🌺🌺🌺🌺khairiyyah 🌺🌺🌺

153 8 4
                                    

Khairiyyah 🌺🌺🌺05

Ita kuma yanzu suke gama makarantar........ Za suyi graduating in one month time....

  Khairat Yar science ce haka ma sauran kawayenta.......

Dukansu kansu daya ne, kuma duk class mates nee......

         Khairat kowa Ya shaideta a makarantar su..... Kama daga malamai har dalibai.....
    
    Tana da kokari sosai islamically and Western education.....  Bazaka taba cewa khairat yar sarauta bace, saboda kwatakwata bata nunawa a dabi'unta.... Sai dai wasu abubuwan da baza a rasa ba wanda dole sai ya nuni saboda jinin sarauta dake yawo a jikin ta....... Amman fah idan yan sarautar suka motsa today kowa mah sai ya sha jinin jikinsa.....

   Duk kewayenta masu kokarine...... Anaji da ita a makarantar, haka yan ajinsu na jidaita...... Saboda for the past 5yrs ita take kwato musu dignity dinsu a kowane competition din da ake yi a inter-school.....  Haka mah a wajen makarantar group dinsu ke wining competitions din akeyi..... Har international suna zuwa competitions.......

        Bata taɓa cin second position bah tunda ta fara schooling dinta..... Sai sau daya!.....
   Shima was as a result of rashin lafiyar ta daya tashi..,(wato ciwon zuciyar data gada gurin mamanta)  lokacin suna jss3 ... A lokacin ne taci second position.... Hmmm ranar kamar wacce ta dauko karshen ajin....

   Haka raanar masarautar gaba daya babu lfy yar sarki na kuka..... Shi kanshi mai martaba ranar ko fita fada bai yi ba saboda mood dinshi...... Ranar kowa fata yake yaga walwalarta Amman ina abun yaci tura.....

    Sai da yamma, domin daman ranar ne ranar dawowan yarima daga karatu, zai zo hutu......
  Ai kuwa da akaje dauko shi daga airport, ya saba duk lokacin da zai dawo ana yi mai tarbar girma sosai.....
  Amman yau sai yaga abun da ban..... domin kuwa koda ya shigo fadan ba bosa sarewa nothing......kowa jigum jigum..... Sai da gabanshi ya fadi, domin a tunaninshi mutuwa akayi....

  Ko daya tambayi fada wanshi cewa sukayi.... Mai martaba ne..............

   Bai bari ma suka karasa ba ya kasa da gudu ya shiga cikin fada... A tunaninshi mai martaba ne babu lfy ko ya mutu......yana shiga part din arfo ko sallama babu ya shiga.....

  Domin kuwa tun daga bakin part din yake jin sheshekar kuka, kuma bana mutum daya ba!!!

  Yana shigowa ya fara zazzzare ido yana cewa ina yake? Ya mutu ko? Innahlillah wa innahilaihi rajiun......jiyuwa duk sukayi suna kallon shi......

Ita kuwa khairat ganin yanda yake ta zazzzare ido, ga fuskan tausayi kuma idanunsa har sun fara hawaye.....   Kwai sai ta fashe da dariya harda rike ciki..... Kawai sai jin Muryar mai martaba yayi yana cewa alhamdlh.........   Ai kuwa ya juyu tana kallonshi baki sake...... Ai kuwa sakin bakin da yayi ya kara sa khairat fashewa da wani dariyan kamar wata zararriyi harda hawaye ta...... Kallonta yayi rai abace. Na dariyan da take mai... Ya tambayi zainab Meya faru ... Ta zayyane Mai komai.... Ranshi ya kara bace wa sosai.... Ita kuwa sai dariya take yi tana nuna shi............

Inci gaba?

khairiyyahWhere stories live. Discover now