Disturbance

1K 56 4
                                    

Fotowar su daga masallacine suka ji saukar ruwan sama kamar da bakin kwarya hakanne yayi sandiyar komawarsu domin yin sallar isha,hakanne kwa ta kasance bayan gama sallar tasu ne dad ya tsaya da wani friend dinsa Alh Ibrahim suna gaisawa ,tsayawa abid yayi a harabar masallacin yana kallon yadda ruwan yake gudu abin sha'awa ,tunowa yayi da rayuwarsa tada wadda take mai dadi da farin ciki wanda baitaba zaton zai gusheba saigashi a yanxu ta zamo tarihi ,murmushin karfin hali yayi daya tuno da babyn ammy wadda ada ruwa na tabata zata sume musu sabida yanayin jikinta da bayya son ruwa.tabashin da dad yayine ya dawo dashi daga duniyar tunanin daya shiga,my boy mu tafi gida ko kana tsoron ruwanne?murmushi yayi baiyi magana ba coz idan ya tuno da irin abubuwannan baya son magana.
Dady ne ya kamo hannunsa suka taho gida da sauri,da yake ba nisa ne da gidan nasuba zuwa masallaci sayya kasance ba su wani jike da yawa ba.Isar keda wuya suka tarar da already mom ta gama shiraya musu abinci ,Dan haka wajan dining din Dad ya nufa domin cin abinci.hankali ya me hawa benin donmin komawa dakin shi,Dad ne ya kira shi
Yazo yaci abinci,girgiza masa kai yayi kawai ya haura sama,tsayawa momy tayi kikam tana kallon izzar yaron da kuma mamakin yadda ubansa baya taka masa birki ,ta howa tayi tana murmushin takaici ta zauna a gefen dady tana cewa,maybe son wani abu na damunsa kwana biyun nan coz tunda ya kama degree Dinnan naga ya tsiri zaman daki da rashin walwala akoda yaushe nayi iya yina na ya fada mini damuwarsa yaki(nikwa gwalo ido nayi nace toh fa yau ake sharaton) shiru Dad yayi yana sauraron matar tasa ,sannan yayi gyaran mirya,nima na kula yana boyemin damuwar shi kwanakin nan dukda dama bamai yawan magana bane amma zan tuntubeshi naji .
Bayan sun gama cin abincin ne dady ya tashi yabi bayan yaron nashi daki,tsaki momy tayi tana kwafa tana me kallon dakin Abid, magana take yi kamar wata zauyacciya ,kwaji dashi ne wlh daga kai har dan naka damuwa ai yanxu kuka fara shigarta sai kun yabawa aya zakin tane(ni kwa cewa nayi idan Allah ya baki iko ba)

Bangaren dady kuwa yana bude kofa da sallama ya tarar da yaron nashi kan sofa a zaune wayanshi na faman ringing amma kamarma baisan tana yiba,kulle kofar da dady yayi ne yayi sanadiyyar dago fuskarsa wadda tayi jajawur da mamaki dadi ya karaso wajanshi,son lpy meke damun ka?talk to me mana son I said what happened? Duk dady yabi ya rude .
Dago da kansa yayi daga kasa ya tsugunna gaban dady ya kamo kafafuwansa yana xubar da kwalla yana fadin dady plss I want see my family,  dady i talking about my mom ,my baby ,my granny my friends and my my wani zautaccen kuka fa kubuce masa yana fitar da sheshshekar kuka sakin baki dady yayi yana kallon yaron nasa nunawa yayi da rabon da Abid ya ambaci Nigeria tun  a watan da duka barota bai kara kiran wata banzar kasa Nigeria ba(abakinsa kenan) wani bacin rai nai ya taso masa amma kasan zuciyarshi fal take da tunanin abubuwa da yawa Wanda baza fassaruba,taba shin da Abid yayi ya farfado daga tunanin da yake ,kallonshi Abid yayi amma sai da yaja da baya sabida irin bacin ran da ya hango a idon dady Wanda rabon shi daganin wannan bacin rai a idanuwan mahaifin nasa tun last 5 years Wanda abunne yayi sanadiyyar barin kasar tasu ta haihuwa.

