[29/11 10:21 PM] Aishat Muhammad: [29/11 8:45 PM] Aishat Muhammad: 🍒🍒🍒KHALEESAT 🍒🍒🍒
🍒🍒 31 🍒🍒
🍒 🍒
Sojoji kusan su biyar naga sunzo daukanshi, shiga cikin mota yayi already wata motan ambulance tazo akadau khaleesat aka saciki, wani babban asibiti ya kaita a abuja mai suna AMAZING GRACE HOSPITAL private asibiti ne, likitocin wurin turawa ne nan aka kwantar da khaleesat saida yagama komi sanan ya ajiye wani soja ya dinga gadinta shikuma ya koma ya shiga mota yatafi headquarter dinsu inda ake nemanshi.HYDAR yadawo ba uhm ba uhuhm, baya fita ko ina, lesson dinma yadena zuwa, hunting ma yadena zuwa, bayama kowa magana, abin duniya yay ma ummi yawa ga hydar ga zulaihat duka sun dawo marasa lpy. Ita kanta karfin hali take dan yanzu tagane khaleesat tazama jininsu, bata a gidan yanzu gidan yadena dadi, gidan yadawo fanko.
FAISOL tunda yakoma gida yake rashin lpy, mai martaba hankalinshi yatashi yaga yatsan danshi a gutsure, yay tambayan duniya amma faisol ba bakin amsawa saboda yanda bakinshi ya kumbura ciwo ya cakashi.Yau kimanin sati daya kenan da tafiyar khaleesat, yaune kuma za'a fara waec. Ummi ta debo ruwa takaima hydar bayi ta dawo dakinshi ta xauna kusa dashi tace "hydar" yadago kai ya kalleta tace yaune zakufara waec katashi kayi wanka katafi, girgiza kai yayima ummi batare dayace komiba.
Ummi itama idonta ya cika da kwalla, tace hydar kayakuri kaje kayi jarabawan khaleesat zata dawo wata rana insha Allah kaji. kulle idonshi yayi batare dayace komiba. ummi tagama magana da wa'azin tafita hydar na zaune, alwala tayi tafara sallan nafila tana rokon Allah yadawo da hankalin danta jikinshi.
Hydar na zaune dakinshi yay shiru idonshi a lumshe babu abunda yake gani sai fuskar khaleesat, tuna ranan data taba cemai inaso kazama soja abun yatuna yamike ahankali yace khaleesat inhar burinki ne nazama sojaa koda baki tare dani, koda shine abu na karshe dazanyi aduniyanan saina zama sojaa kallon agogo yayi yaga saura 30min afara paper da sauri ya shiga wanka.
Yana fitowa yasa kaya yay kyau kaman bashiba, ya shigo dakin ummi yana murmushi yace ummi natafi, mamaki kaman zai kasheta tace to hydar Allah yabada sa'a bazakaci abinciba?? Yace zanyi lattine saina dawo zanci,har zaure tarakashi sanan ya tafi.
Maman Abd shakur 😘
[29/11 10:20 PM] Aishat Muhammad: 🍒🍒🍒KHALEESAT 🍒🍒🍒
🍒🍒 32 🍒🍒
ABUJA
Har yau babu wani improvement a khaleesat, likitoci kullum suna kanta amma ba'a samun cigaba ko kadan, kullum sojanan yana zuwa dubata dan har matarshi mai suna Farida da dansu marwan yakawo sun ganta, farida ta tausayama khaleesat sosai dan har kuka saida tayi.NIJAR
Alhamdulillah hydar ya kammala waec da jamb dinshi a tsawon wata biyu, result yafito yaci da kyau yay applying NDA shima sunanshi yafito dan yaune ma zaitafi Nigeria, zaije chan kaduna makarantan Nigeria defense academy ( NDA ).
Da sassafe ya shirya ya shigo dakin ummi sai murmushi yake dan gani yake dazaran yaje Nigeria zaiga khaleesat, haka yakeji a ranshi zaiga khaleesat, ummi tace hydar ka shirya? yace eh ummi, tace hydar maisa kazabi Nigeria?? Akwai makarantan sojoji na nijar maisa bazakaje wurinba kaga kana kusadamu, yace ummi zan nemo matana a Nigeria ne. tace to abu daya zan fadama shine kariki gaskiya, amana, da takwa, karka zamo mai ha'inci, kakuma dunga taimakom duk musulmin dayake bukatan taimakonka, inhar karike wanan dabi'an hydar tsawon 2 years dinan dazakayi wlh saika zama babban sojaan da akwai sojoji dasukai shekaru goma basu sami mukamin ba.
Dana nahoreka dajin tsoron Allah, ka kiyaye sallolinka biyar, ka nisanci sabon Allah ka kula da kanka kuma. ya rungume ummi, ummi ta fashe da kuka hydar ya share mata hawaye yace ummi nai miki alkawari zanyi amfani da duka abunda kikace sanan ya saketa.Kallon zulaihat yayi wanda ta rakube a gefe tana matsar kwalla murmushi yayi yabude mata hannayenshi, da gudu tazo ta rungumeshi itama tafashe da kuka da kyar ya lallasheta, kallonshi tayi tace yaya hydar plz inzaka dawo ka dawo min da kawata kaji? yay murmushi yace i promise, daganan tadau ghana masgo dinshi suka rakoshi har zaure.