FEEDYN BASH RAMADAN KITCHEN DAY 1

378 15 4
                                    


*FEEDYN BASH REALLY FANS RAMADAN KITCHEN*

               *DAY 1*

Fish fantasia

Abubuwan bukata
Kifi
Fulawa
Veniger
Lemon tsami
Tafarnuwa
Mai
Maggi
Gishiri

Zaki samu kifinki ki wanke shi da lemon tsami sannan ki tafasa ki cire kan da kayar, sai ki farfashi a kwani ki matsa masa lemon tsami da dakakkiyar tafarnuwa ki rufe ki ajiye kamar awa daya, sai ki dakko ki barbada fulawa dasu maggi da gishiri da kori sai ki cakudasu, sai ki shafa mai a abun gashi ki din ga diban wannan hadin kina zubawa kina dandabewa sai ki sa a oven karyai brown sosai.


*SOYAYYEN DANKALI DA NAMA*

Abubuwan bukata
Dankalin turawa
Nama
Kori
Maggi
Albasa wadatacciya
Attaruhu
Mangyada

Zaki fere dankalinki sai ki dora a wuta ki dafa shi, idan ya dahu sai ki kwashe sannan ki jajjaga attaruhu da albasa, sai ki dafa nama yayi luguf sai ki juye kayan miyan da kika jajjaga a kai ki dake su suka, sai ku zuba dankalin a kai shima ki daddaka ki gaurayesu guri daya, sai ki kwashe kidinga dunkulawa kina tsomawa a ruwan kwai idan ya soyu yai brown a kwashe.

*EGG FRIED RICE*

Shinkafa g4
Kwai 5
Hanta/koda
Green beans
Green pepper
Peace
Cabbage
Carrot
Curry
Thyme
Sinamon
Man kuli
Attaruhu
Albasa

Ki tafasa shinkafarki karta dahu sai ki race, sai ki yayyanka cabbage,carrot,green beans,green pepper, da albasa sai ki wankesu tas, sai ki soya peace din ki sannan ki juye ragowar kayan hadin da kika yayyanka ki soya su sama-sama, sai ki ajiye a gefe sai ki dora tukunya ki zuba albasa kadan mankuli kadan, sai ki kawo kwanki ki fasa a ciki kita juyawa zaki ga ya dunkule saboda ba kada shi zaki ba, sai ki kawo wannan kayan hadin naki ki zuba a kai, dama kin tafasa hantar ki ko koda sai ki zuba a kai ki hada da shinkafar ki din ga juyawa a hankali har ko ina ya samu kayan hadin sai ki bar shi ya turara sai ci.

In ba'ai sa'a ba sai kin kamo mai house dan dadi musamman da daddadan lemonki a gefe mai sanyi.

Aci dadi lafiya Happy first day of ramadan.

       *ADMIN FEEDYN BASH*

HAKURI HASKENEWhere stories live. Discover now