Khairiyyah 04
Masarautar ardo ta kasance masarauta Mai tarin Albarkatu, yayin da jamaar masarautar suka kasance masu mutunta junansu...
Ardo ya gaji mulkin shine tun iyayen da kakanni....
Masauratar ardo ta kasance masarauta ce wadda gaba daya 90% na mutanen cikinta fulanine....
Sarki Ardo kamar yadda ake Kiran Shi....
ARDO ya kasance kamar last name dinda kowa yake anfanidashi a family din....
Asalin sunan sarkin shine MUHAMMAD ALIYU ARDO...
matan Sarki ardo biyu....
Uwar gidan itace sarauniya Harira, amaryar Kuma sarauniya falmata....
Sarauniya Harira ta kasance Yar sarkin gombe..... Ya'yan Sarki Abdullah biyar yayinda yake da mata biyu.. .
Uwargidan watoh Maman sarauniya Harira ya'yanta biyu aduniya wato Harira da Muhammad, Kuma sune manya....
Ita Kuma amayar ya'yanta 3 mata biyu namiji daya....
Alokacin da kaninta yake da shkara 18 ita shekarunta 22....
Ta auri Dan sarkin adamawa wato ardo.... Inda suka kasan Yan uwa na jini sosai....
Shekaranta 1 da aure ta haifi danta, aka Rada Mai sunan kakanshi wato ALIYU HAIDAR...
Bayan suna Allah yayiwa kakannashi rasuwa....
Aka nada Ardo mulki...
Alokacin da haidar yake da shekarun 8 alokacinne aka nada Muhammad a sarauta inda kuma ya auri kanwar Sarki Ardo GIMBIYA KHAIRIYYAH.... Bayan shekaru biyu da aure ta haifi ya mace inda ta rasu bayan haihuwar....
Ranar suna aka samata sunan mamanta wato KHAIRIYYAH Kuma ake ake kiranta da khairat....
Riqon khairat ya koma gurin sarauniya Harira da Sarki Ardo....
Tafiya tayi Tafiya inda yarima haidar ya kammala makarantarsa a Cairo, alokacin shekarar 25 a duniya....
Inda ita Kuma khairat take da shekaru 15 a duniya....
Yarinyar ta kasance ta samu gurbi a zuciyar gaba daya Yan gidan, Gama daga kuyangi, dogarai, jakadai da sauransu....
Khairat ta kasance kyakyawar yarinya domin harda kyanta ya Kara mata farin jini.....
Farace sosai, kana iya ganin jijiyoyinta Tana da idanu kwalakwala Kuma farare tas, cikin idonta yakasance ba Baki bane kwayar idonta brown ne irin light brown dinnan.... Atakaice ce dai Tana da cat eyes nee .... Ga hanci zir, dogo.....Kuma ko da take karama takasance dogowace irin mutanen da jikinsu yafi shekarunsu.....halayenta yaban banta Dana yarima haidar shiyasa ma Basa shiri.......
Yarima haidar ya kasance farine Shima, domin zan iya cewa gadon family dinsu nee hasken fata da kyau....lol..... Dogo nee yafi khairat hanci da hasken fata..... Bai cika dariya ba sai ta Kama.....miskili nee sosai, magana wahala take Mai...... Shiyasa ake ga Yana da girman Kai.....hasali sai Wanda ya zauna dashi sosai zai Gane halayyarshi......
Yanzu da haka yanada asibitin kanshi a garin adamawa...... Matan Basa gabanshi..... Shiyasa har yanzu he is single.... Wasu matan suna zuwa asibitinne kawai Dan su ganshi..... profession dinshi ta fannin ZUCIYA ne....
It's