Haushi ne ya cika Sa'adatu da taga ashe ba ta same shi a cikin ba sakamakon tarewa da yayi da hannun sa. Ganin hakan yasa duk suka fasa tafiya asibitin aka ce bari kawai a yi treating dinsa a gida.
Cikin yan mintuna kadan sai ga likitan nan yazo a ambulance wacce take dauke da duk wasu abubuwan bayarda taimakon gaggawa.
Babu wanda yake ta kan Sa'adatu duk hankalin su ya karkata zuwa ga lafiyar Bashir.
Yara ma tuni direba ya kai su makaranta ba tare da sun san abunda yake faruwa ba.
Gumi ne ke ta faman zuba a jikin Bashir saboda tsananin azabar yankar.
Allura likitan ya hada, yayi masa wacce zata taimaka wajen sassauta zafin.
Kallon hannun yayi yaga gaskiya yaji ciwo sosai dan kuwa sai anyi treating dinsa sosai an dinke in ba haka ba kuwa ya tashi daga ayki.
Dinke hannun ya soma yi. Bayan ya gama ne yace dole Bashir din ya dinga zuwa asibiti a gasa qashin hannun sakamakon tsagewar qashi da aka samu.
Nan dai ya gama bayanan sa, ya bayarda magunguna yace zai dawo da yamma yayi masa allura.
Godiya suka yi masa kafin ya fice yana jinjina al'amarin.
A harzuqe Uthman ya tashi yayi kan Sa'adatu kamar wanda yake shirin kashe ta.
Bashir ne ya daga masa hannu alamun ya dakata. Saboda yana bawa yayan nasa girma sai ya koma ya zauna yana huci.
Ita kuwa Sa'adatu ko a jikinta. Dan kuwa ko kashe ta za'ayi domin ta kashe mijinta batayi rashi ba.
Subaiha ce ta shigo da plate din fruits ta ajiye tana yi masa sannu. Gyada kai kawai ya iya yi. Duk da anyi allurori da dama amma har yanzu yana jin zafi.
Tashi sukayi suka bar parlourn. Daga Bashir sai Sa'adatu. Suna gama fita ta mayar da idon ta kansa. Ji take kamar kawai ta tashi ta shaqe shi kowa ya huta.
Wani bangaren zuciar ta kuma lallashin ta yake yi akan tayi haquri Allah yana tare da masu haquri... Saidai ita ji take ba zata iya haqurin ba saboda an kai ta maqura.
Harara ta shiga ayka masa, ba yanda ya iya sai ya sunkuyar da kai. Tsaki taja sannan ta nufi hanyar fita.
"Sa'adatu."
"Sa'adatu." Ya sake maimaitawa amma bata tsaya sauraron sa ba.
***
Buguzum buguzum Hajiya Tafada ta shigo gidan cikin tsananin fushi. Tana zuwa ta banko kofar babban falo. Uthman ta gani a kishingide gefe kuma mai jinya.Qarar kofar ne ya saka duk suka juya a razane suna kallon Hajiya.
Tana zuwa daidai saitin Bashir ta dauke shi da mari. Ya bude baki zaiyi magana ta sake dauke shi da wani.
"Kai! Idan zaka iya salwantar da rayuwarka ka rasa ranka har abada to ni uwar da na haife ka ina son na cigaba da jin numfashin ka a doran kasa..." Uthman ne ya katse ta yace
"Hajiya wai me ya far..." Bai karasa ba shima ta daga hannun ta sama alamun ya dakata.
"Yanzun ba da kai nake ba amma zan dawo kan ka." Hadiyan yawu yayi ya koma ya zauna.
"Duba min nan. Ka karanta a fili naji," ta sa hannu a jakarta ta ciro wayarta. Juyar da wayar tayi dai dai fuskar Bashir tace ya karanta abun da ya gani.
Shi kuwa Bashir tsananin mamaki ne ya saka ya kasa furta komai. Hadiyar yawu yayi ya kalle ta.
"Tunda you've become dumb all of a sudden, bari ni in karanta maka." Hajiyan ta harare shi kafin ta fara karantawa a fili kamar haka.
YOU ARE READING
Dare daya.
RomanceDare daya Allah kan yi bature. Dare daya ya isa ya kawo canji ga rayuwar dan Adam. Dare daya mutum zai iya aykata abunda zaiyi silar shigarsa aljanna ko wuta. Dare daya zai iya gina farin ciki. Dare daya zai iya ruguza farin ciki. A dare daya rayuw...