page 21to 22

645 42 1
                                    

🌹 *NI* *DA* *MALAMA* *TA*🌹
     


              *By*
      *fatima* *Batula*

*Dedicated*
       *to* *my* *shadow*

Wattpad @fatimaumarmoddibo

https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/

*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*


*~We are bearer's of so golden pen🖊~*

*~we write assidiously perceive no pain~.*

*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*

*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*

_*Manzon Allaah(ﷺ)* *ya ce;{IDAN KANA DA HALAYE HU'DU, TO KAR KA DAMU DON KA RASA WANI ABU NA DUNIYA; TSARE AMANA, GASKIYAR MAGANA, KYAWUN HALI, SASSAUCI A CIN ABINCI.}*_

'''[Sahihut Targib;1718]'''

_Duk wanda Allaah Ya azurta da Wa'yannan halayen guda hudu to ya samu arzikin Duniya da Lahira, kada ya damu don ya rasa wani abu na Duniya, don ya riga ya samu abubuwan da suka fi alkhairi. Allaah Ya azurta mu da su. Allaahu a'alam._

'''Allah ta'ala yasa mudace'''


Na gode na  gode sosai da sosai allah yabar kauna ke ɗin dai ta hannun daman batula.

Page ɗinki ne my sis fauzi uwar rigima.

    
page2⃣1⃣to2⃣2⃣

Ba kowa a falon,daman tayi tunanin hakan dan tasan lokacin da Hajia ke zama a falon,zama tayi akan kujera ta kunna tibi,gaba ɗaya hankalin ta ya koma akan film ɗin da ake yi.

"Ƴar Aljanna" da ƙarfi Hajiya ta kirata.

A tsorace ta juyo "Na'am Hajiya ta"

"Sai kiran ki nake yi,ki zo na baki abinci"

cikin shagwaɓa ta ce"Na ci da kai na,yanzu na girma ba sai kin ɗinga bani abinci ba"

"To ni baki girma a guri na ba"

Dariya tayi sosai sanan ta ce" na sani  ni yarinya ce a gurikin ki,kuma bana son na girma a gurinki , amma a idanan wasu kallon  yarinya suke min,kuma ni na girma,a zuciyarta ta ce "Irin su Naufal"

Cikin shagwaɓa ta kwanta jikin Hajiar ta ce"Hajia gobe ina son zuwa makaranta"

"To Ƴar aljanna allah yakai mu da rai da lafiya"

"Amin hajiyata"

~~~~~~~~~~~~~

Ko da ya isa gidan nasu ba kowa falon yaji daɗin hakan dan duk wanda ya ganshi a irin wanan halin yai yayi zargin wani abu.

Yana shiga ɗakin shi ya faɗa bayi ya shiga ya daɗe a bayin yana zubawa kanshi ruwa kafin ya fito daga bakin.

Kan gadu ya faɗa yana kallon sama a hankali yake lumshe idanuwan shi haɗe da sauke wata irin ajiyar zuciya ,a hankali ya buɗe baki ya ce" Why! Why Haulat idan kina min hakan  wata rana ba zan iya control ɗin kai na ba"Runtse ido yayi,ya san halin mahaifin shi,da irin tarbiyar daya bashi.

Ya daɗe a hakan kafin barci yai awan gaba da shi.

Duniyar mafarki ya faɗa,bari na bishi na ɗauko mana rahuto..⛹‍♀


Wani guri ne mai mugun kyau wanda tsayawa rubuta yadda tsaruwar shi take faɗa lokaci ne.

"Meye sa kike tafiya ki barni bayan kin ɗanɗana min zumarki wacce ki sa na fita haiya shi na"

Ni da malama taWhere stories live. Discover now