🌸Na Anty pink🌸
"Wai mey mutuminnan yake nufi ne? Har ni yake ce wa fitsararriya ni wlhy bxn aureshi ba" tana gama fadin haka ta kara fashewa da kuka yayinda ta cigaba da fadin "ni wlhy Allah bana sonshi". "Ai kuwa gwara ki soshi" ta jiyo muryar Anty daga bakin kofa. Ta karasa shigowa dakin ta tsaya a gaban ta tace "wlhy bari kiji in gaya miki idan zaki soshi ki soshi dan aure kam sai anyishi" tana gama fadin haka ta wulla hoto ajikinta tace "gashi nan ki duba ki gani hoton Aliyu haidar ne Wanda xai aureki kuma bari kiji in gayamiki idan ya kiraki kada kisake ki masa rashin kunya da fitsara in bahaka ba abbanku zan gayama kuma kinsan ba karamin rashin jin dadin hakan zaiyi ba snn ki shirya gone za'a zo kawo goron aurenki".
" goro kuma"? "Eh goro kuwa nidai na fada miki saura kuma ya rage naki" tana gama fadin haka ta fice daga dakin.
YOU ARE READING
💞komai daren dadewa💞
Ficção Gerallabarine daya kunshi darusa masu yawa akan zamantakewar rayuwa. Banyi wannan littafin Dan cin zarafin wani ko wataba idan kaga yayi daidai da labarinka toh akasi aka samu