"B zaki zana mun a tafin hannun," yau kam ran Sa'adatu kamar anyi mata albishir da aljanna. Jin ta take fes yayinda ake yi mata lalle ja da baqi. Da safe daman anyi mata kitso jiyan ranar kuma taje anyi mata gyaran jiki.
Murna kamar me, Bashir ya mata waya yace yau zai shigo Nigeria. Yaran ma duk ta shirya su tsaf tsaf dasu ta gaya musu cewar yau baban su sai dawo. Su ma sai nishadi suke yi.
"Kin ganki kuwa kamar wata sabuwar amarya? Kai yau babban yaya bazai gane ki ba ma." Subaihan ta fada tana jijjiga jaririyar ta.
Siririyar dariya Sa'adatun tayi kafin tace "kin ji Subaiha da wani zance. Daga yin dan gyara kuma?" Mai yin lallan ce ta dago ta kalle su ko me take saqawa a ranta oho.
***
Gaba daya dai wunin ranar a gyare gyare Sa'adatu ta qarar dashi. Itace share can, goge can. Tana ta hidima iri iri. Ga abinci nan duk ta dafa kala kala, different continental dishes sai wanda Bashir ya zaba ya bari.
Gidan ko ina qamshi yake gwanin sha'awa. Kallon agogo tayi taga qarfe tara na dare tana neman yi. Yaran har sunyi d'okin sun gama sun koma part din su. Nan hankalinta ya soma tashi.
Qarfe shida sukayi dashi zae shigo gida a cewar sa sai gashi har tara.
Taso ace itace ma zata je dauko shi a airport amma sai yace wai tayi zaman ta zai saka direba.
Dafe kanta tayi tana tunani. To ya na ina? Sai Hajiya Tafada ta fado mata a rai tace wataqila ya fara wucewa can ne tunda ya dade baya gari.
Wayar ta ta shiga nema ba ta ganta ba sai ta tuna ashe ta bawa daya a cikin yaran. Tashi tayi ta nufi sashen nasu ta wata qofa da take linking sashen nasu da qofar parlourn ta ba tare da ta bi ta waje ba.
"Maama wai har yanzu Abbu bai dawo ba?" Ummi ta tambaye ta.
"Eh, bani wayar in kira muji." Tayi murmushi kafin ta juya.
"Shi Abbun nan wallahi sai a hankali kullum baya nan. Ni bana son shi ma." Har ta kai bakin qofa sai taji Ummi tana gayawa daya a cikin yaran.
Dawowa tayi ta zauna a gefensu.
"Abbu baban ki ne kar na sake jin haka daga bakin ki ko? Yana tafiya ne saboda ya samo kudin da ake biya muku school fees kinji?" Sa'adatun ta dage gira.
"Yes amma Abbun su Jawad baya tafiya kuma yana biya musu school fees." Ummin ta tsare uwar ta ta da ido. Sa'adatu ta sani cewa ko wacce irin amsa ta bayar sai Ummi ta samu ta cewa.
"Ni dai na gaya miki. Idan na sake ji sai na yanke bakin nan." Sa"adatu ta fice ba tare da taji amsar yar ta ta ba.
Har zata koma sashen ta sai tace bari taje dakin su Maryam ta ga me suke yi.
Tana zuwa kuwa ta tarar da Maryam da Madina suna cacar baki.
"Me kuma ya faru?" Ta fada fuskar nan a daure.
"Wai Maama kinga sis Maryam dole sai daukar min diary dina kuma bayan kowa ya sani diary sirri ne," Madina ta tabe baki kamar zatayi kuka.
"Wai yaushe zaku girma ne? E? Ke Maryam shekarar ki sha hudu kin kama ta sha biyar. Ita kuma sha biyu me yasa baza ki ja girman ki ba?"
"Maama yi haquri na dena."
"Yayi miki kyau. Ke kuma kece qarama bana son raini." Ta sake yi musu kallon gargadi kafin tayi ficewar ta. Ko waccen su gadon ta ta hau tana jin haushin yar uwarta.
Ring
Ring
Ring
Ring
YOU ARE READING
Dare daya.
RomanceDare daya Allah kan yi bature. Dare daya ya isa ya kawo canji ga rayuwar dan Adam. Dare daya mutum zai iya aykata abunda zaiyi silar shigarsa aljanna ko wuta. Dare daya zai iya gina farin ciki. Dare daya zai iya ruguza farin ciki. A dare daya rayuw...