1

2.1K 53 0
                                    

°🔘° *MACE TA GARI* °🔘°
          *1441H/2019M.*


®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍️*
_{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}_

      '''🎐G•W•A🎐'''
*_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*



*NA MARUBUCIYA:-*
*MAMAN MUHAMMAD✍🏼•*





    
*~Wattpad @GaskiyaWritersAsso.~*

*SHAFI NA 1* 📑
             

*_________📖* Aunty na gama zan tafi dan bana son yamma tayi min , kin san ana wahalar abun hawa a wajajen nan naku mai kama da ƙauye". Ta ƙarasa maganar cikin zolaya .


Wani mugun harara Aunty ta balla mata sannan tace " amma dai ke ƴar rainin wayau ce wajen namu ne zaki kira da ƙuye ,  bayan yafi wannan kwararon naku ".


Dariya tayi tace "koma dai mene ne , ni zan tafi ".

Mijin Aunty da ke gefe babu abunda yake musu sai dariya domin yadda suka al'amuran su gwanin sha'awa , yace

" kinji Salma ƙyale wannan Auntyn taki , ga kuɗin napep dan har duhu ya fara yi ".

"Haba Yaya , dan Allah ka barshi , wanda Umma ta bani ma basu ƙare ba , sai da safen ku ". Tana gama faɗi ta ƙara gaba , ba tare da ta saurari me zasu ce ba .

Kallon mamaki duka suka bita dashi , mussamnan ma Abokin , Ya Jabir dake gefe yana kallon su , dan tun shigowar su yarinyar ta tafi da imanin shi , yarinya ce ƙaram da ba zata wuce 17 yrs ba amma akwai natsuwa hankali da kuma kyawu .

Juyowa yayi zuwa ga , matar abokin nashi yana faɗin " Hajiya Ruƙayya ? Wannan fa ?".

Kallon shi tayi da mamaki tace " Alhaji Ibrahim , ƙanwa ta ce sai akayi yaya?".


dari yayi yace '' ya naga har kin ɗau zafi , tun kafin kiji meke tafe dani ?".

Mai da kanta gefe tayi tana faɗin " inajin ka ".

sai kuma ya juya gurin Jabir yace " aboki ni dai wallahi na samu ta biyu ".

Da mamaki Jabir ya kalle shi yace " Ibrahim , ksan me kace kuwa ?, ko dai suɓutul kalam  , kayi ?".

Wni ƙayatacce murmushi yayi gama da shafa lallausan sajen shi , sannan ya jingina da jikin kujerar da yake zaune , yace

" wannnan ba za'a kirashi da suɓutul kalam ba sai dai akira sji da suɓutul.ƙalb  , ɗomin daga cikin ƙoƙon zuciyata ya fito". Ya ƙarasa maganar da wani murmushi saman fuskar shi .



" Laa ha 'ila ha illallahu , amma dai anji kunya wallahi , yanzun , kalli tsabar idona , kace min , zaka ma Hajiya Asiya , kishiya , wallahi baka mana adalci ba , kama rasa wadda zaka ce kana so sai ƙanwata uwa ɗaya uba ɗaya , eh lallai abun ya girmama". Ta ƙarasa maganar cike da jin takaicin Ibrahim .

Duk yadda Ibrahim yaso ya fahimtar da Ruƙayya abun ya gagara , daga ƙarshe ma , tashi tayi ta barmusu ɗakin , ba tare da sallama ba ,

Domin tsakanin ta da ƙawarta , kuma matarshi Asiya akwai zumunci mai tsananin ƙarfi yadda babu wanda ke ɓoyewa wani sirrin shi acikin su , hakan yasa ta kasa zaune ta kasa tsaye domin ji take , kamar ita ce Jabir ke shirin yima kishiya .

A ɓangaren IBrahim kuwa , koda ya koma gida , duk yadda yaso ya ɓoyr damuwar shi amma sai da Asiya ta gano damuwa afuskar mijin ta , suna kwance bisa gado ta kalle shi tana faɗin ,


MACE TA GARIWhere stories live. Discover now