SAUYIN RAYUWA

380 20 1
                                    

🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺

    🕊 *SAUYIN RAYUWA*🕊

💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞

*Story*
      *And*
          *Writing*✍🏽
                 *By*
*Salma Mas'ud Nadabo*👑

*Edit by*:
   *Aliyu Miko Muhammad*

🌲 *REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM*🐄
('''We are the best among the rest''')

https://mobile.Facebook.com/Real-hausa-fulani-writers-forum-RHFWF-17394973194167/?refid=52&red=operaspeedsdial&-tn_-H-R

*Email*:Realhausafulaniwritersforum@gmail.com
*Facebook*:www.Facebook.com/REALHAUSAFULANIWRITERSFORUM.com

Free page:

*Page: 7_8*

Tafiya take a hankali ɗauke da farantin ta na talla, ƙwalla mata kiran da akeyi ne ya sata waigowa tana sakin murmushi, jummala ce ta qaraso kallan ta Nihal tayi ta ce, "jummala ina farantin ki na talla?
   fadada murmushin ta Jummala tayi ta ce, "ai yanzu Inna ta daina ɗaura min talla tun rana dana dawo kawu Sani ya zo gida ya dinga yima inna faɗa yace idan kuɗi take buƙata duk wata zai dinga turo mata idan sana'ar take sha'awa to tayi a gida ba sai na fita ba," rausaya kai Nihal tayi ta ce, "gaskiya na taya ki murna Jummala rayuwar talla bata da daɗi," ta ida zancan idanuwan ta sun ciko da kwalla, "insha Allah Nihal zan taya ki da addu'a in Allah ya yarda sai kin daina talla sai kin samu ƴancin ki kamar kowa ce ƴar gata" hawayan dake maƙale a idanuwan tane suka sulalo Jummala tasa hannu ta goge mata, "Bari nayi sauri na wuce,"
"to shikenan Nihal ki kula da kanki kin ji,"
"to Jummala nagode" ta faɗa da ƙarfi lokacin da tayi ma Jummala nisa da ƴar tazara.

    Dandazon maza ne birjik majiya ƙarfi, ban da warin taba dana wiwi babu abinda ke tashi gurin danbe, sai kururuwa da kirari da akewa ƴan danben haka Nihal ta raba wajan ƴan uwan ta ƴan talla ta zauna tana kallon yadda majiya ƙarfi ke danbe. 
 
    Wani rusheshan ƙato ne ma'abocin ƙarfi ya zauna gefen Nihal bisa tebiri, tare da janyo tire din gyadar Nihal yana dauki ɗai ɗaya yana ci yana kallon danbe, haka ta rinƙa ciniki kasancewar akwai mutane da yawa a wajan, wannan rusheshan ƙaton dake zaune kusa da Nihal sai da yaci gyadar saba'in zaman sa.

   Gab da magrib Nihal ta gama cinikin ta tsaf, cikin sanyin murya ta ce, "malam nagama ciniki kai nake jira ka bani sauran kuɗin," wata irin dariya ya saki ya ce, "wani kuɗin gyada kuma,?
   "wadda ka ci yanzu ta naira saba'in," dariya ya kuma saki tare da zunguro bangis dake kusa da shi, shima wani murɗaɗɗan ƙato ne guda ya ce, "Bangis wai naci mata gyaɗa sai na bada kuɗi," bushewa da dariya Bangis yayi yana kallon Nihal da jajayen idanuwan shi ya ce, "yo ke ko cinki yayi kina tunanin biya zaiyi balle gyaɗa" ya ƙara sakin dariya abokin banza ya ce, "faɗa mata dai, ni wannan tama min kaɗan ban iya cin ta sai dai na ci uwar tata mai ɗaura mata tallar," dariya Bangis ya saki tare da miƙawa abokin banza hannu suka kashe, kuka Nihal ta fara tare da rokwan su Allah annabi su bata kuɗin  ta daga ƙarshema wuka abokin banza ya curo yace, idan ta ƙara damun shi sai ya farka mata ciki.

  Haka Nihal ta biyo hanya tana kuka maicin rai duk gurin da ta samu sai ta zauna tayi kuka san ran ta, Allah sarki rayuwar, yau Nihal ta zama abin tausayi, yau ita ke ganin Sauyin Rayuwa, har kusan bayan magriba tana yawo ta kasa komawa gida, ta fuskanci horo wajen Gwoggo wani dutsi ta gani dake bakin hanya ta zauna tare da ɗaura kanta zaman ƙatatunta tana kuka saboda tsabar kuka muryar ta ta dashe.

