5

794 44 13
                                    

°🔘° *MACE TA GARI* °🔘°
*1441H/2019M.*


®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍️*
_{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}_

'''🎐G•W•A🎐'''
*_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*



*NA MARUBUCIYA:-*
*MAMAN MUHAMMAD✍🏼•*






*~Wattpad @GaskiyaWritersAsso.~*

*SHAFI NA 5📑*


*_________📖* sosai suka haɗa lefe mai rai da lafiya , Aunty R har mamaki take yadda Asiya bata nuna kishin ta kuma bata ji ƙyashin siyan abu komai tsadar sa , da wata ce wallah ba zata iya ba .


Bayan sun gama haɗa lefe , Asiya ta cire ma Aunty R wanda zasu bada ɗinki , ta miƙa mata , ita kuma ta kaima mawa tela da mesurement ɗin Amarya .

~•~•~•~•~•~•~•~•~•~•~•~•~•~•~•~•~•~•~


Aɓangaren Amarya da Ango kuwa , Salma ta ƙi amfani da waya koda Umma ta magana cewa tayi , sai sun gama Exam dan yanzun inta kunna Wayar zata ɗauke mata hankali, hakan yasa Umma ta yarda da zancen nata ,

Bata san ita ko batason magana da wannan sarkin surutun bane kamar yadda tasa mishi .🤣

Shikam Ibrahim, kullum sai ya kira number ta amma akashe hakan yasa , duk ya nemi natsuwar shi ya rasa ,


Haka akaci sati , kawai yanke shawar bari ya kira , Asiya yasa ta bincika mishi .

Rananr dadare suna cikin waya sai ya sako mata zancen .

"Ina ta kiran wayar ƙanwar ki shiru bata shiga ko lafiya?."

"too , aikam dai ina jin lafiya , amma zan bincika , dama gobe nake nake shirin zuwa gidan akwai saƙon da zan kai mata ".

Cikin gamsuwa da bayanin nata yace " hakan yana da kyau , wani saƙo zaki kaimata ne ?".

Murmushi tayi tace " Abun sirri ne ".

Dariya yayi yace " kuna da wani sirri ne da ya fini , ni mijin ku?".

" akwai mana , ".

Jinjina kai yayi kamar tana ganin shi yace " to faɗi inji dan ya kamata nasan da zaman shi ".

Haɗe rai tayi tace " habibi naga kana son kai mana shishhigi fa tom kayi shiru kawai ".

Dariya yayi sosai , sannan yace " shisshigi kuma ?, duk inda akaje aka dawo , ƙila shirin ma ni aka yima".

"oho dai ba dai zaka ji ba , sai da safe ".

Ta ƙarasa.magnar da wani ƙayataccen murmushi afuskarta ta kashe wayar .

Bata fi 50sc da kashe wa ba sai taji alamar shigowar saƙo , buɗewa tayi ganin daga mijin tane ta fara karantawa cikin murmushi dake bayyana tsantsar farin ciki.

_Allah yayi miki Albarka Asiya , ya saka miki da gidan aljannah , haƙika kin taka wani babban matsayi a zuciyata wanda babu wata mace da zata tunkuɗe ki daga kan karagar masarautar zuciyar Ibrahim , dan haka ki ƙara kwantar da hankalin ki_

Ina miki fatan alkhairi .

Haka ta kwanta tana karanta wannan saƙo mai daɗa sanyaya zuciya da sake sata amincewa da mijin nata ɗari bisa ɗari , ahaka cikin shauƙi bacci yayiɓawan gaba da ita .



You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Aug 04, 2020 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

MACE TA GARIWhere stories live. Discover now