chapter 40

784 61 4
                                    

KARSHAN WAHALA
By
Safnah aliyu jawabi
🏟️🏟️🏟️🏟️🏟️🏟️🏟️🏟️🏟️🏟️🏟️🏟️🏟️🏟️🏟️🏟️🏟️🏟️🏟️🏟️🏟️🏟️🏟️🏟️🏟️🏟️🏟️🏟️🏟️🏟️🏟️🏟️🏟️🏟️🏟️🏟️🏟️🏟️🏟️🏟️🏟️🏟️🏟️🏟️🏟️🏟️🏟️🏟️🏟️🏟️🏟️🏟️🏟️🏟️🏟️🏟️
Alhamdulillah yau nakai 40 chapter am so grateful to (ALLAH)subbuhanahu wata'ala for keeping me  alive and for giving me the strength. Sannan ina sake Mika  godiya ta agare ku masoya masu bibiyar al'amari na Ina fata zaku cigaba da bibiyar al'amura na nagode nagode.

Bismillahi rahamanin Rahim

Dakin suka nufa cikin sauri ganin ta sukayi azaune, ruwa mom ta mika Mata kadan Tasha ta mikawa suwaiba sauran,ya jiki suka shigayi Mata tana amsawa,ba jimawa ruwan ya kare *NASIR*ne ya cire Mata da murmushi mom ta kalle shi tace,"son yaushe ka zama likita harda cire ruwa?

Sunkuyar da kansa yayi cike da kunya, taimaka Mata suwaiba tayi ta shiga toilet wanka tayi ta fito,tea mom ta hada Mata ta Bata bayan ta gama mom ta cire Mata magunguna ta bata,karba tayi duk da Bata kaunar Koda warin magani, amma babu yanda ta iya Haka ta amsa Dan bazata iya yiwa mom gardama ba.

Bayan Tasha maganin Saida ta Dan kwanta saboda ji take kamar zata amayo dashi,*NASIR*Wanda ko kifta idonsa bayayi akanta  ganin yanayin data shiga yasa yayi saurin shiga dakin sa ya dauko Mata tom tom aikuwa ba musu ta karba ta sha,sai alokacin ta dan samu komai ya daidata.

Ba jimawa barci ya dauke ta sai sannan mom da *NASIR*suka koma dakin su kowa da abinda yake tunani aransa.

🌲🌲🌲🌲🌲🌲🌲🌲🌲🌲

Mai buhun kudi kuwa komai ya tsaya masa dama ance lafiya uwar jiki babu Mai fushe dake.
Yanzu idan kaga Mai buhun kudi idan ba an fada maka cewa shi bane bazaka taba gane Shiba, Dan gabaki daya ya fita haiyacin sa sakamakon gobara data tashi agidan sa cikin dare wacce  haryanzu ba'asan musabbabin taba.

To wannan gobarar itace ta cinye Rabin dukiyar sa Dan dama  bankasan ce daya daga cikin mutane masu  ijiyar kudin su banki ba.

Hakan ce tasa yana ji yana gani dukiyar sa ta kama da wuta shi kansa saida wutar ta kuna shi gabaki daya ta lashe mishi kafa.

Da kyar dai aka samu wutar ta mutu. bayan komai ya lafa haka ya shiga jinyar kafar sa, to dama ga cuta ,haka yayi ta kashewa kafar kudi Amma ina anayi kamar ba'ayi to kowa dai yasa yanda kudi take, sannan ai Zara Bata barin Dami,to hakance ta kasance ga Mai buhun kudi intakace muku harta Kai Mai buhun kudi gida jansa ya rinka sayar wa Yana magani Saida ta kai har gidan da yake ciki ya sayar.

Duniya dai tayi mishi ati shawar tsake yanzu agidan yake kwana kafin ya samu mafaka cikin ikon ALLAH mutanan suka amince daya cigaba da zama har sanda zasu bukaci gidan.

Wata rana Mai buhun kudi Yana zaune yunwa duk tabi ta addabe shi ga wani irin zogi da kafar ke masa yaji an bankado kofar dakin,cikin sauri ya dago Kai wa zaigani basi ce ita da sumaiya duk kansu sanyi da glass afuskar su.

Rufe hancinta basi tayi da sauri Dan wani irin wari taji ya daki hancin ta .
Sumaiya ma ba'abarta abaya ba.kallon kyama suka bishi dashi sannan suka fashe da dariya.

Saida sukayi Mai isarsu sannan sumaiya ta kalle shi a wulakance tace,'mai buhun kudi komai buhun kaxanta, wanne zankira ka da ita daga ciki?

KARSHAN WAHALA 2019Where stories live. Discover now