chapter 5

777 25 5
                                    

This chapter is dedicated to @aysherudahmad.
★★★★★★★★★★★★★★★★★★★★
Iskar ma da yake shaqa kawai ta isa ta sanar dashi sun iso qasar shi ta gado wato Nigeria. Yana tsaye Yana laluben wanda suka zo daukan su ya hango qaton farin cardboard an rubuta YARIMA. Fuskar shi ba yabo ba fallasa ya tako har wurin driver din mai martaba yace mishi"mu wuce mallam"jikin driver din na rawa yace "toh ranka ya dade". Haka suka zauna a baya shi da Muhammad driver din mai martaba na jansu. Shirun ne yayi yawa yasa aka kunna mishi karatun al qurani yanaji ya na tunani. A haka har suka ajiye Muhammad a gida Yana ce mishi idan ya huta zezo ya duba jikin mai martaba. 35 minutes drive ne daga gidan su Muhammad zuwa masaurautar adamawa. Gida ne babba na gani na fada don in baka taba shiga ba sai ka bata. Suna isowa fadawa suka fara kwasar gaisuwa shikwa ko kallo ba su isheshi ba. Duk inda ya gifta bayi ne suke kawo mishi gaisuwa amman ko kallo basu isheshi ba saboda SARAUTA bata dameshi ba Kuma burin shi daya a yanzu wato ya gabatarwa da fulani promise din da yayiwa Fatima.
Part din fulani yayiwa tsinke Dan bega me zeyi a sashen sa ba. Yana isowa kuyangin fulani na Mika mishi gaisuwa ,amsawa yayi a takaice ya fada parlour din fulani. Yana shiga maid din fulani tayi mishi iso aka bashi izinin shiga mini parlour din fulani. A zaune ya tadda ita ya tsuguna har qasa ya Mika mata gaisuwar shi cikin ladabi da biyayya. Cikin murna take amsa gaisuwar shi saboda ta dade bata ga tilon danta ba me kama da mai martaba sak.
Yarima ne yace "Fulani na dauka bazan sameki ba"
Fulani tace "Nagama shiryawa dama Kai nake jira Dan nasan sanda jirgin ku ze sauka"
Yarima ya tashi tsaye Yana cewa"Toh mutafi kawai na kosa inga mai martaba"
"Aa yarima kaci abinci ka kintsa sai mutafi ay jikin da Dan sauki akwai improvement ba kamar jiya ba" cewar fulani
Haka ya ci abincin a daddafe suka fito driver ya kaisu asibiti. Ba kowa a asibitin sai waziri Wanda yaxo duba mai martaba. Mustapha ya mugun razana da yaga yadda babanshi ya dawo. Duk ya rame ga Kuma waso wayoyi da machines da aka makala mishi. Ya matukar tausayawa babanshin. Rabon shi da mai Martaba tun sanda ze tafi London da yayi mishi sallama,sai gashi yau ya dawo ya ganshi kwance ba lafiya. Yana tunani yaji motsin Mai martaba alamun ya tashi. Dukkan su sukayi kanshi suna tambayar ya jikinshi. Kai ya kada musu alamun da sauki. Idon shi ne ya Kai kan yarima dake bayan fulani. Lallausan murmushi yayi mishi irin Wanda uba yake wa danshi da ya dade be gani ba. Murmushin ya ratsa zuciyar yarima Wanda be San sanda yaji hawaye a kuncin shi ba.
Chan yarima ya daure ya ce "Barka da yamma mai martaba da fatan jikin da sauqi. Allah ya qara sauki yasa kaffara ne"
Da Ameeeennn fulani da waziri suka amsa.
Nan likita yazo yayi musu bayani akan za a sallameshi washegari amman sai sun kiyaye Kuma sun bi sharadin da aka basu.After likita ya gama musu kashedi da cewar karsu sake ran Mai martaba ya baci if not stroke ne zai kama shi.Bayan kwana biyu Mai martaba yaji sauki sai ya aika a kira masa yarima don suje su gaisa da matansa.Sashin fulanin fara suka fara yiwa tsinke.yarima yasa aka yi musu iso,suka shiga tare da sallama suka gaisa tayiwa Mai martaba ya jikin ya amsa da fara'a tare da cewa "da sauki" tace "Allah ya kara sauki tare da cewar Allah yasa kaffara ce". bayan 30 minutes Mai martaba ya ce da yarima su zo su tafi. fulani fara ta tashi tare da ra ka su har zuwa corridor dinta sannan suka yi sallama ta Koma su kuma suka tafi.
