PART 11/15

322 10 0
                                    

*_TSANTSAR WAUTA_*

          💖💖💖

*_WRITTEN-BY:_*

*_ANTY MAIMOUNATH O.G_*
          *_(Mahnoor)_*

     _Wattpad@maimounathog_

*SADAUKARWA GA:*

*MASARAUTAR MOA👑-ZINDER👑-MACHINA👑 & DOLEN MACHINA👑.*

*💫DA BAZAR-MU WRITER'S ASS💫*

*_~We are here to make you happy, smile, educate and to realized that we are d best among all...DA BAZAR-MU MUKE TUN'KAHO.~_*

*Sak'on gaisuwa ta a gareku sarakunan mu kakannina 'yan na gada, Allah ya tayaku ruk'o, Allah ya k'ara lafiya da nisan kwana( Allah kawun'jo).*

*_LITTATTAFAI NA MASU FITOWA:_*

*_'YAR GADARA_*
*_ZAMBA CIKIN AMINCI_*
*_RAYUWAR SABREEN_*
*_MAHVEEN_*
*_SARK'AK'IYA_*
*_SA'IN SA_*

*_Akwai wasu groups da zan daina tura novel, domin samun cigaban labarin mai so tayi min magana prvt amma idan kinsan ba zakiyi comments ba karki b'ata min lokaci, nagode..._*

*_PAGE 11/15_*

*_BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHIM_*

Bin bayanta yayi inda ta gudu wajen Inna a part d'in ta, daman tanada nata b'angaren idan tazo tun da jimawa.

Cikin takunsa na isa ya shiga falon tare da yin sallama, ai kuwa RAYHANA ta shige k'uryar d'aki tana ihun kiran Inna amma cikin rashin sa'a Inna tana bayi.

Ciki ya k'arasa RAYHANA tace'' wayyooo Inna ki fito ko in iske ki ga mugu yazo zai kasheni''. K'arasawa yayi har inda take ya fisgo ta ya fice da ita falo sai ihu takeyi.

Bakinta ya buge yace'' marar kunyar k'arya ba kince in na isa in kamaki ba? To gashi na kamaki sai inga mai ceton ki''. RAYHANA tace'' nifa ba 'yar iska bace  ka sakeni kazo ka wani rik'e min hannu d'an isk....'' bata k'arasa ba yasa hannu ya matse mata bakin ya had'e hannuwan ta duk biyun ta kasa ko da motsi ma amma fa duk da haka bakin ta bai mutu ba sai cewa tayi'' yo k'arya nayi? Mu a garin mû bamu iya iskanci ba daman ance sojawa 'yan iska ne ashe haka ne''.

Sakin ta yayi dan ya rasa me zai mata yaji dad'i yarinya bata da tsoro ko kad'an duk yaran gidan su har da na waje ma suna shakkar shi amma banda wannan yarinyar, tabd'ijam lallai sai yayi da gaske.

Yana cikin tunanin ne yaji muryar Inna tana magana daga cikin d'aki tana shirin fitowa, ai kuwa RAYHANA ta kwanta a wajen ta shiga birgima tana ihu tana cewa'' wayyooo Allah na Inna kizo zai kashe ni''. Da gudu Inna ta fito daga d'aki nufo inda suke tana cewa'' me ya faru?"

Kallon inda MUBARAK yake zaune tayi tace'' kai ina magana kayi shiru, me kayi mata wai?"

MUBARAK kuwa zaune yake ko a jikin shi yace'' Inna me kuwa nayi mata, kawai iskancin ta ne''. RAYHANA ta tashi zaune tace'' Inna takani yayi da wannan takalmin k'afar tashi kuma ma...'' ai kafin ta idasa Inna ta shiga tafa hannu tace'' soja muguntar taka har takai nan? Ka kama 'yar k'aramar yarinya kana takawa da wannan k'aton takalmin? A haka zan bari ka kaita gidan ka?"

Kafin MUBARAK yayi magana RAYHANA tace'' ke Inna ai baki bari na gama magana ta ba, banda wannan ma fa kamani yayi ya matse a lungun can yayi ta tab'a min nan''. Ta fad'a tana mai nuna k'irjinta.

MUBARAK yayi matuk'ar firgita da abinda yaji tana fad'a a harzuk'e ya tashi zai kamo ta ta shige bayan Inna.

Inna tace'' a,a lallai soja, wato har ka matsu tun kafin akai maka ita ka kama ta kana lalube mata k'irji ko?"

MUBARAK tashi yayi tsaye ranshi ya b'ace idanun shi har sun sauya kala yace'' yanzu ke Inna har kin kama wannan k'aryar ta ta? Me zanji a jikinta? Ki kalle ta da kyau ina abin sha'awa a nan banda ma cuta ta da akayi aka had'a ni da jidali''.

