page 37 to 38

816 31 0
                                    

🌹 *NI* *DA* *MALAMA* *TA*🌹
     


              *By*
      *fatima* *Batula*

*Dedicated*
       *to* *my* *shadow*

Wattpad @fatimaumarmoddibo

https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/

*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*


*~We are bearer's of so golden pen🖊~*

*~we write assidiously perceive no pain~.*

*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*

*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*


*_لسْــــــــــــــــمِ اللَّهِ الرَّحْمَ الرَّحِيْمِ_*

_*عن أم سلمة رضي الله عنها قالت: أن النبي صلى الله عليه وسلم قال : ” لَا تَدْعُوا عَلَى أَنْفُسِكُمْ إِلَّا بِخَيْرٍ فَإِنَّ الْمَلَائِكَةَ يُؤَمِّنُونَ عَلَى مَا تَقُولُونَ“*.
'''{مسلم: ٩٢٠}'''

_An Kar6o Daga *Ummu-Salma (ra)*  Tace: *Manzon Allah (ﷺ)* Yace: *“Kada Kuyiwa Kanku Wata Addu'a Sai ta Alkhairi, Domin Mala'iku Suna Cewa Aameen Game da Abinda Kuke Fadi”.*_
'''{Muslim:920}'''

*Jamily* *yunus* ƙawar arziƙi ina alfahari da ke,kun wuce page a guri na,plss kiyi hakuri na yarda da kuskure na ina naiman yafiya👏.

page3⃣7⃣to3⃣8⃣.

Ringin wayar tayi har ta katse ba'a ɗauka ba,tsoro ya kama shi,tunda yake da Haulat bata taɓa ƙin ɗaukar wayar shi,cikin hanzari da zaƙuwa ya ƙara kira,nan ma shiru ba'a ɗauka ba,saida yai kira biyar abinda bai taɓa yiba ,amma shiru ba'a ɗau wayar ba,jefar da wayar yayi akan gado ransh a ɓace,haɗe da hura hanci.

"Haulat Allah yasa kina lafiya?
  "Taya zata kasance cikin lafiya bayan abinda ka mata."

Da kanshi yayi tambayar kuma ya ya ba kanshi amsar da ta ƙara ruɗa shi,yasan bai kyauta ma Haulat ba,ya kamata ya sanar da ita koma meye,yanzu idan taji a bakin wani fah.

Tashi yayi ya fara safa da marwa a tsakiyar ɗakin,lissafin shi duk ya dagule,kanshi yayi zafi tunanin halin da masoyiyar shi take ciki yake yi,wanda ya ɗaura laifin akan Sabreen ko kaɗan baya jin zai iya raga mata kan abinda da mishi,zumbur! kamar wanda aka tsungula ya fito da sauri,bibbiyu yake taka matalakar dan sauri,har ya iso cikin  falon bai kula da mutanan dake ciki ba,ya fara ƙokarin fita.

"Ango Naufal ina kuma zaka je ka bar amarya ita kaɗai."

Tsayawa chikk yayi sakamakon jin muryar ko ta wacece,a hankali ya juyo dan ƙara tabbatarwa zaro ido yayi ganin ba ita kaɗai ba..

"Naufal saurin me kake yi,baka kula da mu ba."

Momyn shi ta katse mishi tunanin shi,kallon su yayi,Hajiaya ce ita da Momy da farrah sai Sabreen ɗin wacce ke manne a jikin Hajia, "Meye kuma ya kawo su da safe haka? taya zasu zo mana gida a irin wanan lokacin jiya ne fah muka tare", a ranshi yake wanan tambayar,"To meye wani abun zamu yi waɗan da ba son juna muke yiba",duk a zuciyar shi yake wanan tunanin,bai san lokacin da ya ƙaraso tsakiyar falon ba,sai jin shi yayi zaune a ƙasa,cikin harɗaɗiyar murya haɗe ta aro murmushi ya yafawa fuskar shi ya ce"Ina Kwana momy."

Bai tsaya jiran amsarta ba ya juyo da kallon shi  ga  hajia ya ce"Ina kwana Hajia ya gajiya."

yana kai aya hajia ta ɗauka"Lafiya lau Naufal ka barni da kewa shi ne ko tambayata baka yiba,au naga kamar ba baka so ganin mu yanzu ba."

Ni da malama taWhere stories live. Discover now