Hayaniyar yara ne ta ko wane lungu da saƙon makarantar gwamnati da aka fi sani da sarki Musa LEA primary school da ke madarkaci a birnin zaria.
"Malam sai da safe!" "Malama till tomorrow!" "Malam! Malama!!" shine abin da ke fita daga bakin ɗaliban a duk lokacin da su ka wuce malamansu.
"Malam Muhu! Malam!! Malam Muhu!!" shi ke fita daga bakin ɗaliban kama daga yan aji ɗaya har yan aji shida don shekaransa takwas yana malamin Aji ɗaya.
"Sai da safenku! Ku gaida gida!! Bye bye!! Shine amsarsa garesu. Zuciyarsa kan yi wasai ya nemi duk wani ɓacin rai na duniya ya rasa a lokuttan hakan ke faruwa. Murmushin da ke kwance a fuskarsa bai gushe ba har ya karasa inda mashin ɗinsa ke ajiye. Kakkaɓewa yayi kamar kullum sannan ya tayar ya hau don tafiya.
Tafiya yayi na mintoci biyar zuwa bakwai kafin ya isa gidan su da ke unguwar Alkali duk a cikin zaria.
Gida ne babba mai zaure biyu kafin a shiga cikin gidan, Sasa-Sasa ne inda kanne da yayin babansa duk ke ciki. A wani gefe kuma shi da yayyinsa har ma kanensa su ma da na su sashin. Sanannen gida ne don suna da yawa sannan gida ne mai cike da nagarta.
Da sallama ya shiga sashinsa, matarsa Karima na zaune, tun bayan sallamansa da ta amsa ba ta ce da shi komi ba. Bai yi mamaki ba don yana sane da yanda su ka rabu.
"Habibiyata! Har yanzu fushin ne" yace yana mai zama a gefen ta. Banza ta yi da shi ba tare da ta amsa masa ba.
"Kinga ba wai na ki yi miki anko bane, na ce ki amsa, in dai ta yarda zan yi biya biyu" ya fadi duk da ya san ba abin da ta fi tsana sama da biya biyun nan.
"Ban gane biya biyu ba! Tun safe ka ke karanta min biya biyu na haddace su a sake wani babin" tace cikin ɓacin rai.
"Toh ya kike so karima, ko za ki hakura da ankon ne ki yi amfani da kayan sallan ki na bara ne" ya sake faɗi cikin tausasa harshe. So yake ta fahimce shi, so yake ta kalli abubuwa ta fuskar da ya ke kallo.
"Don duk gidan nan mun fi kowa kaskanci ko, ni dai ka nemo dubu takwas mu amshi ankonmu ni da su khairat. Sannan ga kuɗin makarantar islamiyya za a fara kora, ka nemo har na hadda don kwanan nan za su fara maganar a biya. Kalanzir ya kare ka ga damina ake, hura icce ba abu ne mai sauki ba" tun yana fahimtar abin da ta ke faɗi har ya dena fahimta. Ita kwatakwata ba ta gane lamura ne, yanzu ya tashi daga dubu huɗu na atamfa ɗaya takwas ta ke nema.
"Ni fa in bara za ka je ka yi ba abin da ya shafe ni" ya tsunkayo ta cikin tunanin sa.
"Ki yi hakuri, kin san dai ni malamin makaranta ne, ba wani karfi ne da ni ba. Ki kara hakuri, ki kara akan na da, mu cigaba da addu'a kila gwamnatin nan su cika alkawari su inganta rayuwar malamai. Ki yi hakuri don Allah" ya ce kamar zai mata kuka, kwarai zuciyarta ta karaya, ta san yana kokarin yi amma kuma da kunya a yi bikin jikar farko a gidan sannan ba ta yi anko ba.
"Amma ka ga yaushe yaushe Khalid ya samu aiki Napri amma ya haɗe yara ya musu anko, kai tun kan aurenmu ka ke aiki fa" tace tana harararshi.
"Ki yi hakuri Karima, ni ɗin malamin makaranta ne, ki fahimce ni kwatakwata albashin guda nawa ne" ya sake faɗi yana mai tausasa kalamansa don ya fara ƙuluwa. Daidai da ruwan sha ba ta tareshi da shi ba, sai wasu abubuwa da ta san kwance masa lissafi.
Dafe kansa yayi, tunanin mafita ya ke yi, albashinsa kwatakwata dubu talatin da huɗu ne, ciki ya ke ciyar da iyalinsa, ya biya kudin makarantar yaransa, lafiyan su, da duk wani hidima na sa duk yana cikin dubu talatin da hudun nan. Tashi yayi ya bar wajen don ba zai iya sauraren ta ba.
Gunguni ta fara ganin ya nuna bai da muradin sauraren ta. Ta ji haushi ainun kalaman mahaifiyar ta su ka dinga tariyowa a kwakwalwanta
"Karima ki rasa mijin aure sai malamin makaranta? Malami fa, Alli zai ciyar da ku ko zai biya muku bukatar da kuɗi zai biya? Tsaya ki ji, babu talaka sama da malami kuma ba za ayi ba"
ČTEŠ
TSANINMU
PovídkyDuk abin da mutum zai zama a duniya sai ya bi ta wasu matakala wanda ke manne a jikin tsani, tsanin kan iya zama na katako wanda ruwa da rana ke saurin lalatasu wani tsanin kuma na karfe ne da sai dai yayi Tsa-tsa. Ana samun tsani na azurfa ko lu'ul...