Salam alaikum.
Dare daya by #naanaah01
*unedited*
||||||
Zaune take kan kujera tana shan inabi tana kallon labarai a TV. Za'a iya cewa idonta yana kallon TV ne kawai amma hankalin ta baya kai sam. Motsin da ta ji ne yasa ta dan juya taga daya daga cikin yaran tsaye a bakin qofa tana jiran abata izinin shigowa.
Murmushin da bai qarasa zuci ba Sa'adatu tayi gami da gyada kanta alamar ta bayar da izinin shigowa. Madinah ce ta mayar da murmushin da ya tsaya a kan lebenta kafin ta shigo.
Gefe guda ta samu ta zauna. "Nima zan sha grapes," ta fada tana kallon mamanta. Tray din Sa'adatu ta dauka ta nufi inda Madinah ta zauna. Tana zuwa ta zauna a gefe, ta dan shafa fuskar ta kafin tace
"Yaya kike? Dafatan babu wata damuwa a tare da ke?" Shiru ne ya ratsa ba tare da Madina ta ce mata komai ba. Hakan kuwa yayi wa Sa'adatu ciwo amma sanin halin yarinyar ya saka kawai ta kau da kai. Sun dauki kamar mintuna biyar babu magana.
"Me yasa ba kya magana da Abbu?" Daga kai tayi ta kalli maman ta tana jiran amsa. Ita kuwa Sa'adatu sai tayi sauri ta dauke idonta daga kanta. Ita kam yaran suna bata mamaki, saboda miskilancin su sai take tunanin basu san abunda yake faruwa ba a cikin gidan. Tayi tunanin baza su taba lura akwai matsala tsakaninta da Bashir ba.
"Waye yace miki haka? Muna yin magana mana." Sa'adatun ta fada tana sanya wani murmushi a fuskarta dan ta samu Madina ta yarda da maganarta. Tabe baki taga Madinah tayi, bude bakin da zatayi tayi magana, sai ga Bashir ya shigo.
Sa'adatu ce ta danne zuciyarta ta miqe ta je gabansa ta riqe hannun sa suka qaraso parlourn.
Shi kuwa Bashir har cikin ransa yayi mamaki. Hantar cikin sa sai da ta motsa sabida tun ranar da abun ya faru, Sa'adatu ko inuwar ta bata bari ta hadu da tasa balle a kai ga riqe hannu.
Silently Madina ta miqe ta fita ba tare da ta ce komai ba.
Daure fuska Sa'adatu tayi gami da sakin hannun sa. Fuskar nan babu walwala ta kalle shi tace
"Me kake gayawa yarana?" Hannun ta dora a kan qirjinta tana jiran amsar sa.
Rufe idon sa yayi kafin yace
"Ba abinda nace musu. Su suka gani da idon su." Ya nemi guri ya zauna, yaja tray ya fara shan apple.
"Okay kai ka sani." Ta juya zata fice ya riqo hannunta. Kallon ta yake yi har cikin idonta, kallon yana dauke da saqonni da dama. Saqonnin da ita kadai zata fahimta.
A hankali taji tana neman ta yafe masa su dawo normal. Sai kuma wani bangaren zuciyarta yace mata Bashir bai cancanci yafiyar ta ba. Hakan yasa ta fisge hannun ta ta qarfi tana watsa masa harara.
"I want to explain." Ya fada briefly, daman shi bai cika doguwar magana ba.
Kallon sa tayi sannan tayi dariyar da bata kai zuci ba.
"You want to explain what? What Bashir? Sanda nake buqatar explanation ka bani ne? Wani excuse kake dashi na tafiya ka bar ni for over five months? Da ace karatu kake yi sai in daga maka qafa amma ba haka bane. Ina so ka sani cewa, na san a cikin five months dinnan you have been in Nigeria five times; Abuja to be precise, if you were so occupied that you can't come here, sai ka kirani a waya kayi mun bayani amma gaba daya sai ka nuna min baka sa qafa a Nigeria ba. Bashir dan Allah dan annabi ka sake ni na huta!" A yanzu, hawaye ya gama wankewa Sa'adatu fuska. Radadin da take ji a zuciyarta ya gwaraye duk jikinta.
Wata sabuwar tsanar mijinta na qara shigar ta.
"I'm sorry amm..." Katse shi tayi.
"You're what? Sorry fa kace Bashir. Lallai ka samu matsala a kai!" Ta fada tana tafa hannu. Tun kafin ya bata amsa ta fice daga parlourn hadi da banko masa qofa.
YOU ARE READING
Dare daya.
RomanceDare daya Allah kan yi bature. Dare daya ya isa ya kawo canji ga rayuwar dan Adam. Dare daya mutum zai iya aykata abunda zaiyi silar shigarsa aljanna ko wuta. Dare daya zai iya gina farin ciki. Dare daya zai iya ruguza farin ciki. A dare daya rayuw...