Jikin shine yayi sanyi domin rashin ganin  samun nasara awajan Dad din nashi,saukar dakai kasa yayi yana shashshekar kuka Wanda yake yinshi bil hakki da gaskiya,shi kansa dad yayi mamakin son dinshi coz tunda yake dashi wato tun yana yaro ba karamin Abu bane yake sashi kuka ba tunda suka sauka akasar  island kuma baita ganin hawayenshi ba saidai muguwar damuwar data mishi yawa ita ma kuma baya nuna dadyn nashi.zama dad yayi yana mai kallon yaron nashi da wani irin kallo yace,duk duniya ba Wanda nake so  a yanxu kamar kai da kuma son nunawa farin ciki amma hakan baya nufin nabarka kayi duk wani Abu da kake so Wanda yake zai batan rai,zan bari kaje ko wacce kasa amma badda Nigeria ,idan har kaga kaje Nigeria toh fin karfina kayi,dago idonshi Abid yayi Wanda yayi wani irin colour yace,bana fatan ranar da zan bijire maka Dady but gani nayi ba kasar da yafi nayi service irin kasata wadda hakan dole a can sannan ina sha'awar taimakawa yan kasata amma idan hakan na nufin bata maka rai na hakura dady ,yana fadan haka ya shige toilet ya datse ,kikam dady yayi yana sauraran dannasa coz yasan ba kowanne da bane azamanin nan zanyi biyayyar da Abid yake masa ,tashi yayi yana buga masa kofar toilet din domin ya fito amma shiru yaki fitowa daga karshe da Dad yaka 1:30 na kokarin yi ya tashi jiki a sanyaye zai koma daki.
Motsin tahowarsa da momy taji ne yayi sanadiyyar saukowa da sauri ta wuce part dinta tana jan numfashi domin ganin aikinta yana neman tabalbalcewa tun kafin aje ko ina ,bata kwanta ba saida ta kira aminiyarta Hajiya lami tana fada mata abin data jiyo saida suka warware yadda za suyi sannan suka kwanta bacci.
Ban garen dad kuwa yau ko takan mom baibi ba said faman juyi yake akan akaan bed yana tunanin muguwar kyamar da yakewa kasar tashi ta haihuwa Wanda idan asan ransa ne yanaso yaji ya manta da komai daya faru last 5 years amma abin yaci tura ko yayi niyyar mantawa amma said yaji kamar kara mar tsanarta ake da wannan tunani bacci yayi nasarar dauke shi.
Jin gidan yayi shiru ,hakan saiya bashi nasarar bude toilet din ya fito ,jikinshi ajike sai rawar sanyi yakeyi a haka ya samu ya shirya ya shimfida sallaya domin kaiwa Allah kukansa ,bayan ya gama sallar ne yazo kwanta ya shiga tunanin da ya saba jiyayi abin na Dan lafa masa ba kamar da ,da haka har yasamu bacci barawo ya sace shi.
****************************************Da asussuba Dada ta shi tayi sallah bayan ta gama azkar ne 5:30 ta hadawa babynta ruwa mai zafi domin jin jikin haryanxu da zafi ta taimaka mata ta kaita toilet tayi wanka da kyar domin acewarta dadan tayi mata tace ta fara kirgyan dangi baza tayi ba shiru Sabrin tayi tana mamakin wannan suna,bayan ta gama ne duk da dauriya kawai take but ita tasan ciwon Da cikin nata yake mata .
A gaggauce suka shirya domin 6 jigin nasu zai daga, suna isa airport kwa bada dade waba jirginsu ya cillah California.
Bangaran ammy kuwa tun safe ta isa asibiti ta samu doctor mukhtar tayi masa baya nin yarinyarta da zai duba mata domin  doctor mukhtar ma bada ga nanba wajen kwazo domin acewar ammy baza ta iya ganin abin dake damun babyn nata ba sabida gudin abun dazai daga mata hankali.