Inna tace'' kai wallahi ka kiyayeni kaji na fad'a maka, aure kuma ya d'auru babu wanda ya isa ya warware shi ehee''. Saboda tak'aici bai sake magana ba ya fice daga d'akin.

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

Lokaci yana gudu kwanaki na shud'ewa, an had'o ma RAYHANA kayan lefe dai-dai misali duk da abban su MUBARAK yanada kud'i bai son ana bidi'a sosai ko ana b'arnar kud'i komai cikin tsari suke yin shi.

Zainab ce ta kwashi sauran kayan lefen suka kai d'inki tare ma da RAYHANA suka tafi har da auta Faisal dan bâ nisa da gidan su.

Gyara akeyi ma RAYHANA a matsayin ta na amarya, idan ka ganta zaka ce ba ita bace dan tayi kyau sosai daman kyakykyawa ce sai dai zaman k'auye da na birni ba d'aya ne ba dole akwai banbancin abubuwa dayawa babban abun ma wayewa.

Ana washe gari RAYHANA zata tare aka kira mai k'unshi da kitso tazo tayi mata masha Allah kitso da lalle da kitso sunyi dan k'ananu akayi mata kuma ba laifi tana da gashi.

MUBARAK ango damuwa tayi mishi yawa yaga dai da gaske suke tunda gidan su ya d'inke da 'yan, Aysha ma tazo a nan zata kwana, haka Suwaiba ma k'anwar su abban MUBARAK tazo daga k'auye da dai sauran 'yan uwa dan bâ wani gayya za'ayi ba.

Anje anyi mata 'yan gyare-gyare a gidan irin na amare dai komai fes.

Washe gari da daddare abba ya kira MUBARAK a lokacin yana can gidan shi tare da abokan shi suna bashi baki akan ya daure yayi biyayya su zauna lafiya da matar shi wata rana sai labari.

Suna cikin maganar ne kiran abba ya katse su, cikin sanyin jiki ya d'aga wayar tare da yin sallama abba yace'' kana ina ne?"

'' Ina gida abba''. MUBARAK ya bashi amsa.

Abba yace'' to kazo ka d'auki matar ka ku tafi kar dare yayi dan banson wata rakiyar amarya''.

MUBARAK yace'' to abba gani nan zuwa''. Sukayi sallama yayi jifa da wayar har sai da ta watse.

Abdallah ya dafa kafad'ar shi yace'' calm down friend, wai meye haka? Ya kamata fa ka daina saka damuwa a ranka dan kasan aure ba fashi tashi muje mu d'auko amaryar''.

Hararen shi MUBARAK yayi yace'' wacece amarya? Kai ka maidata mace ma har kake kiran ta da amarya karka k'ara min haushi, wai abba ne yace inje mû taho tare banda 'yan rakiya''.

Duk suka kwashe da dariya suna cewa kaga angon RAYHANA kace tafiyar ta amarya da ango ce.

Haushi yasa ya tashi tsaye yaje ya tattara wayar shi yayi gaba ya barsu. Amir ne ya d'aga murya yace'' abokina karka manta dai da kazar amarci''. Sake tuntsurewa da dariya sukayi gami da bin bayanshi.

A falon gidan su abba ne yake mishi nasiha akan cewa ya rik'e 'yar uwar shi amana ko saboda maraicin ta idan tayi ba dai-dai ba ya zaunar da ita ya mata bayani a nutse kar ya sake ya b'ata mata.

Haka ya juya inda RAYHANA take kwance a jikin Inna yace'' 'yata kibi yayan ki sau da k'afa kiyi mishi biyayya ku zauna lafiya kar inji wani abu mara dad'i ya taso a tsakanin ku kinji ko 'yata?"

RAYHANA tayi tsagal tace'' abba ni ba yayana bane mugunta gareshi haka ranar nan ma....'' bata k'arasa ba Inna ta bige mata baki dan tasan abinda zata fad'a.

Haka duk akayi musu nasiha sannan suka musu rakiya bakin motar MUBARAK mama ce tace'' 'yata kiyi bismillah sai ki shiga motar''.

Haka tayi yanda aka umarce ta ta shiga ko a ka ba wani kuka da takeyi sai ma cewa tayi'' Inna shigo mu tafi mana''.

Dariya sukayi mata Inna tace'' oh ni jama'a ke bakin ki bai mutuwa ko? Amare suna kukan rabuwa da gida ke kuwa dad'i ma kikeji ko?"

Murgud'a baki RAYHANA tayi tace'' idan ba zaki je ba shikenan''.

MUBARAK ya shiga mota suna d'aga musu hannu har suka fice daga gidan.....

*Toh fa ya zaman mutanen zai kasance ne?*

*Ku biyoni dan jin cigaban labarin.....*

*Manej it please, wallahi wayata ke bani matsala wani wuri ta shiga na kasa gane mata.*

TSANTSAR WAUTAOù les histoires vivent. Découvrez maintenant