Biyu

948 89 23
                                    

Malam Muhyiddeen haifaffen garin zaria ne, Anguwan Alkali. Mahaifin sa malam Jibril ɗa ne  ga Galadiman Zazzau lokacin sarki Jafaru. Bayan rasuwan Galadima a wannan lokacin sai sarautan ta koma hannun kanen mahaifinsu saboda yayansa maza da ke da rai duk yara ne. Sun taso cikin aminci da kaunar juna haka su ke zazzaune a cikin gidan da mahaifin nasu ya rasu ya bari kowa da sashin sa.

Yana kammala firamare ya shiga makarantar Alhudahuda da ke kusa da su. Inganci karatuda kuma kwazo irin na Muhyiddeen ya sanya shi samun sakamakon mai nagarta.

Ko da ya kammala ba shi da burin da ya wuce ya zama malami hakan ya sanya yayansa da ke kula da lamuransa tura shi makarantar horar da malamai anan birnin zaria.

Geography/biology aka bashi, yayi farinciki don a duk biyun babu wanda bai kasance wani mahiru ba a wannan fannin.

Cikin nasara ya fara karatun sa don ko sau ɗaya bai taɓa cin kasa da saba'in bisa ɗari ba, hakan ya sanya aka sanshi tun daga maluma har ɗalibai. 

Ko da su ka isa matakin gwajin iya karantarwa a firamaren kusa da gidansu yayi, nan ma cikin nishaɗi ya ke yi saboda kaunarsa ga karantarwa. 

Yana kammala karatu yayansa ya dama masa aiki a karkashin gwamnatin jiha da ɓangaren ilimi na karamar hukuma ke kula da su.

Makarantar Sarki Sambo da ke bayan  fadar sarki aka tura shi, babu ko ɗar ya isa wajen. Cikin nishaɗi da kwarewa ya ke koyar da ɗalibansa, yana tabbatar da ya koyar da su sun iya kafin ya shiga sabon babi. Yakan tuna da cewa koyarwa hanya biyu ta ke sada mutum walau wuta ko aljanna saboda kasancewar sa sana'a ta zama tsani ga cikan nagartan al'umma.

***

Matsalar farko da ya fara fuskanta shine rashin biyan albashi akan lokaci, sau da yawa sai sun shafe tsawon kwanaki sittin sannan ake ba su, lokacin a teburin akawun karamar hukuma ake biyansu, su kan shafe kwanaki su na kan layi don kawai a biya su hakkinsu. Sannan in aka tashi biya idan matakin aikinka ya kai mataki na bakwai (grade level seven) kamar na shi, albashin mataki na biyar haka nan su ke amsa su yi fatan Ubangiji Allah ya sa masu albarka.

Tun bayan samun aikin sa yan uwansa su ka cire hannun su a kansa, ba a haka su ka tsaya ba sai da aka ɗaura masa siyan maganin mahaifiyar su duk karshen wata, hakan ya sa da kyar albashinsa ke cika wata ɗaya kafin ya kare. 

Sai da ya yi shekara shida a cikon na bakwai yayi tunanin komawa makaranta don samun shedan degiri a fannin ilimin abubuwa masu rai (biology) a jamiar Ahmadu Bello, ko da ya je ma hedimasta ɗinsu da maganar bai Musa ba don mutumin kirki ne sai ya sanya shi rubuta takardar neman izinin karo ilimi (study leave). 

Hedimasta ya sanya hannu ya tura shi ga sakataren ilimi na karamar hukuma, ko da muhyideen ya isa ofishin, mai tsaron baki na ofishin sai da ya bukaci ɗari biyar kafin ya masa iso ga ES. 

"MaashaAllahu abu ysyi kyau, ilimi na da matukar mahimmanci saboda haka ba zan taɓa bari ka salwanta ba, zaka koma makaranta amma duk wata ina da kashi ɗaya bisa ukun albashin ka" ES ya fadi hakan ya sanya muhyideen saurin ɗago kai. 

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Jul 30, 2019 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

TSANINMUWhere stories live. Discover now