*_TSANTSAR WAUTA_*
💖💖💖
*_WRITTEN-BY:✍🏻_*
*_ANTY MAIMOUNATH O.G_*
*_(Mahnoor)_*_Wattpad@maimounathog_
*_SADAUKARWA GA: MASARAUTAR_*
*_MOA👑~ZINDER👑-MACHINA👑& DOLEN MACHINA👑_*
*💫DA BAZAR-MU WRITER'S ASS💫*
*_~We are here to make you happy, smile, educate and to realized that we are d best among all.... DA BAZAR-MU MUKE TUN'KAHO.~_*
*Sak'on gaisuwa ta a gareku sarakunan mu kakannina 'yan na gada, Allah ya tayaka rik'o, Allah ya kara lafiya da nisan kwana(Allah kawun'jo)*
*_LITTATTAFAI NA MASU FITOWA:_*
*_ZAMBA CIKIN AMINCI_*
*_RAYUWAR SABREEN_*
*_ALA'KAR MU DASHI_*
*_MAHVEEN_*
*_SARK'AK'IYA_*
*_SA'IN SA_**_Mai hankali shi yake gane d'ingishin kwad'o._*
*_Masoya me zan ce daku banda godiya👏🏻ashe haka YAYANA HASSAN yake da farin jini? Masu son in cigaba da rubutu afwan gaskiya ba yanzu ba sai na gama novels d'in nan biyu idan ma zan iya kenan. Nagode, nagode sosai Allah ya bar k'auna.💞_*
*_PAGE 96/100_*
*_BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHIM_*
°°°°°Inna ta kalli MUBARAK tace'' jeka abin ka ai ta hak'ura ma sai dai karka sake irin wannan maganar kaji ko?"
'' Insha Allah Inna bazan sake ba kuskure nayi ku gafarce ni''. MUBARAK ne ke fad'in haka. Mama dai cewa tayi'' humm''. Kawai dan akwai abinda take ayyanawa a ranta.
An sallame su daga asibiti MUBARAK ne ke jan motar ya doshi hanyar gidan shi mama tace'' ya naga ka biyo ta nan?''.
Cikin ladabi MUBARAK yace'' eh mama inaso in ajiye ta a gida sai in wuce daku''.
'' A,a juya ka kai mu gida har HANAH d'in can zamu je''. Gaban shi ne ya bada wani dumm me mama take nufi kenan? Oho maka.
Suna zuwa mai gadi ya bud'e musu gate suka shiga, bayan yayi parking ne driver'n gidan yazo da d'an saurin shi ya bud'e musu k'ofa suka fito.
Mama da kanta ta kama HANAH suka nufi hanyar part d'in ta tace da driver'' ka kwaso kayan cikin motar''. Sannan suka wuce MUBARAK dai kallon ikon Allah yake.
Bayan sun shige ya kalli Inna yace'' wai Inna me hakan yake nufi ne? Ban gane komai ba''. Inna tace'' muje ciki dai inji ya abin yake dan nima ban gane ba''.
A tare suka shiga falon a lokacin ne mama take cewa'' 'yata tashi kije ciki kiyi wanka ki huta zan sa a dafa miki wani abin''.
Tashi tsaye tayi sai da suka had'a idanu da MUBARAK ta kauda kanta duk ya zama kalar tausayi haka ta shige bata k'ara waigowa ba.
Bayan sun zauna ne mama ta kalli MUBARAK tace'' kai kuma lafiya ka shigo? Ka tafi harkokin gaban ka nawa''.
Bai yi magana ba kanshi a k'asa sai Inna ce tace'' hajiya nifa ban gane ba, to ba dole ya shigo ba tunda matar shi ta shigo ki bashi matar shi su tafi gida''.
Cikin ladabi mama tace'' Inna ki gafarce ni amma HANAH ba zata bishi ba haka kawai yaje ya zubar mata da ciki''.
Hak'uri dai zakiyi ai ya gane kuskuren shi''. Cewar Inna. Mama fa ta gama kai da k'afa tace sam bata san zancen ba. Inna ta rok'e ta har ta gaji amma sai hak'uri ta ba Inna.