4

288 15 1
                                    

💕          ❤      💕
     💕            💕
           💕 💕
              💕
         *KAICON SO...!*
               💕
          💕 💕
     💕          💕
💕       ❤      💕

    ŇѦ

        *ɧAFىAT  ɧAFŊAŊ*
        watpadd @ Xclusive__hafnancy

    *ɖҽɖɩcatҽɖ tɷ:ɧaųwa •ى• ʑAɾƖA (MAMAŊ ŲىWAŊ)*

*ƖŊTҼɭɭƖƓҼŊT  WɾƖTҼɾى  ASSɷ📚✍*

      _•watsup! hafnan's freaking fan's?hope kuna lfy?i juz want to thank you all for ur wonderful comments,haqiqa kuna sani farin ciki,Asmarku tana gaidaku😜°_

       *🅿4*

____________📖Bikin wata course mate d'insu Asma ne ya taso kuma qawartace sosae,kusan xan iya cewa iya shegensu yazo daya,sunanta Saudat,su uku suke yawo amakaranta,da ita Saudat din,sae wata wacce ake k'ira da Zeezee sannan ita uwar gayyar wato Asma.

Ita kuwa baiwar Allah Jaleelah qawar unguwa ce kurum don ko amakaranta  bata binsu sbd kwata-kwata qawayen Asmar basu mata ba,gashi basa son gsky ko kadan,idan ta soma musu wa'azi tofa balbaleta suke da fad'a sai kaga tayi shiru,toh shiyasa basa shiri,kai hatta da ita kanta Asmar ma ba cika shiri suke ba don kunsan ance idan mutum na gaya maka gsky kullum tofa watarana sai kaga ya zamo maka mak'iyi tunda gskyr ce dai baka sonta (Allah dai ya k'yauta).

Toh hakan take ga Asma,ta rage yayin Jaleelah kamar da sbd gskyr da take yawan fad'a mata musamman yadda take maltreating din Yaseer,sosae abin ke soya ranta amma kuwa yata iya?Asma tafi fifita su Zeezee akan Jaleelah.Yo! toh ba dole ba?abokanan cin mushe wa'enda ke dorata akan hanyar da xata cimma burinta ai kuwa ya zama dole ta fifitasu akan uban kowa.

Bikin Saudat wata d'aya ya rage cur! tun da aka saka rana su Asma aka kasa tsaye haka kuma aka kasa zaune,su alan dole sai sunyi bikin kece raini,party kala-kala har wajen biyar xasuyi kuma kowanne da tsadadden anko,biki ne sukeson su shirya irin bikin daya amsa sunansa biki na manyan mata,balle ma ita da Zeezee sune manyan qawaye kunga kuwa dolene suyiwa sauran friends din nasu fintikau ah haduwa.

Yau ma fita xasuyi ita da Zeezee xuwa kasuwa don yin siyayyar anko biyun daya sauran musu,Asma tana da wani sugar daddy mai suna Alh.mansur,shine ke biya mata buqatun komai amma harwa yau yaki samun abnda yakeso atare da ita,don ita Asma ba irin matan nan bane masu siyar da mutuncinsu donsu samu abin dunia ba,a'ah ita ta siyasa xata ci kudinka har tabar yayinka ba tare daka samu abnda kakeso atare da ita ba.

Manemanta ahalin yanxu su uku ne,Alh.Mansur,Amjad sai kuma Yaseer,kuma duk Yaseer yasan tana da wasu samarin don wasu lokutan ma har agabansa take waya dasu amma bey isa yace komae ba,idan kuwa har ya kuskura yace xaiyi magana toh sai ta nemi ta hau kansa ta xauna,zagi kuwa bbu wanda bazai sha ba aranan,hadda su gorin ido,kai Asma! wallahi haka dai d'an talikin nan yake haquri da ita wai don yana masifar qaunarta.

Kudi har dubu dari Alh.Mansur ya turawa Asma ah acct. na shagalin biki,duk da hakan tana ganin kudad'en bazasu isheta ba gashi kuma batason ta sake rok'onsa wani kudin don bey wani dad'e da siya mata laptop ba,ta rasa yadda xatayi don haka sai kawai ta dauki wayarta ta latso ta hannun dama Zeezee,

  Bugu daya ana biyu ta daga tana fadin''Babyn d'an makaho ya akayi ne?kin fito ne?

Cike da jin haushin sunan data ambato agareta tace''A'ah Zeezee zaki soma ko?wai ni sau nawa xance miki ne ki dena kirana da wannan sunan bana so?pls bury dat name immediately banaso.....''

Ganin tayi fushi yasa Saudat fadin''Ai fa sai kiyi donni ko kasheni zakiyi baxan ta6a dena kiranki da babyn d'an makaho ba,ni dallah malama ki gayan kin fito ne ko kuwa yaya?

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Nov 06, 2019 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

KAICON SOWhere stories live. Discover now