3

411 25 0
                                    

°🔘° *MACE TA GARI* °🔘°
          *1441H/2019M.*


®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍️*
_{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}_

      '''🎐G•W•A🎐'''
*_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*



*NA MARUBUCIYA:-*
*MAMAN MUHAMMAD✍🏼•*





    
*~Wattpad @GaskiyaWritersAsso.~*

~GASKIYA DA BANSO FARA LABARIN NAN YANZUN BA SAI JANUARY , AMMA MASU BUƘATAR KARANTAWA SUN ROƘI ARZIƘI NA FARA , AMMA COMMENTS SAI YA GAGAREKU , KU SANI SHIFA COMMENTS KESA WRITER TASAN ANA BIBIYAR LABARIN TA RASHIN COMMENTS KUMA KANSA TA FAHIMCI WAHALAR BANZA TAKE , TO DAN ME BA ZAMU RUNGA YI BA DOMIN ƘARFAFA MA JUNA GUIWA~

*GA SABON TSARI , IDAN KIN SAN KINA KARANTA WA, KIYI MIN MAGANA TA WANNAN NUMBER DOMIN NA TSUNDUMAKI CIKIN FANS ƊINA , 08165728746*

*SHAFI NA 3📑*

*_________📖* Shirye shiryen biki ake tsaf , dan Alhaji Idris yace da zarar ta sun gama zana jarabawar gama secondry zai aurar da ita .

Wannan yasa duk wani faran faran da Walwalar Salma ya ragu , ga wata rama da taje yi , tun Umma na matsa mata taci abinci , har ta daina , dakanta idan taji yunwa zata je ta ɗiba taci .


Ta dawo makaranta kenan dan yanzun da wuri suke dawo wa saboda sun kusa fara exam .


Sallamar da akayi ne a ƙogar ɗakin yasa gabanta mummun faɗuwa , indai ba kunnen ta bane yake jiye mata , to tabbas muryar Asiya take ji a ƙofar ɗakin su ,


Ita ko Asiya batayi ƙasa a gwuiwa ba ta cigaba da rafka sallama , Umma dake ƙuryar ɗaki , ita ta leƙo ta masa gami da kallon Salma da ta tsura ma ƙofar ido kamar wata Statue.

" kedai anyi sakaryar banza wallah , kina ji ana sallama amma kika kasa amsawa , kina can kina tunanin banza da wofi ".

Asiya da ta shigo tace " Kai Umma maybe bata ji bane ,kinsan idan hankalin baya kan abu to da wuya kaji shi ". Ta ƙarasa magaɓar tana zama kusa da Salma .

Ai tsam Salma ta miƙe kamar wadda a ka tsikara ta bar falon ta shige bedroom .

''au kinga halin ko?". Cewar Umma tana bin Salma da kallon takaici .

Murmushi Asiya tayi tace "ƙyaleta Umma kafin na tafi , sai na lallaso ƴar ƙanwata ".

Nan suka shiga gaisawa da ƴan firarraki , sannan ta miƙe tace bari tashi giga wajen ƙawar tata , dan so take ta koma , da wuri , kar yara su dawo islamiya basu sameta ba .


Da sallama tashiga ɗakin ta samu Salma ta kife kai da pillow tana sharɓar kuka , zama tayi a bakin gadon yayin da ta dafa ta , jin an dafa ta yasa ta ɗago kai domin kallon ko waye , ganin Asiya yasan ya hantar cikin ta kaɗawa .


" Salma , tashi muyi magana ".

Babu musu ta tashi , ta zaune gami da share k
Ƙwallarta

"Aduniya , yana da kyau ɗan Adam duk halin da ya tsinci kanshi ya zama mai yarda da ƙaddara  Alkhairi da Sharri , ni ya kamata na kasance a hanlin da kike ciki , Amma kuma cikin Ikon Allah sai bai jarabce ni da hakan ba , domin na sama kaina yarda da ƙaddara ,".

Nisawa tayi sannnan ta cigaba ," da ace zaki taushi zuciyarki , kuma ki danne ta na tabbata , zaki ga ribar hakan , wai ma dai tukun tsaya , kakkyawan mijin nawa ne bakya so koko mene ?". Asiya ta ƙarasa maganar cikin zolaya .


MACE TA GARIWhere stories live. Discover now