Kwance yake cikin bishiyun dake island,wajen shakatawa ne Wanda ya kasance mafi soyuwar duk wani bil Adam,da wuya ka kasance a wannan waje ba tare da ka ji dadin jikin ba,waje ne Wanda ya kunshi abubuwan jin dadi bila adadin awajan,saidai daka karanci yanayinshi zaka fuskanci akwai abun dake damun shi aransa,tashi yayi karo na biyu ya zauna ya dafe kansa yana Jan tsaki Wanda ya zame masa jiki akoda yaushe,a kullum idan ya tuna da dafin dake xuciyarsa saiya ji inama ace farin cikin sa na da ya dawo kareshi but saidai ya riga yayi loosing abubuwa da yawa awajansa neman hanyar dazai gyara yake gashi yarasa ta inda zai fara.
Dafa shi yaji anyi ta baya ana tapping bayanshi Wanda yakasance ba kowa bace face Mom dinshi,maimakwan yaji relief a ranshi sai kishiyar hakan yaji ,murmushin yake yayi ya dago face dinshi ya kalle ta yace ,anything thing ?kallonsa tayi a yangance ta yi smiling, axuciyarta ji take kamar ta yi hauka da irin I don't care attitude dinshi dayake nuna mata duk da tasan cewa for d sake of Dad dinshi take rage masa waasu abubuwan but if not da sai yasha mamakin ta a matsayinta na wadda tahaifeshi.miryar Dad ce ta katsesu da tunanun nukan da sukeyi,my boy lpy na ganka so silent gashi mom na tambaya kayi shiru ,smirking yayi yana mikewa tsaye domin kansa da ya faramar ciwo ,no dad I'm having headache ne kawai,kallonshi mom tayi ,tai fuskar tausayi tana masa sannu ,kamo annunsa Dad yayi sukayi gaba domin tafiya gida.
A motar ma haka ta kasance mom na driving shi da Dad na baya suna hira sama sama Wanda yakasance dabi'ar sace hakan bamai son surutu bane .i so warsu gida keda wuya ya haura sama domin sakarma kanshi shower.
Wannan ba kowa bane face ABID BIN OMAIR saurayi Dan kimanin 22yrs yanxu haka ya gama university a island iinda ya karanci law a nan kasar yanxu haka service yake son zuwa Nigeria but bai San yadda abin zai kaya ba.
Shigar sa wanka keda wuya ya sakar ma kansa shower Wanda ko kayan jikin nasa bai cire saboda ciwon kan da yake damunsa ,da haka har ya shude 20mint sannan ya samu nutsuwa ta dawo masa ,bude sleepy eyes inshi yayi wadanda suka yi ja da kuma kara girma sabida yanayin da yake ciki. Kyakykyawa saurayi ne Wanda tsarin kyauwayin shi daban yake ko a samarin kasar,ko lokacin daya school hankalin ko wacce mace akansa yake sabida tsarin surar da Allah yayi masa saidai kwata2 magana bata dameshi su Kansu lecturers din behaviors din ABID na basu mamaki sautari suna kiranshi har office su tambayeshi matsalarsa but one thing da kullum zaiyi shine xuba musu ido ba tare da ya basu amsa ba ,amma duk da haka baya sa ya fadi exams nashi infact ma shine overall best a set dinsu shiyasa ko da yaushe malaman suke alfahari da shi kasancewar shi mai basira gashi baya da hayaniya,but ako da yaushe yana kokarin boye damuwar sa awajen mahaifin sabida gudun tashin hankalinsa sabida duk duniya ba Wanda yake so da kauna kamar ABID Wanda yake shika daine awajansa.Fitowar shi daga toilet keda wuya yazauna ya fara shafe shafe lotion ahankula kamar Wanda ake shafawa baby ,Wanda yakasance Al'adar sace hakan komai a nitse.Kirayen kirayen sallah yaji an fara hakan ya bashi damar sa kayan shi yayi haramar tafiya masjid,kanin shi tiraren da Dady yaji ne yayi sanadiyar kallon part din ABID,my boy are u done ?daga masa kai yayi ya tsaya alamun yana jiran dadyn ne ,murmushi dady yayi ,yana mamakun muskilancin yaron nashi suka kama hangar tafiya masjid din dake kofar gidansu Wanda yake Dadyn shine ya gina.
*****************************************
Isar su asibitin keda wuya ,ganin motar dake shigowa ne ya bawa ma'aikatan asibitin damar saurin iso wa motar sanin matsayin wadda ta shigo asibitin da hanzari suka bude wa Dada kofa ,hakane ya bata damar fitowa ,hannun tasa ajikin babyn nata domin daukar ta,karr ta bude idon ta akan Dada Wanda suka yi wani irin colour, murmushin yake ta sarma Dada tana kokari fitowa daga motar ,Dada tai saurin riko ta sabida kokarin faduwa da takeyi,amma tai saurin tallafeta tana kamo hannun ta,babyna sannu kinji ,jijjiga kanta tayi tana mai fitar da kwalla daga idonta ,ana haka saiga doctor Aqaq nan yazo ya durkusa yana gaida Dada ,riko hannun Sabrin yayi yaji zafin jikinta ,da sauri ya kalli Dada cikin yanayin damuwa yake magana,dama Dada babyn kice ba lafiya?eh wlh son narasa mai ke damunta.dagowa tayi akaro na farko tana kallon doctor Aqaq, smiling yayi mata yana mai daukar ta ya tafi ,ya shige office dinshi ,Dada ta bisu abaya.
