80-85

595 47 11
                                    

HAKURI HASKENE☄

                  NA

FAREEDA ABDULLAHI

        (Feedyn Bash)

_*Facebook_Farida Abdullahi*_

_*Wattpad @Feedyn Bash*_

_*Instagram Feedyn bash*_

_*Snapchat Feedyn Bash 6660*_

_*Email faridaabdullahiibrahim6660@gmail.com*_

*بسم الله الرحمن الر حيم*
____________________________________

*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
___________________


Bissmillahirrahmanir rahim

                   80-85

Kallon ta kawai ya ke ya na tsananin tausaya mata ,tare da tsantsar soyayyar ta a ransa, ina jinki Fateema ta gyara zama hankalin kowa yayo kan ta musamman masu san jin kwaf.

Asalin suna na Fateema yar mahaukaciya ake kira na ,wasu bayin Allah ne su ka  rada mun suna Fateema, wanda su suka dauki nauyi na da rayuwa ta gaba daya a wannan lokacin!.

Sun ban labarin kawai mahaifiyata ta na yawan zama a bolar bayan gidansu ta na tsince tsince ance, ba ta duka bata komai sai dai surutai, ba ta umm bata umm umm sai dai kallo, idan taga zaka takura mata za ta sanja waje bayan ka ta fi ta dawo gurin ta ci gaba da yin tsince tsincenta.

Watan ta uku da fara zama a wannan bolar aka lura da bullowar ciki daga gareta .

Abun ya daga hankalin mutanen unguwa sosai da sosai, sai aka fara zargin Alhaji Habibu da yiwa mahaifiyata fyade.

Saboda ya na yawan zuwa ya bata abinci musamman da ya fuskanci ciki ne da ita. yana ajiye mata kuma ta na dauka sosai cikin ke girma wanda mutane suka fara zuga matarsa mama nafi akan shi yai mata cikin.

Mama Nafi mace me yakana da fahimta da tsananin tsoron Allah, ganin haka ta sa aka dakko mahaifiyata ta dawo da ita gidan ta, lokacin cikin ta ya yi nauyi sosai .

Mijinta ya dawo yai mamaki dan hankalinsa ba karamin tashi yai ba da ya duba inda ta ke bata nan.

Yaji dadi kuma yai hamdala ga Allah ya sawa matarsa albarka sosai da wannan abun alkhairin da tayi, da yadda ta fahimce shi bayan wata biyu mahaifiyata ta haifeni tasha bakar wahala tun daga lokacin kulawata ta koma karkashin Mama Nafi.

Mahaifiyata wadda har yau ban san sunan ta ba, ta na masifar sona duk da tana halin hauka tun da ta haihu ta warware sai ta dauke ni ta gudu zuwa wannan bolar.

Ganin haka hankalin su ya tashi da kyar suke karbata su ganni sai sun mata dabara fafur ta ki zaman gida kullum magani suke amma abun shiru .

Bayan na kai shekara goma a lokacin tuni Alhaji Habibu ya sewa Umma wannan bolar an gina mata daki guda kuma tana zamanta a ciki, ga makeken tsakar gida haka za ta hada bolar ta tai ta wasa, niko idan taga na fara kuka za ta fara kukan itama tai ta rungumeni.

Ganin haka sai nadena yawan kuka a  gabanta, A lokacin Alhaji Habibu ya sani a makarantar boko da ta islamiyya.

Alhamdulillah ina da tsananin kokari ,hakan ya ja mun farin jini wajen malaman mu sabanin yan ajin da suke kirana yar mahaukaciya" ba na wasa da kowa banda kawa ba na kula kowa haka rayuwata ta kasance.

HAKURI HASKENEWhere stories live. Discover now