🌹 *NI* *DA* *MALAMA* *TA*🌹
*By*
*fatima* *Batula**Dedicated*
*to* *my* *shadow*Wattpad@Fatimaumarmoddibo.
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*
*~We are bearer's of so golden pen🖊~*
*~we write assidiously perceive no pain~.*
*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*
*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*
*Sorry* *page* *ɗin* *jiya*
1⃣5⃣to1⃣6⃣ ne mistake nayi gurin rubutawa.Idan ina son na baku page sai naji kunya dan kun wace matsayin page a guri na.ƴan uwana ƴan *GOLDEN* *PEN* *WRITER'S* *ASSO*.
Allah yabar mu tare ya ƙara ma kungiyar mu ɗaukaka ya ƙara mana basira.
Yau page ɗin naki ne momi kiyi gunduwa-gunduwa da shi.
page1⃣7⃣to 1⃣8⃣.
Sabreen bata daina dariyar ba har saida ta gaji ,ta tsaya dan kanta, ta juyo ta kalleshi ya ɗaure fuska kamar me shirin yin kuka,sai ya ƙara bata dariya ta ƙara fashewa da dariya.
Ya ƙasa tashi ya fita kuma ya ƙasa mata magana kallon ta kawai yake yi,yana murmushi wanda bai san dalilin yin shi ba.
Bayan ta gaji da dariyar ta matso da litattafan gaban shi har ya ɗauka ya buɗe aka kira wayar shi yana ganin kiran na waye yai wani irin murmushi.
Kallon shi Sabreen tayi a zuciyarta ta ce "Ikon allah waye kuma da ake mishi irin wanan murmushin"
Duk yadda Sabreen ta so jin abinda yake faɗi ta ƙasa dan yadda yake maganar ko maciji ba zai ji ba.
Sun daɗe suna wayar har sabreen ta fara gajiya sai wurga mishi harara ta gefen ido take yi.
guntun tsaki taja ta tashi ta haye sama.
Bayan ya gama wayar ya ga ba Sabreen a gurin yamutsa fuskar yayi ya tashi ya wuce abinshi.
~~~~~~~~~~~~~
Yau ma ƙarfe ukku da rabi da dawo daga makaranta,kamar yadda suka saba zama a falo kafin a kira sallah yau ma hakan ne,kiran sallah shi ya tashi su kuwa ya wuce ɗakin shi dan gabatar da ibada.
Bata yi sunanin Ya Naufal zai xo ba,cikin ƙananan kaya da sauko kasa kanta ba ɗan kwalli ,lokacin hajiya ma bata fito ba.
Cikin salo da ƙarya murya yayi sallama ,kasancewar tibin a kashe yake yasa taji sallamar,amsawa tayi ba tare da ta juyo ba.
A yatsine ya shigo ya zamu kujera ya zauna,yana zama kiran Haulat ya shigo.
"Hello ita ta fara faɗa.
"Hi my dear ya kike?
"Lafiya qalau ya su momy,gaskiya yau ina son ganin da wuri jiya kawai amma ji nake kamar na shekara ban ganka ba,kasan irin damuwar da nake shiga kuwa idan ban ganka ba,plsss ka zo kar zuciyata ta fashe"
Murmushi kawai yake,ita ke kira kuma ta fishi yin magana.
"Ok to zan zo karki damu"
Duk wanan maganar da suke yi Sabreen bata jin komai,tana jin ya gama wayar ta juyo ta kalle,bai san lokacin da murmushi ya kuɓuce mishi ba.
YOU ARE READING
Ni da malama ta
Fantasyɓoyayyar soyayya abin dariya ,da kuma sabon salon,rikici tsakanin malama da ɗaliba.