4

352 22 0
                                    

°🔘° *MACE TA GARI* °🔘°
          *1441H/2019M.*


®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍️*
_{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}_

      '''🎐G•W•A🎐'''
*_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*



*NA MARUBUCIYA:-*
*MAMAN MUHAMMAD✍🏼•*





    
*~Wattpad @GaskiyaWritersAsso.~*

_Wannan shafin sadaukarwa ne a gareku MRS JAMEEL(my Aminiya) INNARO , MOM AYSAR, ina godiya da nuna kulawarku a gareni_😍


*SHAFI NA 4📑*

*_________📖* Tunda rana Asiya ta kira Aunty R ta gaya mata zancen zuwan Ibrahim gurin Salma , hakan yasa  itama ta kira Umma take gaya ma , sannan ta buƙaci Umman da ta ba Salma wayar.


Bayan ta Amsa wayar tayi ma faɗa akan idan yazo karta sake tanuna alamar bata son shi , idan ma ba zatayi magana ba to tayi shiru.

Badan ranta yaso ba ta amsa .

Tun bayan la'asar Umma tasa ta tayi wanka , Ta sanya kaya masu kyau.

************************************

A can gidan Ibrahim kuwa tun da yayi sallar magrib ya kira Asiya yace yana waje tafito su tafi , amma sai tace mai , ba zata samu zuwa ba , saboda kanta da ya matsa mata da ciwo , tasha magani ta ɗan natsu ,.

Yaso ya shiga ya duba ta amma ta nuna mishi babu komai , ya je kai kar dare yayi , babu yadda ya iya haka ya tafi zuciyar shi cike da zullumi .

A dai dai ƙofar gidan yayi parking , yana tunanin yadda za'ayi akira mai ita sai g ƙanin ta Aliyu wanda yake bi mata , zai shiga gidan .

Ganin shi da Aliyu yayi yasa ya ƙarasa inda yake yana gaishe shi .

Bayan sun gaisa yace, "uhum bari na shiga na kira ta". Ya ƙarasa maganar yana yanƙale haƙora .

Bai jiran amsar Ibrahim ba ya juya ya shiga gidan yayin da Ibrahim.ke binshi da kallo dan yaro ne mai barkwanci sosai .


Yana shiga ya iske Salma akan Sallaya tana tasbihi , sai da ya wani haɗe rai wai shi kar a raina shi duk da ta girmeshi , amma ya iya rainin wayau .

" kije mijin ki na magana a waje ".

Jin maganar tayi yadakiɓƙoƙon zuciyarta ,

Kallon shi tayi up nd down , sannan tace ," yaushe na fara wasa da kai?".

Yanƙale baki yayi yace ," A'ah su manya fa za'a yi aure dole a koma serious ".

Tsabar takaicin da maganar ya bata bata san lokacin da ta miƙe , ta ɗauko pillon kujera ta fara dukan shi dashi ba .

Shikuna sakaran sai ya fara kukan ƙarya , jin hakan yasa  Umma dake bedroom fito wa tana faɗin ,

"ke meye haka kuma ?".

Cikin muryar kuka da bata san lokacin da ya kufce mata ba tace " Umma wallahi yaron nan ya raina ni , Allah wata rana sai na ɓalla shi ".

Ganin yadda take kuka , yasa Umma kallon Aliyu tace " Kai Balarabe (dake sunan baban ta ne ) me ya haɗaku ?".

Nan cikin zolaya ya fara ba Umma labarin abunda ya faru , madadin , Umma tayi mishi faɗa sai ta goyi bayaɓ shi , ta juya ta kalli Salma tace ,

MACE TA GARIWhere stories live. Discover now