chapter 10

1K 83 1
                                    

Gudu yake babu kama hannun yaro harya Isa karamar asibin dake garin,
Bayan anduba ta aka tabbatar masa da guba Tasha,

"Laure kin cuceni yanzu saboda ALLAH yadaya tilo da ALLAH ya azurtani da ita kikeson kashewa?

Wallahi malam maganin bera na sa, bansan lokacin da ta tashe daga barcin ba, ka yarda dani.

Haka dai suka cigaba da jinyar ta hartasamu sauki suka Kuma gida.

Ranar wata asabar da asuba laure taga malam haryanzu baitashi yatafi sallah ba, abin yadaure mata kai.

"Malam asuba fa tayi.

Jin shiru bai'amsaba yasa ta Kuma Kiran sunan shi, "malam malam innahlillahi wa'inna ilaihi raju'un

Kankace jama'a sun cika gida haka dai akayiwa gawar malam jauro sutura, aka sadashi da gidan shi na gaskiya.

Bayan arba'in dangin Maryam suka zo tafiya da SAFNAH.

"yanzun saboda ALLAH tafiya zakuyi da yarinyar Nan,bazaku duba halin da nake ciki. Kubar min it narinka ganin ta amadadin malam ba.

Haka dai badan ransu naso ba, suka hakura suka barwa ,laure da alkawari zata rinka zuwa gurin su duk bayan Kuna biyu.

Haka rayuwa taci gaba da tafiya, gashi yau har malam jauro yakai shakara shida da rasuwa.hakan yayi daidai da shigar SAFNAH shikara goma Sha daya aduniya, babu irin azabar da Bata gani ba gurin laure,

Safnah takasance yarinya Mai natsuwa ,batada hayaniya,asalima idan ka ganta awaje to innar ta laure ce ta aike ta,
Tana da farin jini agun mutane ,mafi yawance suna tausaya mata saboda maraicin daya sameta akarancin shekaru irin nata.
Tana da kawa maimuna

Kawancan safnah da maimuna yasamu asalini kasancewar islamiyar su daya safnah Bata fiya zuwa gidan su maimuna ba Dan bata son yawan yaho.

Laure tana zaune ta rinka Jin sallama, ta amsa tana gani lantana ta tashi da sauri suka rungumi juna, cike da farin cikin sake ganin juna ,Dan tunbayan rasuwar malam bata Kuma zuwa garin ba.

"Ki safnah dibu ruwa yau manyan baki ke garemu.

"Inah kawana.
"Lafiya Lau.
"Laure kardai kicemin safnah CE wannan tayi girma haka.

"Ita ce
Hmmmm lailai girman dan mutum. Ba wuya .

"Lantana gaskiya naji dadin zuwan ki,Kinga wallahi tun bayan rasuwar malam, komai ya tsaya min.
Lantana ta kalli ta cike da mamaki tace" ki yanzu kina da katuwar budurwa haka kike rashin na kashewa?

"To yazanyi.

Kamar ya.yazakiyi ga yara Nan suna talla agari.

"A a Kinga lantana bazan iya sawa yarinyar mutane talla ba gaskiya.

"To saiki tsaya kina kallon ta haka, ke laure inzaki daina damuwa da maganar mutane ki daina Dan ba'aiya musu.

"Gaskiya kam,to koda ma nace zanyi Sana'a in nakeda jari.

"Zanranta miki dubu daya saiku fara Sana'a banyan kwana biyu zanzo na amshi abata.

"Gaskiya babu abinda zance Miki lantana saidai nace nagode da dawainiyar da kike yi dani ALLAH yasaka.

Safnah tana dawowa daga islamiya tace,"sannu da gida Inna.
"Yauwa jiki kicire kayan makaranta ki zoki dauki tallan Nan.

Jin haka Saida kirjin ta yabuga da karfi,Dan tasan idan laure ta aiyana Abu babu makawa saita aikata.

Jiki babu kwari tashiga daki, taciri kayan makarantar, tasaka kayan gida tazo tadauki tiran shinkafa da wake hawaye na zuba.

Hartakai kofar gidan Laure ta kira ta.
"To muguwa bakar munafuka ,wato sukike mutane gari su zagini ko?ace ina azabtar da ke ko ?
To ta ALLAH ba Taki ba,maza ki share hawayan dake wanna. Munmunar fuskan Nan taki, kibace min dagani shashasha.

KARSHAN WAHALA 2019Donde viven las historias. Descúbrelo ahora