Labarine me fadakarwa wa'azantarwa ga tarin tausayi da hakuri tsantsa

3K 117 5
                                    

☄HAKURI HASKENE☄

                  NA

FAREEDA ABDULLAHI

        (Feedyn Bash)

*بسم الله الرحمن الر حيم*
____________________________________

*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
_________________________________

     *1/1/2020*

~*DA SUNAN ALLAH ME RAHMA ME JIN KAI. GODIYA TA TABBATA GA ALLAH UBANGIJIN TALIKAI, INA GODIYA GA ALLAH DAYA BANI DAMA NA FARA WANNAN BOOK DIN.YADDA NA FARA DA BISSIMALLAH, ALLAH UBANGIJI YASA NA GAMA DA ALHAMDULILLAH, YADDA NA FARA LAFIYA, ALLAH YASA NA KARE SHI LAFIYA. ALLAH YASA MU AMFANA DA DARASIN DAKE CIKI, KUSKUREN DA KE CIKI ALLAH YA YAFE MANA, INA GODIYA GA MASOYANA A DUK INDA KUKE, ALLAH YABAR KAUNA.*~

_*WANNAN BOOK DIN SADAUKAR WANE GA MAMANA TA KAINA BAYA GOYA MARAYU HAJIYA BINTA (MAMA JINJIN) ALLAH YA KARA LAFIYA DA TSAWON KWANA ALLAH MY FANS KUSATA A ADDU'ARKU*_

_*GAJERAN LABARI ME CIKE DA FADAKARWA, DA ILIMANTARWA, DA WA'AZANTARWA,DA  TAUSAYAWA*_

*BANYI SHI DAN CIN ZARAFIN WANI KO WATA BA. BAN YARDA WANI KO WATA YA SAI DA MUN DA NOVEL BA, BANYI DAN NA SEDA BA BANGA DALILIN DA ZA'A SIYYAR MUN BA.*

           PAGE 1-5

A tsaye take a gefen titi rana ta dake ta, banda wari ba abunda take,gefe guda ga yayanta nan akwance, kowa yazo wuce wa kyankyamin su yake yi, ga yara kana na a tare da ita, danger ce ta bada hannu,motoci suka tsaitsaya,duk wajen motar da taje sai su kore ta, wasu ma su zuge glass din koda ko a sauke yake, taje jikin wata mota da gudu har tana faduwa, amma ta mike ta kade jikin ta ta karasa jikin motar, da hausar ta bata fita sosai.
"Ka temaka mun dan Allah katemake ni, ka bani abunda zamuci nida yayana" wani mugun kallo yai mata, matashin saurayi ne ya watso mata yawo a fuska, matsa ki bani wuri kazaman banza bararoji kawai, sadakar yalla kawai kun baro kasar ku kunzo kun dame mu da a kasa mtsww," dai dai lokacin da aka Basu hannu ya figi motarsa.

Kadan ya rage ya take ta, ta saki marayan kuka ta koma kan yayan ta, da gudu ta kara rungume su, ga yarinyar macen babbar kwance sharban, itace me dan girman ba lafiya, ga wata macen da namiji karami, gashi ta rasa yaza tai dasu, kuka kawai suke dukan su basu da girman da zasu jure yunwa. Koga babba ya ya kare bare yaro, ta rasa ina zata sa kanta, kawai itama ta rushe da kuka. Cike da karfin hali babbar tace "adda kiyi hakuri zamu samu mafita insha Allah, komai na Allah ne, Alaife ce ta karaso wajen maman itama, ita ke bin Sheri,  adda yunwa zan mutu, kuka tasa ta rungume su, ta jawo Karamin ta rungume shi shi bama ya magana.

Suna wannan halin wata jibgegiyar Jeep tai parking dai dai su, daga mota ya kare musu kallo wow very nice, burina ya cika lallai dawa zatai nama, wannan dabge haka ga alamu ba wani tare dasu, ya daga waya ya kira wata number, "hello oga wallahi wasu buzaye nagani irin yan Nijar din nan, amma a wahale suke idan suka ji kiwo ba karamin kudi zamu karba dasu ba, dan iri ne me masu daraja" daga chan bangaren aka sheke da dariya, "shiyasa bana jinka na gida na, indai kaya ne masu kyau da inganci kasan su, maza maza ka tahon dasu" yai murmushi angama oga ya kashe wayar ya fito.

Cike da tausayawa a fuskar sa ya kara sa wajen su, "hajiya lafiya  nagan ku anan a gefen hanya", cike da kuka adda tace "almajirai ne mu sadaka muke nema, diyata bata da lafiya karta mutu ka temake ni" yai murmushi a ransa murmushin mugunta a zuciyarsa, cike da tausayawa a fuska, hajiya bakusan cewa kama mabarata ake a kano ba? suka kara fashewa da kuka, ya kalleta ya hadiye yawu, gaba daya yarinyar da aka kira Sheri ta tafi da imaninsa, "yi shirun ki insha Allah yanzu zan temake ku, idan kunyar da zan kai ta asibiti, daga nan ku bini gidan mu wajen mamata, zaku samu masauki me kyau. Wat yarinya ce ta karaso da gudu tana haki, ta fada jikin uwar adda ga wannan kuci wata busashshiyar gurasa ce rabi, nan uwar ta karbe ta gutsutstsura musu.

HAKURI HASKENEWhere stories live. Discover now