*😥😥BIYAYYA😥😥*
~NA~
*MUNEERA*
*wattpad* @fatimamuneera001
*Dedicated to my lovely husband💞💞my yaya i luv u🙈Allah ya raya mana mukhlisa*
*10💞11*
Tsale yaya habib yayi ya fincike Ahlam daga hanun maman Yusuf yana fadin haba mana wallahi baze yuyu ki kulawa kanwata sharin sata ba na rantse me zatayi da wani gold din ki bayan tafi karfin shi wallahi duk cikin gidan mu babu barawo wallahi bata sata kuma bata gaje ta ba kai kuma yusuf nagode sosai da abinda ka nuna min kanwar tawa kaiwa haka kalli fuskar ta daga gani dukanta kayi da sauri ahlam ta rike yaya habib tana kuka take fadin A'a yaya baya dukana baya min komi faduwa nayi ne na buge numfarfashi yake yi yana kallon Yusufji yake kamar ya zane shi amma kuma Ahlam ta hana shi Kallon maman yusuf yayi wacce tayi tsuru- tsuru yace nawane gold din naki kame-kame uhmm 100k ne wani uban tsaki yaja yace Allah wadaran Yusuf ne yace habib ya isheka fa mahaifi......Kasa karasawa yayi saboda wani mugun kallo da Habib ya watsa masa shiyasa shi saurin tsuke bakin sa 🙊 zaro 100k din yayi rafar yan 1k ya mika mata yace gashi dukda nasan karya kikayiwa kanwata dan munsan irin tarbiya da muka bata tai saurin karba shi kuma habib ya wuce yaja motar shi ya fice Ahlam na ganin haka tayi saurin yin cikin gidan da gudu ai kuwa Yusuf yabi bayan ta da gudu shima seda ya lakada mata dukan da ko motsi ta kasayi sanan ya barta acewar shi dan uwan ta ne ya jawo mata tayi kuka ta rarashi kanta
Haka rayuwa ta cigaba Ahlam itace ke aikin duka gidan kama daga part din su harna Maman Yusuf gashi komi tayi bata tsiraba saboda kullum Yusuf da kallar muguntar da yake mata yan aikin gidan ma tausayin ta suke saboda yanzu basa aikin komi ita keyi me gadi ma wata rana har kuka yake mata yana addu'ar allah ya fitar da ita daga wanan kuncin rayuwa karshe ma Yusuf daya ga yan gidan su ahlam na zuwa se yaje yace musu ai tafiya zasuyi tundaga ranar bawanda ya kara zuwa saboda su a tunanin su sunyi tafiya wayarta kuwa ya karbe
Yauma kamar kullum ta gama duka aikin gidan ta duba store taga abincin ya kare wani mumunar faduwar gaba taji Batasan da wani ido zata kali Uncle yusuf tace ba abinci ba tasan halin shi ze iya mata illa dan haka taja bakin ta, tai shiru intaji yunwa ta ishe ta tasha ruwa har gari ya waye tana gama shiryawa ta fito yana zaune kan daya daga cikin kujerun palon tsugunawa tayi tace uncle yusuf pls ka temaka min abincin mu ya kare dan Allah mikewa yayi yaja tsaki ze bar wurin tayi saurin rike kafar shi tana fadin ka temaka uncle yusuf wallahi yunwa nake ji zan iya mutuwa dan allah karka hukunta ni da rashin Abinci dan bazan iya jurewa ba ka temake ni naushi yakaimata da kafar take bakinta ya fara jini yana kokarin barin wurin ta kuma rike shi Uncle Yusuf kar.......Tasss!!! ya bata mari tohm mayya wace ta gaji maita In banda ke mayya ce ai naji koo amma sekin nuna min halin ku irin na mayu wawiya jaka jahilla wallahi bakida amfani amma ki cigaba lokaci nake jira da lokaci yayi zaki ga abinda zan miki sena tarwatsa miki rayuwa sena tarwatsa miki farin cikin ki a zuciyar ta tace yanzu ma aika tarwatsa min shi cigaba yayi da magana dama habib ma seya gane kuskuren shi ke bari kiji duk wani familyn ki se yayi Allah wadarai dake saboda sena saki kinji dama mutuwa kikayi kika huta da irin *RUYUWAR KUNCIN* da zan jefa ki wanda karema baze kala ba Natsane ki ahlam na tsani me sonki ma wallahi bakida mahimmaci a rayuwata karki taba tsamanin wata rana zan soki ko zanyi dana sanin abinda na aikata miki bazanba me bakin hali Mahaifinki da yake babba malami a garin nan se yaji dama be haifeki ba ki jira lokaci ki gani wasu zafafan hawaye ahlam take tana Allah ya fika yafi wanin ka uncle Yusuf kayi min fin haka ma zan jure kuma duk abinda zaka min ai Allah daya hallice ka yana gani yana kuma ji 😭wallahi tunda kamin kaima se an maka ka jira lokaci kaimaMuneera
Dont forget to
#vote
#comment
#share
YOU ARE READING
BIYAYYA
Короткий рассказlabari ne kan wata yarinya data tashi cikin so da kwnar Yan uwa Wanda kaddara guda daya ta tarwatsa Mata farin cikin ta