SAUYIN RAYUWA

296 15 1
                                    

🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
          🕊 *SAUYIN RAYUWA*🕊
💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞
   *Story*
        *And*
             *Writing*✍🏾
                    *By*
*Salma mas'ud nadabo*👑

🌲 *REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM*🐄
('''We are the best among the rest''')

*Page: 43_44*

   Daran yau daga umma har Nihal ba wanda ya rintsa saboda zazzabi dake damun umma a hankali Nihal ta daura kan umma a saman cinyar ta, tana shafa kanta wanda jikin yayi rau kamar  garwashi, wasu hawaye ne ke sulalowa Nihal tana sa bayan hannun ta tana gogewa kwantar da umma tayi ta fita ta debo ruwa ta dawo ta dau zani ta nufo umma tare da maida ta bisa cinyoyin ta tana danna mata ruwan a hankali tana cewa, "umma sannu kin ji Allah ya baki lafiya" sai dai umma ta daga kai ita ka d'ai tasan abinda take ji.

                     ****
Sultan nashiga part nashi wanka ya sake ya fito sanye da bathrobe da dan k'aramin towel yana tsane jikin shi knocking din kofar da a keyi ne yasa shi tsayawa da goge gashi kanshi yana kallon kofar, cikin honey voice din shi Sultan ya ce, "koma waye ya jira ni a parlour na gama shiryawa" jin hakan yasa, khalifa tsayawa a parlour tare da zama saman kujera ya b'oye wuk'ar dake hannu shi cikin riga, janyo lotion Sultan yayi ya shafa sannan ya bude wardrobe ya curo fara jalabiya me kyau ya saka masha Allah tuni kyan Sultan ya fito, yayi kyau kamar balarabe sannan ya feshe jikin shi da turare a hankali ya bude handle din kofar daki tun da ya hango khalifa yake sakin murmushi tare da k'arasowa cikin takun shi na mulki hannu wanshi na hard'e a baya, da sauri khalifa ya mik'e kan shi a k'asa ya ce, "Ranka yadade barka da wannan dare dama  na zo na taya ka hira ne,"
      Murmushi Sultan ya saki yana bin khalifa da kallo yace, "amma fa ka kyauta khalifa, sai dai kuma kash main parlour zani dinner yau sweetheart  tasa an dafa min  favorite food dina, ko zamu je tare muyi dinner tare? Murmushi khalifa ya saki ya ce, " ranka yadade  ban dade da cin abinci ba na gode da tayin ka, Allah ya k'ara maka tsawan cin rai,"  gajeran murmushi Sultan ya saki yana kallon khalifa ya ce, "mu tafi ko" Sultan na gaba Khalifa na baya zaro wuk'a yayi daniyar caka ma sultan har ya d'aga zai caka  wuk'ar ya ga alamar zai juyo sai ya maida wuk'ar yana maidawa Sultan ya juyo yana murmushi ya matso kusa da khalifa kamar me rad'a ya rungume shi tsam a jikin shi ya ce, "a duk inda kake ka iya takun ka, saboda mak'iya na zagaye da kai , so dayawo ana kashe mutum ta hanyar wanda ya yadda da shi, amma ka sani mutane da yawa nayi ma kallon biri kai kuma kanayi masu na ayaba shiyasa nake son ka, kasancewar ka jarumi, " Sultan ya shafa k'ungu shi yace yana sakin murmushi, "saboda kullun kana yawo da makamin saboda mak'iya idan nine kai da mindiga zanyi yawo" wani irin miyau khalifa ya had'iya me d'aci, take a nan jikin shi ya fara rawa, amma sai yayi ta maza ya daure yana murmushi yak'e, Sultan ya katse shi da cewa, "idan makashin ka ya shigo gidan ka idan kai ne me zaka mashi,? baki khalifa na rawa yace, "kashe shi zanyi" dariya Sultan yayi yace, "Ni bana kashe mak'iyi na a ranar farko sai a rana ta biyu" sannan Sultan ya kakab'e rigar khalifa yana shu'umin  murmushi yace, "muna iya tafiya" jiki a sab'ule khalifa ya fito duk sai ya ji ya tsani kanshi.