  Dafatan da akayi ya sata razana ta miƙe da sauri tana ƙoƙarin arcewa, jin an riƙe mata hannu ya sata tsayawa tana sauke ajiyar  zuciya, cikin sanyi murya ta ce, "yaya.! tare da sakin marayan kuka ta ce, "yaya" faɗawa jikin shi tayi tare da sakin kuka, lallashin ta Yaya  ya shiga yi cikin shessheƙar kuka ta labar ta masa abinda ya faru, ta cigaba da cewa "wallahi yaya na koma gida ba kuɗin nan Gwoggo kashe ni zatayi"
"shhhh ya isa daina kukan haka kinji" zaunar da ita yayi saman dutsin yana facing nata sai sauke ajiyar zuciya take muryar ta duk ta dishe, "nawane kuɗin,?
  "naira saba'in" ta faɗa da shaƙaƙiyar muryar ta,
"Ƙanwata bana so kina kuka kin ji, kwata-kwata baki dace da talla ba, insha Allah sai kin zama wani abu a duniya wadda kowa zaiyi al'fahari dake kanwata, daga yau idan an baki talla ki rinƙa zuwa kina samuna a wurin nan," murmushi Nihal ta saki mai nuni da farin cikin ta.

  Naira dari ya curo ya miƙa mata sannan ya riƙe hannun ta ya rakota har ƙofar gida sannan ya juya yana tausayawa irin rayuwar da Nihal keyi.

   Ɗauke da sallama a bakin ta tashigo, kusan duka ƴan gidan suna tsakar gida suna hira cikin nishaɗi  kallo ɗaya zaka masu kasan basu da wata matsala, gaban Gwoggo Nihal ta ƙaraso tare da duƙawa zata bata kuɗin Mudi dake kusa da Gwoggo ya ce, "Gwoggo ya maganar  kuɗin da kika ce zaki bani," murmushi  Gwoggo ta saki ta ce, "dama waƴannan kuɗin kai nayi niyar bawa su, tunda kana kusa sai ka amshi abinka," jin haka yasa Nihal miƙawa Mudi kuɗin hannu  ya kai tare matse hannuwan ta yana mata wani shu'umin kallo rawa jikin Nihal ya ɗauka ganin irin yadda yake matse mata hannuwan ta cikin wani irin salo kuma yaki sakin su wani irin ƙarfi ne ya zo mata ta fizge hannunta ta tashi, da Sauri tayi ɗakin su, tana shiga ta zame bakin ƙofa tare da sakin marayan kuka marar sauti.

   
      *_TUNA BAYA_*

Malam mamman  haifaffen ɗan wani kauye ne da ke cikin ƙauyen Shanono yana zaune da matan sa biyu Larai da Lantana, malamin Al'majirai ne sannan yana noma sosai kasancewar sa bafulatani haɗe da kiwon dabobi.

Lantana itace uwar gida tana ɗa ɗaya mai suna Tanimu wanda shine ɗan fari a gidan malam , tunda Lantana ta haifi Tanimu bata sake haihuwa ba har tanimu yayi wayo sosai kasancewar, malam  mutum ne ma'abocin son yara sai ya ƙaro aure ba irin kishin da Lantana bata zubaba haka Larai ta zauna zaman haƙuri har Allah yasa ta samu ciki malam yayi murna sosai da jin labarin Larai tana ɗauke da juna biyu.

  Bangaren Lantana ko ji take kamar ta hadiyi zuciya ta mutu,

  A kwana a tashi ba wuya wajen Allah har cikin Larai ya isa haihuwa. Ta haifi santalelan ɗan ta ranar suna yaci Abubakar ana kiranshi da Habu

   Duk irin rigingimun da Lantana ke nema wajen Larai ta ƙi bata fuska sai ma Ladabi da biyaya da take mata hakan yasa ta zubar da makaman yaƙin ta suka zauna lafiya, haka Larai ke kula da Habu da Tanimu duk da Tanimu ɗan kishiya ne amma haka take kula da shi tare da ɗan ta ba tare da nuna ban banci ba, hakan nayi ma mahaifiyar Tanimu daɗi sosai sai dai tun tasowar Tanimu yaro ne Marar jin magana da San abin duniya.

  Bayan wasu ƴan watanni Larai da Lantana suka fara laulayi, murna wajan malam ba'a cewa komai saboda tsabar farin ciki.

  Kulawa sosai suke samu wajen mijin nasu inda suke ƙoƙari wajan haɗa kan ƴa-ƴan nasu Tanimu da Habu

Yau ta kama asabar ranan ne su Larai suka tashi da naƙuda...

'''Taku har kullun salma mas'ud nadabo'''

SAUYIN RAYUWAWhere stories live. Discover now