PART 1/5

792 31 3
                                    

*_TSANTSAR WAUTA_*

💖💖💖

*_WRITTEN-BY:_*

*_ANTY MAIMOUNATH O.G (Mahnoor)_*

_Wattpad@maimounathog_

*SADAUKARWA GA:*

*MASARAUTAR MOA👑-ZINDER👑-MACHINA👑 & DOLEN MACHINA👑.*

*💫DA BAZAR-MU WRITER'S ASS💫*

*_~We are here to make you happy, smile, educate and to realized that we are d best among all...DA BAZAR-MU MUKE TUN'KAHO.~_*

*_GODIYA_*
_Dukkan godiya ta tabbata ga Allah mad'aukakin sarki, mai girma da d'aukaka, mai iko akan komai._

_Tsira da amincin Allah su k'ara tabbata ga shugaban mu Annabi Muhammad(S.A.W). Allah ya k'ara aminci da karamci a bisa ga dukkanin sahabban Manson Allah (S.A.W), da kuma iyalansa baki d'aya._

_Bayan godiya ga Allah mad'aukakin sarki, ina rok'on Allah ya dafa min kan rubutu na, ya Allah karka bani damar rubuta abinda yake sab'o a gareka, ya Allah yanda na fara lafiya kasa in gama lafiya._

*Sak'on gaisuwa ta a gareku kakannina 'yan na gada, Allah ya tayaku ruk'o, Allah ya k'ara lafiya da nisan kwana( Allah kawun'jo).*

*_GARGA'DI:_*
*_Wannan labari k'irk'irarre ne banyi shi dan wani ko wata ba, idan yayi dai-dai da rayuwar ka/ki akasi ne, kuma ban yadda a copy min rubutu ba ko a juya min labari...._*

*_LITTATTAFAI NA MASU FITOWA:_*

*_'YAR GADARA_*
*_ZAMBA CIKIN AMINCI_*
*_RAYUWAR SABREEN_*
*_MAZNEEN_*
*_SARK'AK'IYA_*
*_SA'IN SA_*

*_PAGE 1/5_*

*_BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHIM_*

Da gudu wata yarinya ta shigo tana fad'in cewa'' wallahi ba'a isa ba sai na rama, yo ni kin isa ma in k'yale ki tabd'ijam''. Tana cikin fad'an ta ne wata mata wacce zata kai k'imanin shekaru sittin(60 Years) ta fito daga d'aki tana cewa'' to 'yar masifa yau kuma ke da wa?"

Yarinyar ta k'araso inda matar take tace'' Inna wallahi bazan yadda ba sai na rama ji fa ki gani yanda Huwaila ta yaga min riga ai bata isa ba''.

Inna tayi dariya tace'' kai jama'a, to me ya hanaki ramawa tun a can sai kizo kina min surutu a gida ko sallama baki iya yi ba''. Baki ta turo tace'' ai wallahi sai na rama bari a jima idan na had'u da ita a bakin rafi''.

Inna ta rik'e baki tace'' ke Rahane ki kiyaye ni kinji ko? Wai ke kam yaushe zaki daina masifar nan? Baki san yanzu kin fara zama 'yan mata ba?"

Hararen Inna tayi tace'' kinga Inna ki daina ce min wata Rahane ni Rayhana sunana haba haka kawai kina b'ata min suna''. Ta k'arashe maganar tana mai murgud'a baki. Inna ikon Allah kawai take kallo dan abin yafi k'arfin ta, wannan yarinyar ta rasa wa ta biyo masifar nan ta ta.

Kamar yanda Rayhana ta fad'a hakan kuwa akayi dan da yamma suka had'u a rafi sukayi fad'a kaca-kaca ita da Huwaila saboda Rayhana bata barin ta kwana idan akayi mata sai ta rama.

'Kawayen su ne suka raba su da k'yar aka kai Rayhana gida ga k'ugun ta d'aure da gammon da zata d'auko ruwa. Ruwan da bata d'auke shi bâ kenan.

Da daddare suna cin abinci Inna ta kalleta tace'' Rahane wallahi halin ki ya ishe ni birni zan kaiki wajen baban ki na birni dan bazan iya ba masifar ki ta isheni''.

Haba wa ai Rayhana tana jin haka ta fara birgima a k'asa daman bisa tabarma suke shine take ta juyi a k'asa tana cewa'' wayyooo Allah na jama'a Inna zata kaini birni dan a yanke min kai, kuzo ku ceceni''. Haka tayi ta kururuwa Inna tayi banza da ita haka mak'otan su ma suna jinta amma da yake sun san halin ta kowa bai zo ba.

TSANTSAR WAUTAOù les histoires vivent. Découvrez maintenant