2

584 25 0
                                    

°🔘° *MACE TA GARI* °🔘°
          *1441H/2019M.*


®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍️*
_{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}_

      '''🎐G•W•A🎐'''
*_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*



*NA MARUBUCIYA:-*
*MAMAN MUHAMMAD✍🏼•*





    
*~Wattpad @GaskiyaWritersAsso.~*

*SHAFI NA 2📑*

*_________📖*  Washe garin misalin 12 , Aunty Ruƙayya na zaune taji wayarta na faman ruri,

Ganin mai kiran ya sata taɗan murmusa kaɗan sannan ta ɗaga gami da sallama.

Bayan an amsa a ɗayan bangaren , sai aka cigaba da magana ,

" haba Aminiyata wato jiya kika ma Abban su wankin babban bargo".

Jin kalaman Asiya yasa Ruƙayya fahimtar inda zancen ya dosa , amma sai ta nuna kamar bata san komai ba dan gudun kada tayi kwaɓa tunda Asiyar bata fito fili tayi mata maganar ba.

"haba Aminiya wani irin wankin babban bargo , wani abun yace miki nayi halan?".

Asiya da tayi murmushi tace , " nasan ma'ar wazge wannan naki , amma ki jirayi baƙunci na nan da awa biyu , dan kawai ina jiran yaranki su dawo makaranta ne , bacin hakan da kin ganni ".


Ƴar dariya Ruƙayya  tayi tace," Allah ya kawo ki, lafiya ". Daga nan suka katse kiran .




************************************

Tsaye suke a bakin wani gidan mai da alama mota suke jiri .

Su uku mata biyu maza, dukkan su cikin uniform sky blue da navy blue , mata sun ɗora zumbula zumbulan hijab kasancewar , hijab ɗin makaran tar nasu ko kafaɗa bai gama rufe musu ba .

Har motar ta wuce sai kuma tayo baya ahankali dan tabbatar da abunda idanuwan shi suka gane mishi ko gaskiya ne .


Ganin idanuwan shi basu yi mishi ƙarya ba ya gangara har wajen da suke tsaye , sannan ya faka motar shi ya fito .

Wajen su ya nufa yayin da yaba mazan hannu suka yi musabaha , suko matan tunda suka kalleshi sau ɗaya babu wacce ta sake waigawa ,

Domin yarane masu Class da tarbiyya ba sa taɓa ma mutum kallon da ya wuce ƙa'ida , hakan da suka yi sai ya sake burge  shi .

Sai ya cema ɗaya daga cikin mazan ," Abokina Halan mota kuke jira?".

Ɗan sosa kanshi wanda aka tamba yayi yace " wallahi kuwa , gashi yau friday , idan an sako masallaci mota wiya take ".

Jin jina kanshi yayi yace , " to muje in rage muku hanya mana , ga sisters ɗin naku kamar sun gaji ".

Cikin fara ɗayan yace "aiko mun gode Allah ya saka , Hafsat muje a rage mana hanya ".


Jin ance rage hanya dama duk sun galabaita , sai sukayi godiya zasu shiga , amma abun mamaki , Salma ko motsawa daga inda take batayi ba .


ɗaya daga cikin matan ne ta je wajenta tana faɗin , "Salma , muje mana kinga har biyu da rabi fa ".

"ke Maryam ki ƙyale ni , tunda kinga zaku iya hawa motar mutumin da baku sani ba kuje , inya so idan ya kai kawunan ku aka yanke ba shi kenan na ". Ta ƙarasa maganar ranta a haɗe , domin ita uya gaskiyar ta kenan .

MACE TA GARIWhere stories live. Discover now