     Direct main parlour Sultan ya wuce lokacin kowa ya halara a dining area shi kad'ai ake jira, dauke da sallama a bakin shi ya shigo Gimbiya jalila dake zaune sai da tasha jinin jiki ta, tana bin Sultan da kallo jan kujera yayi tare da zama kusa da ammi yana murmushi ya ce, "ya dai matar na ga duk kin wani bi kin tsure ko tsoran kar na ce ki sha maganine," yana maganar yana kallon Gimbiya jalila ko ba'a fad'a mata ba tasan wannan magana da biyu akayi ta an jefi akuyar kishiya, murmushi maimartaba yayi ya ce, "Ku dai baku gajiya kai da ammi," murmushi ammi tayi tana jawa Sultan kumatu tace, "wannan bokan turan wallahi ya ishe ni," basmal ta ce, "mu dai bamu shiga tsakanin ku, ka shiga kasha kunya" tana maganar tana saving din Sultan waina da biyar taushe wadda taji yan'ciki da kaji da naman rago ga man shanu ya ji, tun kafin ta ajewa Sultan ya fara lashe baki yana cewa, "sweetheart wannan shagalin duk ni ka d'ai gaskiya zan baki tokwici," murmushi basmal ta saki tana aje mashi plate din, Nazili da mom suka hada baki wajan cewa, "wannan abun har da son kai shine kika wareshi shi kad'ai kika mashi wannan shagalin ko," Nasim yace, "nima yaya zanci" minal tace, "nima" ita da shukura suka had'a baki wajan fad'i dariya Basmal tayi tana cewa, "ai shi yayana bai san cin abinci shiyasa na yi mashi favorite nashi ko ya samu ya ci," Ashad dake gefe sai aika masu da harara  yake da ya sannan da wannan abinci da guba zai sa mashi ko shinkafar b'era yaci ya mutu, a haka suka gama dinner din wasu na farin ciki wasu zuciya cike da mugunta.

  Bayan sun gama dinner Sultan ya ruk'o hannu ammi suna tafiya suna ta6a hira har suka k'araso dakin ta ta zauna saman sofa tana cewa, "Sultan wai yaushe ne zaka kayi aure ka ga mun zuba maka idanuwa amma har yanzu shuru, naga alamar ma maimartaba bai damu da zancan kayi aure ba ya zuba maka na mujiya," hade rai Sultan yayi tare da daura kan shi saman cinyar ammi yana cewa, "shi fa aure lokaci ne ni har yanzu ban samu wadda ta kwanta min a rai ba," ture shi ammi ta shiga daga cinyar ta tana cewa, "kai kullun aka yima maganar aure sai ka hau wa mutane wasu jawabi, ko dai baka da lafiya ne? dariya Sultan ya saki yana jan bedside drawer yana cewa, "lafiya ta lau ammi garas nake lokaci dai nake jira" yana maganar yana balo mata magani, duka ammi da kai mashi ya goce tana cewa, "ja'iri  indai da gaske kake mu gani a k'asa," to Sultan yace yana mik'a mata  glass cup ta amshi glass cup din ta kora  magani, Sultan yayi kissing goshin ta yace, "matar Allah ya baki lafiya" tace, "ameen," sannan ya fito.
     direct part nashi ya wuce yana shiga bedroom ya iske night dress din shi saman bed zurawa kawai yayi ya fad'a bed yana tunanin maganar da ammi ta mashi, shi kan shi bai samu peace of mind ba yama za'ayi yayi aure, shi kwata-kwata aure baya gaban shi ma yanzu hasali ma mata haushi suke bashi tunda Asiya taci amanar shi, aka had'a baki da ita wajan kashe shi, watsar da zancan yayi bacci me dadi yayi awangaba da shi.

                       ****
  Sanyi-sanyin Asubane yasa umma yin bacci gyara mata kwanciya Nihal tayi sannan ta fito ta dauro alwala ta koma ta gabatar da sallah, bayan ta idar ne ta sake tab'a jikin umma har yanzu jikin da zafi amma ba kamar jiya da daddare ba.

Fita tayi ta fara aikace aikacanta na yau da kullun kasancewa yau wanki jiya zata k'arasa dan haka yau ba talla, ruwan koko ta daura sannan ta koma bakin rijiya tana jan ruwa, sai da ta gama cika ko ina na gidan sannan ta shek'a koko ta juyewa su gwoggo nasu abokiti ta d'ibi nasu, ta d'umama tuwo ta aje da sauri ta kwashe nasu ta kai daki tana fitowa suka hade da gwoggo ko kallo bata ishe ta ba ta dau kayan kalacin su ta shige daki, sauke ajiyar zuciya Nihal tayi ta koma dakin su lokacin umma ta tashi murmushi ta saki tare da jinginar da umma ta zuba koko a cup ta fara ba umma kurba d'aya zuwa biyu umma tayi ta fara kakarin  amai sai da ta amaye kokon tas tana maida numfashi.

SAUYIN RAYUWAWhere stories live. Discover now