Don't forget to vote, comment and share dan Allah. Nagode❤❤❤
Mutane ne suke ta kai kawo a harabar gidan. Wani gida ne tafkeke me bene, bayan benen kuma gidan bangare uku ne. Gaban gidan ya sha fulawoyi masu ban sha'awa. Shige da fice kawai ake tayi da kwanukan abinci da lemuka iri iri. Wasu masu shige da ficen mata ne wa'anda ba ma a gayyace su taron da akeyi ba amma saboda su sa mu abinci sai suka shiga gidan kamar su ma sun zo taya murna ne. Wasu kuma yaran su suka tura karbo abincin. Kai qarshe ma har almajirai ma basu abincin akeyi saboda komai a wadace akayi shi. Masu gidan mutane ne wanda Allah ya musu arziqi ya kuma basu zuciyar taimakon mara sa qarfi.
Wasu maza ne kusan su biyar ko shida a gefe sun zagaye daya a cikinsu sun saka shi a gaba sai zolayarsa suke yi. Biyu daga cikinsu kuwa basa cewa komai illa faman danna waya da suke tayi in anyi abun dariya kunnen su yaji, su dara.
Daya a cikin mazan ne ya kada kai yace "wai dan Allah duba mun ku gani. Wai nawa ma Engineer yake ne amma har ya tara yara hudu. Wai dan yaron nan dashi wasu zasu bude baki su ce masa baba kuma ya amsa. Kai abun da mamaki wallahi." Dariya suka sheqe da ita har sai da suka kusa qwarewa. Daya a cikin su mai suna Khalid ne ya karkace yace
"Toh wai kai Sadiq tsaya tukun, tsakanin kai da Engineer waye babba? Engineer ya bawa shekara talatin baya fa, ina yarintar take a nan?" Ya karashe maganar tasa yana cin naman kaza.
"Kai ma dai ka fada. Kasan shi Sadiq rayuwar turawa yake yi. Wai life starts at forty, kaji fa nikam idan nayi arba'in ay na fara tanadin lahira. Allah dai ya kyauta." Engineer Uthman wanda ake ta tsokana neh yayi wannan maganar.
"Yallabai kayi shiru," Uthman ya zunguri Sadiq din wanda yayi nisa a tunani.
"Kun dan sa jikina yayi sanyi amma kar ku damu nima ku saurari biki na nan da qarshen shekarar nan." Dage kafadar sa yayi yana wani ciccika wai shi sabon ango. Dariyar suka qara yi kafin Uthman ya dan kalli agogon sa yayi tsaki.
"Me kuma ya faru eyyi?" Abokan suka hada baki suna tambayar sa. Murmusawa yayi kafin yace "hmm ku bari kawai, nifa ba a san raina ake yin sunan nan ba. Subaiha ce ta dameni gashi duk mutane sun cika mun gida tun safe ko gamuwa ba muyi ba." Ya karashe maganar kamar wanda ya bada labarin abun tausayi.
"Oh ni Habu. Wai dan Allah wani irin so kake wa Subaiha ne? Kun ajiye yara uku ga na hudu amma har yanzu ka mayyance mata. Anya kuwa ba..." Daga masa hannu Uthman yayi.
"A'a babu ruwanka tsakani na da mata ta. Ina masifar son ta kuma tsakani da Allah." Ya qare yana hararar abokin nasa.
"Toh mijin tace, ko ince mijin Haji..." Tauu Sadiq yaji Uthman ya kai masa duka baya. Dariya aka sake yi.
"Allah ya huci zuciyar ka Romeo na Juliet. Wannan soyayya haka? Ko hurul ayn ce Subaihan nan ay sai haka." Uthman ne ya tabe baki kamar baze bashi amsa ba sai kuma yace
"Kai ka sani dai, kaje kayi aure zaka ban labari amma ka tsaya sai aykin karaya zukatan yan mata." Bai jira amsa ba, ya taka zuwa bakin qofar gidan. Leqawa yayi yaga mutane danqam ko wajen taka wa ma sai mutum yayi sa'a zai samu ya wuce.
Uthman irin mazan nan ne masu kunya da nutsuwa. Ba shi da hayaniya kuma bai cika shiga sabgar da ba tashi ba amma kuma idan aka qure shi to tabbas zai dau mataki qwaqqwara. Fasa shiga yayi ya koma suka cigaba da hira da abokan sa.
***
A dayan bangaren gidan kuwa, wata mata ce zaune a cikin daki a takure duk abun duniya ya ishi rayuwar ta. Ji take yi kamar ta shaqe kanta saboda baqin ciki. Gashi dai yau ranar farin ciki ce a wajen mutanen gidan amma ita kam baqin ciki, takaici da qunar zuciya sun mata dirar mikiya a rayuwar ta. Rabon ta da farin ciki kuwa har ta manta, ita bata san me yasa yau abun yafi tunzura ta ba.
YOU ARE READING
Dare daya.
RomanceDare daya Allah kan yi bature. Dare daya ya isa ya kawo canji ga rayuwar dan Adam. Dare daya mutum zai iya aykata abunda zaiyi silar shigarsa aljanna ko wuta. Dare daya zai iya gina farin ciki. Dare daya zai iya ruguza farin ciki. A dare daya rayuw...