17

115 4 0
                                    

💕          ❤      💕
     💕            💕
           💕 💕
              💕
         *KAICON SO...!*
               💕
          💕 💕
     💕          💕
💕       ❤      💕

    ŇѦ

        *ɧAFىAT  ɧAFŊAŊ*
        watpadd @ Xclusive__hafnancy

    *ɖҽɖɩcatҽɖ tɷ:ɧaųwa •ى• ʑAɾƖA (MAMAŊ ŲىWAŊ)*

*ƖŊTҼɭɭƖƓҼŊT  WɾƖTҼɾى  ASSɷ📚✍*

   *🅿---17*  

       •gαιѕυωαя вαη gιямα gα 'уαη кυηgιуαтα,ιηα αℓfαнαяι ∂αкυ ѕσѕαι,∂ση нαкα уαυ ραgє ∂ιη ηα мυѕαммαη ηαкυ ηє°

_*•Boss madam Maryam mom Afra*_
_*°Meenah Abba*_
_*•Sainah Ummun Meenal*_
_*°Sis Nerja'art (Mommanah)*_
_*•Jameela Janaf (Sahiba)*_
_*°Beebah Moh'd (My beebi)*_
_*•Maman Kausar tawar*_
_*°Sis Khaleemerh (my leemah)*_
_*•Mummy Fadyl*_
_*°Mummy Zill*_
_*•Sis Mugirat*_
_*°Real mom Afra*_
_*•Aufana Ukhti*_
_*°Ummu Abideen (Nameskirt😜)*_
_*•Real mom Afra*_
_*°My Sidiya*_
_*•Chubad'o Moh'd (Granmama)*_
_*°Sis Aysha*_
_*•Ummun Meenal*_
_*°Fatima Sani*_

  _*Duk na gaisheku k'yauta👍,readers kuyi haquri zaku ce na cika maku page da hayaniya😀,ya zama dole ne na mika gaisuwata ga gwanaye na,page dinku ne agaba don haka zan zak'ulo masu comments na mika gaisuwata agaresu,Asha karatu lfy don yau Dramar daban take📖*_

__________________________________

  ''Ke Shalele meye haka?tashi man! nace kiyi shiru naji zan miki duk abinda kikeso…''

Sake bud'e wani shafin kukan tayi tare da cuno karamin bakinta gaba tace''Abbu wallahi wayau zaka mun,so kke kawai nayi shiru amma ni nasan tabbas se kayi na'am da shawarar Umma...'' ta cigaba da kukan wiwi sanin da tayi na cewa ko kadan Mahaifin nata baya son ganin kukanta arayuwarsa,

    ''Ya salam!'' ya furta tare da shafa kansa da hannu don duk ta birkitasa kuma ya rasa abunda ze mata ko ya gaya mata har tayi shiru,can yace''Tou ai ga umman taki nan ta dawo nasan zatayi maganinki yanzun nan kuwa...''

Ai be ida rufe baki ba sai gani yay tayi tsit kamar tsayawar ruwa tare da mik'ewa tsaye ta hau en kame-kame ''Ammm Abbuu nace ba..?''

     Idonta k'yam akan k'ofa tana jiran shigowar Umman amma shiru kake ji,hakan ne yasa ta nufi k'ofa cikin sanda tare da lab'ewa,ahankali ta dage labulen tana lek'e,bata hango kowa atsakar gdn ba,sannan k'ofofin dakinsu Umman dukah ah rufe yake,hasalima ma bbu alamun da ze nuna cewa akwai wanda ya shigo gdn,hakan na nufin k'arya Abbu yay mata kenan ko?don yaga tana tsananin tsoron Umman tata?tou shikenan ai in yasan wata ai besan wata ba...

Ta ayyana hakan aranta tare da gyad'a kanta alamun gamsuwa da shawarar xuciyarta,juyowa tayi ta zubawa Abbu ido dake faman tikar dariyarta,

   Dafe k'irjinta tayi tare da k'arya gwiwowinta xuwa kasa,cikin seriousness d'in da ban ta6a ganinta aciki ba tace''Wallahi Abbu da gaske nake karka bi shawarar Umma ka aura mun wanda bani so in ba haka ba kuwa kuna iya rasani,yau zan gaya maka gaskiyar ko wacece 'yar da kuka haifa?da kuma burikanta arayuwa!

Jan gwauron numfashi tayi kan ta cigaba''Abbu 'yarka ba er iska bace kamar yadda mutane da yawa suke mata kallon hakan,bbu wani d'a namijin da zaizo yace maka wai shi ya ta6a ganin kalar pant d'in Asminka,wannan k'arya ne,ba yabon kai ba amma ni nasan ina da kamun kai in har akan mutuncin kaina ne,wulaqanci kuwa da ake cewa ina dashi,ka ganni nan wlh bbu ruwana da kowa sai in har mutum ya shiga gonata ne da gangan ya kuma nemi daya kawo mun raini ko iskanci,tou shine nake karta masa rashin mutunci son raina,Abbu kowa nada burika da yawa arayuwa,bbu wanda zaiso ace ya dawwama acikin talauci sai in Allah ne yaso hakan,kowa na mafarkin ya ganshi cikin jindadi,yaci meh k'yau,yasaka meh k'yau,ya shiga meh k'yau,kai komi ma meh k'yau,tou meh zaisa mutane su dunga mun kallon makwadaiciya da kuma tirr dani don kawai nima ina da wannan  burin ta auran mai daula?wata ma har habaici tamun wai _*''Idan dambu yai yawa baya jin mai!garin kwaɗayin na bayan ludayi sai na cikinta ya zub'e''*_

KAICON SOWhere stories live. Discover now