Maraici Stories

Refine by tag:
maraici
maraici

7 Stories

  • KOMAI DAGA  ALLAH NE!!!( ARZIKI & ILIMI) by Allauma
    Allauma
    • WpView
      Reads 2,336
    • WpPart
      Parts 15
    Rayuwa komai daga Allah ne. Mutum baya cika cikkanken mumini har sai ya yadda da kaddara Mai kyau ko akasinta. Komai ya same ka daga ALLAH NE! Babu Mai baka sai Allah. Sannan babu Mai maka illa sai da sanin Allah. Rayuwa cike take da jarabawa kala kala. Hakuri, rikon gaskiya da amana da tsoron Allah na Kai wa nasara. Yan uwa musani babu Mai mana sai ALLAH. Malami ko Boka bazai amfane ka da komai ba. Mu mika wa Allah lamarinmu Mai komai Mai kowa. Allah shi ya halicci duniya da lahira da abunda suke cikinsu. Mu kiyayi sallolonmu Biyar akan lokaci. Mu lazimci istigfari da salatin annabi. Azumin litinin da Alhamiz Sallar dare Sadaka Karatun Alkur'ani Sun ishe mu. Xamani ya lalace Allah kadai zai iya mana ba malami ko boka ba. Littafin nan zaizo da wata salo na daban. Rayuwa da jarabawar da take ciki. Yadda hakuri da rikon Allah da manzonsa da rikon gaskiya da amana kai kaiwa ga nasara. Illar kazamtacciyar soyayya . Tsaftatacciyar soyyaya da nasaran ta. Ku bini da sannu cikin wannan kirkirarriyar labarin nawa mai cike da abubuwan tausayi da daukan darasin .
  • Rayuwar Deejah by Katakore
    Katakore
    • WpView
      Reads 62
    • WpPart
      Parts 1
    Deejah yarinya fara mai kyau sai dai rayuwarta ta zo mata ba kamar yanda ya kamata ba. Wanda daga baya kuma sai Allah ya kawo mata jin daɗi marar misaltuwa "maraici babbar cuta"
  • Yanayin Rayuwa by FadimaFayau
    FadimaFayau
    • WpView
      Reads 212
    • WpPart
      Parts 8
    Tsananin rayuwa ya sa Kakar ta za ɓar kai ta aikatau wanda ya yi sanidiyar canjawar rayuwar ta baki ɗaya.
  • MEEYRAH  by youngnovelist001
    youngnovelist001
    • WpView
      Reads 59
    • WpPart
      Parts 2
    *HAKURI#* *CIN AMANA#* *YAUDARA#* *MARAICI#* *ZAZZAFAR ƘAUNA#*
  • Najma da Mahir by Fatima_writes_
    Fatima_writes_
    • WpView
      Reads 10,278
    • WpPart
      Parts 18
    "Ga wannan sunanshi 'Dan aike' domin ko in ya je dawowa ya ke, an hadashi ne da majinar damisa mai mura,jelar'beran da bai taba satar daddawa ba,da kuma hakorin muzuru mai kimanin kwana cassa'in, ya yarda ke tun bai san miye yarda ba,a coffee za ki 'diga, 'digo biyu ina jaddadawa!!!, ki bawa Anisa ita zata hada ta kai masa, ba so ba ko zuciyarshi ce a jikanta ba zai aure ta ba, Anisa zai aura,amma duk ranar da Najma ta furta mai da kanta tana son shi ki Kuka da kanki don babu Ruwan Boka Mugu" Ya fada yana zare idonshi da ya sha farin kwalli. *** Gishiri ya ji a bakinshi mai hade da ruwa, lokacin ne ya gane ba ita take bu'katar handkerchief din da ya bata ba shi ke bukata, yaushe rabon da ya yi kuka? Tun ranar da ta yi wani ciwon ciki mai cike da azaba, ya bawa kanshi amsa yana goge majinar da ta samu damar zubo masa, zuciyar sa ce ta kuma tarwatsewa a karo na ba adadi jin