Kwantar da ita yayi ya fara aikinsa domin duba abin da yake damunta ,shiru Dada tayi azaune tana danne dannen waya domin kiran ammyn Sabrin ,jiyowa yayi ya kalli Dada da damuwa a face dinshi yana tambayarta,Dada bayan zazzabi akwai wani abun ne ?ajiyewa wayar tayi ta fiskanceshi tace, tace min da ciwon ciki dai but bata fadi specific gun da yake mata ciwon ba,komar da kanshi yayi kanta Wanda tuni baccin wahala ya dauketa,kara saita na'urarsa yayi domin duba ainahin abun da yake damunta,cire glass dinshi yayi yana kokarin saita numfashi sannan ya kara yima scanning domin tabbatar da abun da yake saidai duk iya inda doctor Aqaq yai da masirarsa bai gano ainahin abinda ke damun babyn Dada ba,toh fah,jiyowa yayi ya zauna kan kujerar aikinshi yana mai fuskantar Dada domin fada mata halin da ake ciki,A gaskiya Dadar mu yanayi iya bakin kokarin domin na gane sanadiyar ciwon cikin amma na kasa ganewa Wanda abun ne yayi causing fever din stiil saidai abari sai madam ta dawo ta duba mana ita, sauke numfashi Dada tayi tana mai gyara zamanta domin hankalin ta daya tashi coz abun dake dagawa Dada hankali a kullum baifi rashin walwalar babyn taba sabida son Sabrin daban yake axuciyar ta ko ammy wadda take matsayin mahaifiya awajan Sabrin baza ta nunawa Dada sontaba.shiru maganar da yakeyi yine ta katse Dada daga nunanin da ya kawo mata kai,Dada wannan ba abin da muwa bane kamata yayi kawai asanar da madam abin da ake ciki,dago kai tayi take cewa,na kira bata picking maybe ta shi wani uzirin nata ne,ana haka kuwa phone din Dada ya fara ringing ,daukowa tayi taga mai kiran nata sannan tayi picking.Zazzakar muryar matar ne ya doki kunnan Dada ,aminci Allah ya tabbata a wajan mafi soyuwar uwa gareni,lumshe ido Dada tayi tana mai bude su Wanda suka cika taf da hawaye domin aduk lokacin da sukaai waya da ammy sai xuciyarta ta raunana saboda abubuwa da yawa da suke dawo kanta,katseta ammy tayi daga tunanin da take,Dadar mu lpy kuwa naji kinyi shiru,duk da ammy tasan tana haka amma shirun yau na dabanne,murmushin da yafi kuka ciwo Dada tayi domin kauda damuwar ta tace,lpy kalau daughter na ya kokari da jama'a ,amsawa tayi da komai normal Dadan mu,tana tambayar ina babynki domin sakayawa ,gauran numfashi Dada ta sauke tana mai cewa,dalilin kiran Dana miki kenan domin baby bata da lpy ,anduba meke damunta but doctor Aqaq bai gano ainahin me yasata ciwon cikin ba Dan haka ina so ki dawo Nigeria gobe domin duba min jikin babyna domin amanace a wajanmu,
Dif ammy tayi sabida hankalin ta idan yayi dubu ya ta shi ,hanka li tashe take CWA Dada, su taho California kawai gobe da Sabrin domin can sai anfi samun kayan aiki masu kyau fin na Nigeria, da haka suka rabu jiki a sanyaye .
Farkawar ta kenan ta fara motsi da hannun tana kokarin ta shi da sauri Dada ta tafi majanta domin taimaka mata domi n ita kanta Dada tasan duk shagwabar babyn ta sometimes idan taga hankalin
Dadan ya ta shi tana dauriya akan ciwo. Kamo t a tayi tana mai shafa bayanta ,shigowar doctor Aqaq ne ya kasar da Dada daga abin da take,Dan bata San ya Fita daga office dinbama sai da ya shigo tasan ya fita,sannu yayiwa Sabrin yana mai bata wasu maguna domin tsagaitawar fever din, bayan tasha ya dauketa ya kaita mota ,Dada ta shigo driver yaja suka tafi gida da zimmar washe gari su daga California.
A cikin Daren madam ta sa doctor Aqaq ya musu komai na tafiyarsu.
*****************"***Bangaren ammy ma damuwa ce ta isheta domin mamakin rashin ganewar da doctor Aqaq yayi akan meke damun Sabrin coz tasan likitane mai shegen kwazo ta ko wanne fanni daban ta fishi nisa a karatu ba zata iyacewa yafita kwazo,saidai itama tayi karatu bana wasa ba Wanda har yakai takai matakin karshe a karatu,Addu'a tayi Allah yasa ba babban Abu ne ke damun diyar ta taba.da wannan tunanu bacci yayi nasarar dauke ta .
Follows, vote and comment plss.
Instagram @zainab Dangyatin
Zeeluv CE.

YOU ARE READING
ZAKI SAN SO NE KO KAUNA?
RomanceThis story is undescribable ,just read and u will tell me d rest of d story. Taku zee Dangyatin.luv u all my f