page 43 to44

793 43 0
                                    

🌹 *NI* *DA* *MALAMA* *TA*🌹
     


              *By*
      *fatima* *Batula*

*Dedicated*
       *to* *my* *shadow*

Wattpad @fatimaumarmoddibo

https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/

*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*


*~We are bearer's of so golden pen🖊~*

*~we write assidiously perceive no pain~.*

*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*

*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*

_*Manzon Allaah(ﷺ)* *ya ce;{BA ZAKU WADATAR DA MUTANE TA DUKIYARKU BA, AMMA HALAYENKU SUNA WADATAR DA SU.}*_
°

'''[Sahihut Targib;2661]'''
~~
_Wannan hadisin yana nuna mana cewa duk yanda zaka ba ma mutane dukiyarka to ba zaka iya wadatar da su ba, amma in kana da kyawun hali, kana mu'amalantar su da ita to zasu wadata da wannan kyawun halin. Allaahu a'alam._

'''Allah ta'ala yasa mudace'''

_*ﺳﺒﺤﺎﻧﻚ ﺍﻟﻠﻬﻢ ﻭﺑﺤﻤﺪﻙ, ﺃﺷﻬﺪ ﺃﻥ ﻻ ﺇﻟﻪ ﺇﻻ ﺃﻧﺖ، ﺃﺳﺘﻐﻔﺮﻙ ﻭﺃﺗﻮﺏ ﺇﻟﻴﻚ.​​*_
  
__________________     ​
"Duk wanda ya ce shi ne,ba shi ne ba"

Mu  *GOLDEN* *PEN*
*WRITERS* *ASSOCIATION* ba mu ce mune ba amma fans sun ce muna, ji da kai fariya alfahari kadara isa ba halin mu ba ne.

   Up

      Up
     
         Up

Golden  pen writers association muna tare da allah kuma shi ma yana tare da mu,dan haka mu saka ran mu a inuwa.

ALLAH YA DAGA GOLDEN PEN WRITERS ,AMIN YA SAMI'U.

page4⃣3⃣to4⃣4⃣

Cikin zafin nama Naufal ya janye jikin shi ya miƙe tsaye,yana wani irin numfashi,koƙarin buɗe baki yayi magana yayi,amma ya kasa bakin ma bai iya buɗe shi ba,cikin kasala da rawar da jikin shi ke yi ya gyara jikin shi ya nufi kofa zai buɗe har yakai hannu Haulat ta riƙo shi,juyowa yayi ya kalle ta da rinannan idanuwan shi,ita kanta kasa mishi magana tayi kuma ga bakinta yana son cewa wani abu amma ta kasa,girgiza mata kan shi yayi alamar bazai tsaya ba,sakancewar jikin ta ba ƙwari yasa ya janye hannuwan shi ya fita.

Yana isa falon ba kuwa yaji daɗin hakan sosai dan ko wani baya son ya ganahi a irin wanan yanayin da yake ciki balle su iyayen ta.


Ta gyar ya iya jan motor  ya fita daga cikin gidan,yana fitowa daga gidan ya fara gudu kamar wanda za shi bangon duniya,cikin ƙanƙanin lokaci ya isa gidan su,yana zuwa mai gadi ya buɗe mishi ya shiga,a tsakiyar gidan yayi farkin ɗin motor ya fito.

Ba kowa a falon ko da ma akwai ba zai gane ba tunda halin da yake ciki,kai tsaye ɗakin shi ya nufa,bai kula da Sabreen ba wacce ke kwance akan gadon shi,ya faɗa danne tan da yayi ne yasa tayi ƙara.

"Waiyo Yaya baka ganni ba ne zaka danne ni?

Tashi yayi yana kallon ta da rinnanun idanuwan shi,"Mai ya kawo ki?

"Meya kawo ni ɗakin miji na kuma yaya."

Jin amsar da ta bashi ya tabbatar mishi da taji abinda ya faɗa,dan bai yi tunanin zata ji ba.

"Mijin ki! ya faɗa cikin dakushashar muryar shi.

"Eh ko kai ba miji na ba ne."

Lumshe ido kawai yake yi yana kallon ƙaramin bakin ta,da fararan idanuwan ta  masu hasken gaske kamar auduga.

Ni da malama taWhere stories live. Discover now