Karfe 10 dadai su Dada suka iso California wata muguwar faduwar gaba CE ta risketa ayayin da shigo kasar domin inbadda amanar sabrin da take wajanta da ba abun da zai kawota wannan kasar.
Sunan su suka gani barobaro awajan Wanda yazo daukarsu ,kyakykyawan saurayine ya na dauke da murmushi ,isa wajansa sukayi direct ya wuce dasu asibitin da ammy take Wanda ya kasance nata ne na kashin kanta.isarsu asibintin keda wuya Dada taga abinda ya tada mata hankaki Wanda ba komai bane sai katon hoton da aka kafe dasunan Fatima special hospital ,batasan lokacin data fashe da kuka ba Wanda yayi sanadiyyar farkawar sabrin daga bacci ,kuka itama ta fara ganin dadar tata acikin damuwa,kasa fitowa Dada tayi saida ammy ta fito acikin kyakykyawar shigarta ta likitoci ta iso wajan su dadar ganin yadda take kukane tasan dama arina ,tasan tabbasa Dada taga hoton mafi soyuwar yar tata kafe a sibitin nan saitayi kuka .
Rungumeta ammy tayi tana bata hakuri itama tana sharen hawayen nata ,tsayawa kawai sabrin tayi itama tana kallon hoton wadda taji lokaci guda matar ta kwanta mata mai tsananin kama da ammynta .kamo hannunta ammy tayi ta rungumeta tana mai shafa kanta ,suka fita harda Dada wadda ta tsagaita da kukan nata ,suka shiga asibitin domin yin abun da ya kawo su.bayan shigarsu direct aka shigar da sabrin ciki domin duba lafiyarta ,zama su Dada sukayi a office din ammy Wanda yake birjik da pictures din wata mata tana 22 yrs an rubata proud to be a doctor ajikin hoton Wanda kana kalla zaka san ranar vocation dinsu ne na university Wanda graduation gown ne a jikinta fuskarta dauke da smile,Dada CE ta goge hawayen daya ke xuba afuskarta,ta tashi tace wa da ammy ta kaita masaukin domin zamanta cikin asibitin na kara tuno mata da tabon da maza ta taba mantawa da shiba,ba yadda ammy ta iya ,ta dauki Dada domin kaita gida .
Kafin ta tafi ne take sanarwa doctor samir friend din doctor mukhtar zata je gida ta dawo su kafin a gama duba mata babynta duk yadda ake ciki akirata kafin ta dawo.
Ta fiya suka yi gidan ammy a mota kowa shiru yayi yana tuna baya, isowar su keda wuya aka wangale musu katon get suka shige,gida ne na gani na fada wanda take cke da kayan more rayuba da xarar kaga wannan gida zakasan cewa ba karamin mutanen ba su Dada.
Kayan abinci tasa aka Jere mata Wanda already an gama komai dama, bandaki Dada ta shiga domin haramar yin sallah ,wayyar ammy ce tayi ringing akaro na uku kenan tayi sauri ta yi picking Dan ganin Wanda yake kira sallahma tayi ta fara amsa kiran baka jin abin da ake fada a daya bangaren sai kawai innalillahi da ammy take ta faman ambatawa bata San lokacin dawayar ta tarwatse a hannun taba ,fitowar Dada daga toilet yayi daidai da faduwar wayar kallon ta Dada tayi ta hango tashin hankali cikin idonta Wanda haryayi jajawur da gudu ta isa wajan Dada ta rungumeta ta saki wani wahalallen kuka tana Dada karmu rasata dagota Dada tayi tana tambayarta waye CE?

Ina zuwa.
Follows, vote and comments plss.
Instagram @zainab Dangyatin.
Zeeluv CE.

ZAKI SAN SO NE KO KAUNA?Where stories live. Discover now