudu yusuf yayi kanta yana jijiga ta amma bata motsi dora hannu yayi aka yana fadin na shiga uku kardai na kashe musu yarinya😳 ruwa ya yayafa mata amma ina ahlam ko motsi bata yi jijigata yake yana ihu amma taki motsi da sauri ya sureta dama yanzu ta zama yar shafal ba nauyi se kasusuwa da hakoran da sukayo waje idonta kuwa duk sun zurma se wani haske da tayi sosai. Mota ya shiga da ita yanata zufa gaba daya ya fita hayyacin shi a tunanin shi Ahlam din ta mutu Asibiti kusa dasu wani private yakaita da sauri aka anshe ta aka fara bata temakon gagawa seda aka kusa minti 10 sanan dr din ya fito yace ya biyoshi office jiki na bari yusuf yabi bayan sa seda suka zauna sanan yace kayi hakuri..Sir amma.....Da sauri yusuf fara zare idoo yana fadin amma me  doctor mene ya fada a razane doctor kuwa cewa yayi haba mana cool down ta samu hawan jini ne kuma ga ulcer Ta suma ne Amma yanzu zata farfado se lokacin hankalin yusuf ya saisaita ya zauna yana maida numfashi a zuciyar shi yace lalai lokaci yayi tun kafin ta mutu a gidanaBema karasa jin maganar dr ba ya tashi ya tafi gida ya nufa ya shige bangaren maihaifiyar sa ya fada mata tace A lalai lokaci yayi yanzu dai kanemi sallama a sallamo ta se mu aiwatar da abinda muka shirya murmushi yusuf yayi ya fice ya shirya ya koma asibitin aka sallame su, suka dawo gida farfesu ta gani da kayan abinci yusuf ya jera mata sanan ya zaunar da ita ya zuba mata abincin ta karba ta faraci tana tunanin yaushe ya canza haka.

Wai ina labarin *faruk* ne🤔

Lokacin da faruk ya dawo daga tafiya be sauka ko a gida ba se gidan su ahlam tun a bakin gate me gadi ya sanar dashi ai ahlam tayi aure tashin hankali da ba'a sa masa rana faruk yana juyawa ya tafi harya hau titi be sani ba mota ta buge shi akai asibiti dashi ya samu karaya a kafa da ya warke faruk ya zama abin tausayi saboda faruk mutum ne me wasa da dariya ga barkwnci saboda rashin Ahlam se ya koma in ana magana eh da A'a ko kuma hmm anyi nasiha anyi rarashi anyi fada amma faruk be dawo normal iyaka ma in aka dame shi ya bar auri har wurin aikin su seda suka gane ga companies din mahaifinshi dayake kula dasu duk sunyi sanyi faruk baya bada wata ishashiya kulawa.

Koda Ahlam ta gama cin abinci yusuf ya tashi ya fice ya dauki mahaifiyarsa suka bar gidan ni kuwa nace ko ina zasu Ahlam kuwa shiryawa tayi tasha magunguna ta ta kwnta tuni bacci yayi awon gaba da ita Jin ana bubuga part dinsu yasata zuwa ta bude me gadi ne ya mika mata wayarshi uncle yusuf yace tai maza maza tazo gidan su babanta yana nemanta ji tayi gabanta ya fadi ta dauki hijab kawai ta fita befi 10mnt ba ta karasa gida   tundaga kofar gida taga yayanta maza na wula mata harara da mugun kallo

Dont forget to
#Vote
#comment
#share

*Muneera*

BIYAYYAWhere stories live. Discover now