Suna kan hanyarsu da zuwa sashin fulanin sura,yarima Yana tura mai maitaba a wheelchair suna Dan taba hira sai Mai martaba yake cewa yarima "yawwa mustapha daman ban sanar dakai ba cewar na hada auran ka kai da neice din fulanin sura".cak yarima ya tsaya saboda ji yayi duniyar na juya mishi ya kasa motsi sai da suka shafe kamar 2 minute a haka. Tsintar muryar Mai martaba yayi Yana cewa"ina maka magana har so wajan uku kayi shiru ba shawararka nake nema ba. Umarni na baka Kuma nasan kana da biyayya zaka amince"
Daurewa yarima yayi dan a gaban Mai martaba yake amman a zahiri ya mugun shiga rudani. Tunanin sa daya ya ze yi da fatyn sa ga shi Kuma bai da damar yin sa'in sa da Mai martaba saboda likita yace kar a sake a tada masa hankali.
Tun alokacin yaji zazzabi yafara rufe shi haka dai yayi karfin hali suka karasa zuwa sashin fulanin sura haka dai suka shafe wajen 35 minutes a wajen ta sai da suka zaga wajen matan sarkin kwaf sannan ya maida mai martaba sashinsa sannan ya wuce nasa sashin. Yana isa daki yanufa ya zube a kan kayataccen gadon dake malale a dakin ya shiga duniyar tunani a kan taya zai bullowa zancen. Baibi mintuna talatin da kwanciyar sa ba wayan shi ya fara ruri kamar ba zai duba ba Amman kawai wata zuciyar ta raya masa ya daga sai da kiran yazo dab da zai tsinke sannan ya dauki wayan ya duba sai ya ga BAE a bayyane a kan screen din wayan. Sunnan da yayi saving din numbern fatynsa kenan. Haka kurum ya ji gabansa na faduwa . ya daure ya daga jiki a sanyaye yace "hello bae ya kke?
Lpy qalau ya jikin Mai martaba?
Yacce yaji muryarta yasan ba lafiya ba Dan gaba daya muryarta a sanyaye take. Hope komai lafiya naji muryar ki ba dadi ,
Nisawa tayi tace"daman maganar da muka yi rannan ne, yau aka yi family meeting akace in ban fito da miji Nan da 3 weeks ba za a hada aurena da cousin dina Kuma na roqi Abba ya Dan bani lokaci yace shi ba ruwanshi duk abun da Dadda ya yanke daidai ne. Wai ay sun nunamin so da qauna tun ina karama wannan auren ma da za amin cigaban so da qaunan da suke nunamin ne. Tun da muka koma London da Abba kullum idan munyi waya da Dadda sai ya sanar Dani ina gama karatu na zemin aure in haifa mishi tattabakunne me kama da mama na sak. A rayuwa Yana so yaga nayi aure kafin ya koma ga Allah. Nima ina son in cika mishi burinshi Kuma yanzu lokaci yayi Dan banga me zan jira ba na kammala karatuna. I do beseech you idan aure na dakai baze yiwu ba ka fadamin tun kafin lokaci ya kure".dakyar ya bude baki yace mata"faty kin San dai da cewar ina mutuwar kaunar ki kin riga kinzama wani bangare na rayuwata Kuma dai kinsan bazan yaudare ki ba, inshallahu ni ne mijinki!!!".jiki a sanyaye ta amsa masa sabida maganganunsa sun ratsa mata ilahirin jikinta.haka dai yata kwantar mata da hankalu har sai da ya ga kamar ta dan sami nutsuwa kana sukayi sallama da cewar gobe insha Allah ze kirata.
    Gama wayansu ke da wiya yaji wanu zazzabi ya rufe shi gashi zuciyar shi na mashi zafi kamar an zuba mashi garwashi tsabagen zafi. Haka dai yadinga tunane-tunane da yaga hakan bazai fishshe shiba kuma gashi ya kasa yin barci kawai sai ya tashi ya shiga toilet ya dauro alwala yafara nafil-fili. Bai idar ba harse da Al fijir ya keto. Ya data hannu biyu Yana rokon Allah,Allah yabashi fatyn shi tazamo uwar ya'yansa. Yana gaba addu'ar ya shafa sannan ya tashi ya kara tada kabbara don yayi sallah asuba.yana idarwa bayan ya gama yayi adduoin shi sannan ya koma ya kwanta.
    Muhammad ne zaune akan gujerar dake tanede a parlour din shi da waya a hanunsa. Numbern yarima yake ta  ta trying Amman a kashe tun wajen karfe daya yake ta faman kiranshi Amman a kashe gashi yanzu karfe wajen uku ba amo ba labari wayar ta ki shiga kawai sai ya yanke shawarar yaje har fada ya sa meshi.Direct sashin yariman yanufa ya shiga parlourn da sallama Amman shiru ba a amsa ba don haka kawai ya wuce bedroom dinsa kwance ya ganshi a kan gadon shi kudundine a cikin bargo Yana mushas-sharan sanyi ga dakin yadau sanyi saboda AC da take a kunne. A hanzarce ya karasa cikin dakin yayi sauri ya kashe AC da take a kunne ya hanzarta karasawa gurinsa janye bargon dake jikinsa yayi jiyayi wucin zafi nafita daga jikinsa yayi saurin sa hannunsa a goshinsa ji yayi zafi dau tamkar garwashi.da sauri yafita yakira fadawan daje tsaye a gurin kofar shiga sashin yace musu su shigo su taya shi daukan yariman sannan wasu su je su fadawa fulani fara yarima bashi da lafiya sannan kuma zai wuce da shi hospital. Suka amsa da toh suka tafi sannan wasu suka taya shi daukan yariman suka sashi a cikin motar Muhammad din sannan yaja ta a guje.suna isa da sauri a ka karbesu sabida yadda suka ga jikin yariman.
