PART 101/102

337 13 4
                                    

*_TSANTSAR WAUTA_*

            💖💖💖

*_WRITTEN-BY:✍🏻_*
*_ANTY MAIMOUNATH O.G_*
          *_(Mahnoor)_*

_Wattpad@maimounathog_

*_SADAUKARWA GA: MASARAUTAR_*

*_MOA👑~ZINDER👑-MACHINA👑& DOLEN MACHINA👑_*

*💫DA BAZAR-MU WRITER'S ASS💫*

*_~We are here to make you happy, smile, educate and to realized that we are d best among all.... DA BAZAR-MU MUKE TUN'KAHO.~_*

*Sak'on gaisuwa ta a gareku sarakunan mu kakannina 'yan na gada, Allah ya tayaka rik'o, Allah ya kara lafiya da nisan kwana(Allah kawun'jo)*

*_LITTATTAFAI NA MASU FITOWA:_*

*_ZAMBA CIKIN AMINCI_*
*_RAYUWAR SABREEN_*
*_ALA'KAR MU DASHI_*
*_MAHVEEN_*
*_SARK'AK'IYA_*
*_SA'IN SA_*

*_Assalamu alaikum sister's please mai rauni kar ta karanta wannan shafin fatan kun gane😉_*

*_PAGE 101/102_*

*_BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHIM_*


*^^^^^^^* Yana bud'ewa sukayi ido hud'u da Zainab sai ya k'ara d'aure fuska ya fice ba tare da ya kulata ba.

Bin shi tayi da kallo kafin daga bisani kuma ta shige d'akin inda ta iske HANAH tana sharar k'wallah.

Cikin sauri ta k'arasa bakin gadon tana tambayar HANAH me ya faru, da farko batayi magana ba sai da Zainab ta sake cewa'' ko dai yaya ne yayi miki wani abin?"

HANAH tana sharar k'wallah tace'' ba shi bane yace zai k'ara aure". Ta k'arashe maganar tare da fashewa da kuka. Zainab tace'' to ai ni banga laifin yaya ba ko da auren zaiyi''.

Jin hakan da HANAH tayi yasa ta tsagaita kukan tace'' au haka ma zaki ce kenan?"

'' To me kikeso in ce miki? Duba kiga yaya yanda ya koma ya zama abin tausayi sai ja masa rai kukeyi ai wallahi ina bayan shi yayi auren shi kawai tunda ba son sa kikeyi ba''.

Baki ta turo tace'' to wai ni ya kikeso inyi ne? Mama ce ai tace inyi zama na dan kar yaje ya bani wani abu in sha cikin ya zube''.

'' To ai shikenan gashi kin ja ma kanki zama da kishiya kina 'yar k'ank'anuwar ki''. Duka ta kai ma Zainab tace'' kuji muguwa nidai wallahi banson kishiya dan Allah meye mafita?"

Dariya Zainab tayi tace'' iyyyeee kice daman kina son shi kike masa jan aji ko?"

Rufe fuska HANAH tayi tana murmushi tace'' nifa tausayi ne yake bani shiyasa ma nake son komawa''.

'' Uhm fad'i gaskiya dai mutuniya ta''. Cewar Zainab cikin tsokana. HANAH tace'' please meye abin yi yanzu?"

Zainab tace'' kawai kije kice ma mama kina son komawa gidan mijinki''. Idanu HANAH ta zaro tace'' ke Zainab saboda bani da kunya ko?"

'' To nidai ba ruwana idan yaje ya kawo miki wata wayayya, oh ni ashe yaya har hira yake zuwa wurin budurwa bamu sani ba lallai''.

Abinda Zainab ta fad'a ya kular da HANAH sai ta tashi ta shige toilet dan tsaftace jikinta duk ta manta ma da taji maganar kishiya.

Cikin kwanaki biyu HANAH ta daina walwala gashi tun ranar da MUBARAK ya bar gidan bata sake ganin sa ba yana zuwa da ya gaishe da mama yake ficewar sa.

Mama tayi-tayi HANAH ta fad'a mata abinda ke damun ta amma tace ba komai, haka Inna ma ta tambaye ta har ta gashi duk dai amsar d'aya ce babu komai.

TSANTSAR WAUTAOù les histoires vivent. Découvrez maintenant