kalaman da ke fitowa daga bakinta dukda cewa a wurinshi sun fi kama da aman wuta mai zafi, so yake ya ce mata 'I love you ' kalmomin da tun bata fahimtar magana yake fada mata saidai yau ya kasa,wani abu mai kama da Zuma rock ya danne masa harshensa da zuciyarshi kuma sai bitarsu yake kamar almajiri ya rike allonsa. Dumm zuciyarshi ta buga a karo na uku tun bayan da ta fara magana,bakin shi ya bude wanda ya yi sanadiyyar zubowar yawun da bai san da shi ba a yayinda ya cigaba da kallonta kamar wanda ya ga Tinkiya da'Ture ka ga tsiya' daurin yan mata masu ji da kansu. *** "Haba Yayana 'dan baki!Ya kake so in yi da rayuwata ne?Na san ba Anisa kake so ba ni kake so ba sai ka fada min ba wallahi na sani, amma ka ki ka nemi aurena tun tuni? Mai kake jira? Hmmm, Ya Mir me ya sa ka canza min gaba daya? na yi ta kokarin in jure na kasa saboda zuciyata ba zata iya ba,Nisanta kanka da kake yi da ni 'kara tarwatsa min zuciya yake, Ka yi sake har Abbu ya hada aurena da Ya Jamil,gobe za a daura tunda haka ka zaba you have 24 freaking hours to decide, abinda na sani shi ne I LOVE YOU WALLAHI DA GASKE..."
  • ILLAR MARAICI by Bookaholicnutella
    Bookaholicnutella
    • WpView
      Reads 3,139
    • WpPart
      Parts 22
    Ta kasance sanyin idaniyar iyyayenta. Sanadin farincikinsu, dalillin jin dadinsu kuma 'ya kwalli daya ga attajirai biyu. Yaya rayuwarta zata kasance idan ta rasa dukkansu biyu? Follow the bittersweet emotional rollercoaster life of Jannah. A little girl who believed in unicorns and rainbows oblivious to the dark and frowning aspect of life. Living in oblivion until reality gave her a tight slap. Yar mutan Borno, ©Zahrfatimahh
  • KOWA YA GA ZABUWA... by Gureenjo6763
    Gureenjo6763
    • WpView
      Reads 51,574
    • WpPart
      Parts 47
    Rayuwa wani abu ne da kan zo mana da kalubale iri iri, wani muna iya fin karfinshi da taimakon Allah wani ko sede mu zubawa sarautar Allah idanu zuwa sadda ze kawo mana karshen shi walau Mutuwa walau sakamako na farin ciki. HIDAYAT yarinya me ƙarancin shekaru marainiya gaba da baya, bata da kowa bata san kowa ba, ta taso cikin kangin rayuwar marikiya an aura mata mafi zaluncin miji cikin maza a rashin sani, wadda ya kasance ɗa ga marikiyarta Kaddarar ƴaƴa ta Haɗa ba tare da wannan azzalumin miji yayi maraba da su ba, ya rayuwa zata zame mata? Ta ina zata iya Kula da kanta da kuma yaranta? Cin su shan su, suruturarsu? Anya zata iya tsallake wannan jarabawar kuwa? Anya ba zata gaza a hanya ta fawallawa Allah lamuranta ta zubawa sarautar shi idanu ba? Shin da dangin miji zata ji ko da Shi karan kanshi mijin ko kuwa da baƙar rayuwa da take ciki? Shin zata iya tsira daga wannan taskar na Tsaka mai Wuya? Duk ku biyo ni cikin wannan littafi na KOWA YA GA ZABUWA... Na muku Alkawari ba Zaku taɓa yin nadama ba, Alqalamina a feke yake don Nishad'antar daku, fad'akantar daku da kuma ilmantar daku duk a cikin wannan littafi.. karku bari a baku labari.