     Emergency room aka shiga da su saida suka shefe wajen 2hours akan yariman.kan lokacin fulani fara da tawagarta sun iso. tana ta kuka sabida yarima shi ka dai Allah ya azurta ta da shi ana ta rarrashin ta Amman kamar kara ce mata suke tayi. Likitane yafito yace da fulani fara ta biyo shi zuwa office dinsa.ta shiga da sallama yayi mata nuni da ta zauna a kujerar da take facing dinsa ta zauna tana kara share hawayen da ke zubo mata.likitan ne yace da ita " a yanzu yarima yana cikin wani hali saboda yanzu ciwon zuciya ne ya ka mashi kuma jininsa ya hau sosai shiyasa ma zuciyarsa ta kumbura"a sanyaye ta amsa da" toh".ta shi tayi jiki a sanyaye zata fita daga office said ta jiyo ta ce da likita "a wani room yariman yake"sai ya ce da ita"yana intensive care unit wato ICU room 20."ta amsa da" toh."
A hankali ta bude kofar dakin tare da yin sallama bakowa a ciki kai tsaye tawuce wurin daya ke kwance ta janyo stool ta zauna ta zuba masa ido tana tunani kome yasa shi hawan jini har yasa zuciyar shi kumbura.ta jima a hakan tana ta kallonsa sai gani tayi ya fara motsi da hannayen sa ita ta za ta  ko hallucinating take can sai taga like kamar zai bude idanunsa aikwa sai taga ya bude su, a hanzarce tayi waje tace da Muhamma yaje office din likitan yace masa yariman ya tashi.bai fi minti biyu ba sai ga muhammad ya dawo tare da likitan.suka shiga dakin   a gaggauce likitan ya fara duba shi sai da ya shafe mintuna Yana duba shi sai daga baya ya dago yace da su "Alhamdulillah jinin nasa ya dawo normal Kuma it's like zuciyar tasa ta sace yanzu shiyasa ma ya farka."sai ya juya ga muhammad yace da shi" muje office dina zan baka list din magunguna da ze dinga sha in yaso sai kuje pharmacy ku saya."ya amsa da "toh ."bayan sun fitane fulani fara ta juya ta zauna kusa da yarima ta kalle shi a sanyaye tace da shi "ya jikin naka" cikin sanyin murya ya amsa da " sauki."
Fulani Bata fadawa kowa yarima bashi da lpy ba saboda bata son Mai martaba yaji bashi da lpy Kuma saboda gulmar GIDAN SARUTA. Waziri kawai ta fada wa shima saboda Yana matuqar kaunar yarima Kuma dayake qanin Mai martaba ne. da waziri ya shigo dubashi ne ya tsare shi da tambayoyi akan me yasa a ranshi da yake tunani har ciwo ya kama shi.
Fulani ma tambayar shi take me yake damin shi da har yasa mishi hawan jinin. a hankula yake kallan su da kyar ya bude baki yace mata" ba komai ."  tace
"taya zaka ce mana ba komai main while likita yace min tunane-tunane ka ke yi har yasa maka  hawan jinin ."yai shiru Yana tunanin ya fada musu abunda ke faruwa kokuma yayi shiru kawai sai wata zuciyar tace da shi kawai ya fada musu. Jiki a sanyaye ya kwashe abunda yafaru tsakaninsa da Mai martaba da kuma yadda ta kaya tsakaninsa da faty sannan Kuma ya daura dacewar" Kuma wlh in ban aure faty ba wlh zan iya rasa raina."
Sai kawai yasa kuka. Kukan me tsuma duk zuciyar me sauraro. Waziri ne da fulani suka zuba mishi ido suna kallon shi dan a iya idanun yarima mutum ze karanto nimbin tarin soyayyar da yake wa Fatima. Kuma gashi yanzu me martaba yace sai na auri faiza yar gidan kanwar fulanin sura. Ba shawara ya ke bani ba Wai umarni yake bani Kuma bazan iya bijirewa umarin mai martaba ba. Shiru fulani da waziri sukayi. Tabbas sun hango abun da yasa yarima shiga halin tsaka me wuya.
Hello readers, Dan Allah kuyi hakuri na koma school komai sai a hankali Amman stay tuned for more chapters.
Ku biyo ni kuji ya yarima yake auran Fatima
Shin yarima Yana auren niece din fulani sura???
Keep reading zakuji komai
VOTE 😊
COMMENT 😊
SHARE 😊
I love you all❤️

GIDAN SARAUTA 👑Where stories live. Discover now