SAUYIN RAYUWA

349 21 1
                                    

🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺

   🕊 *SAUYIN RAYUWA*🕊

💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞

*Story*
     *And*
         *Writing*✍🏽
               *By*
*Salma Mas'ud Nadabo*👑

*Edit by*:
  *Aliyu Miko Muhammad*

*follow me on wattpad:* salmamasudnadabo

🌲 *REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM*🐄
('''We are the best among the rest ''')

https://mobile.Facebook.com/Real hausa-fulani-Writers-forum-RHFWF-17394973194167/?refid=52&red=opera-speed-dial&-tn_-H-R

*Email*:realhausafulaniwriters@gmail.com
*Facebook*:www.Facebook. com/REALHAUSAFULANIWRITERSFORUM.com

*Free page:*

*Page: 9_10*

Ko da unguwar zoma ta shigo cikin gidan ɗakin Lantana ta fara shiga saboda ta riga Larai soma naƙuda tasha matuƙar wahala sosai,  daga ita har abunda yake cikin ta basu rayu ba, Lantana ta rigamu zuwa gidan gaskiya ko da Labari ya riski Malam yayi kuka sosai, Allah sarki Ashe haihuwa ce ajalin Lantana haka ya rinƙa sunbatu ga fargabar itama larai kar ya rasata.

     Tun kafin unguwar zoma ta isa ɗakin larai, larai ta haifi ƴan biyu maza masha Allah daga nan murna da rashi suka haɗe wa malam, wunin ranar zungur ba Wanda ya iya labarta wa Larai mutuwar Lantana, da tace zata je ganin abunda lantana ta Haifa sai ace mata ta bari ta huta tukun.

   Bayan an kai Lantana ma kwancin tane malam ya dawo gida, ya shigo ɗakin larai Duk ƴan zaman barka suka fita, zama yayi a saman gado tare da fuskantar ƴa'ƴan nasa ya amshe su yayi masu huɗuba sannan ya kalli Larai tare da gyara murya yace, "kin san cewa duk wani mai rai mamaci ne Larai kuma Allah daya fimu so ne yake amsar bayin shi," shuru Larai tayi Duk jikin ta yayi sanyi, sannan malam ya ce, "Allah yayima Lantana rasuwa daga ita har abinda ta haifa."

  Kuka larai ta saki tana sanbatu "Allah sarki Allah ya jiƙanki yaya, Allah yasa mutuwa hutuce a gare ki" daƙyar malam ya lallashe ta, tayi shuru haka dai akayi zaman barkar uwar jego ba wani Kuzari.

  Ranar suna yara suka ci suna Hassan da Hussaini.

  Tun da Lantana ta bar duniya Larai ke kula da Tanimu da ƴa-ƴa ta bata gwada masu ban-banci komai tare take masu da ƴa'ƴan ta, sai dai Tanimu yasa ma ranshi baƙin hali Don gani ma yake kamar baƙin cikin Larai ne ya kashe masa mahaifiya, shiyasa kullum a ƙullace yake da ita, gashi bugu da ƙari Habu ya fishi komai tun daga ladabi da biyaya da iya zama da mutane, shiyasa malam yake nuna mai so ba wai dan baya san Tanimu ba, sai dan ya gyara halaiyar shi, hakan sai ya dasawa tanimu hassada a zuciyar shi da baƙin ciki gami da kyashin ɗan uwansa  Habu.
 

Bayan wasu ƴan watan ni ma,  inna ta ƙara  samun wani cikin  tasha wahala sosai sannan  ta haifi 'ƴa mace tun daga nan bata ƙara samun wani cikin ba, saboda wahalar data sha.

*Bayan Shekara Goma (10)*

"Yanzu saboda Allah Tanimu abinda kake kana kyautawa? Malam ya cigaba da cewa,
"kai kaƙi boko saboda wai baka iya zarya daga shanono zuwa ƙauyen nan, sannan ƴar nomar ma baka iyawa har sai Habu ya dawo sannan  shi zaiyi ta kai kana can kana yawon banza wannan ba rayuwa bace tashi ka ban guri," malam ya faɗa cikin tsawa.

Tanimu kansa dake duƙe gaban malam ne ya miƙe yana gunguni yana cewa, cikin gunguni, "tun da su uwar su na da rai ai dole a fifita su akai na."

Inna dake bakin rijiya ce ta ce, "mikake cewa,? Tanimu wai kai me yasa baza kayi hankali ba kullun idan malam nama faɗa sai kaita magana kasa-ƙasa bayan nace maku yin hakan tamkar zagi ne kake ma iyayan ka"
   ko saurarata baiyi ba yana huci ya fita.

Inna tace, "Allah ya shirya min kai Tanimu, sannan yaji kan Yaya".

   Yana fita yaci karo da Habu ya dawo daga makaranta janye da kekyan shi, murmushi Habu ya saki ya ce, "Yaya"
Ɗaure fuska tanimu yayi yana ji kamar ya kashe shi, "shi wai mai tarbiya ai wallahi wata rana shi da kanshi zai ga bayan shi" maganar da Habu  yayi ne ya katse masa tunanin da cewa, "dama Yaya dazu ne muka haɗu da malam Barau, rediyon sa ta lallace shi ne nace ya bani na gwada, ko zan iya gyara mai tun da ana koya mana sana'oi a makaranta, aiko ina kwancewa na gyara ta gyaru, shine ya ban narai hamsin."

  Tanimu ne ya ƙara hade rai a karo na biyu tare da nuna hassada shi yace, "to sai akayi yaya dan ya baka hamsin.?

"Dama hamsin ɗin zan baka, ka ɗau talatin ka bani ashirin tunda kai Babba ne" washe baki Tanimu yayi yac e, "kai amma nagode ina ma laifin ka bar min hamsin ɗin tunda na fika buƙatar kuɗi"

  Murmushi Habu yayi mai nuni da jin daɗi shi ya ce, "ka ɗauka yaya na baka" sannan ya shige gida bai tsaya saurara godiyar da Tanimu ke masa ba.

  Ɗauke da sallama ya shigo a bakin shi malam da inna na zaune a tabarma har ƙasa ya duƙa ya gaishe su sannan ya shige ɗakin su, ya cire uniform ɗin shi ya fito ɗauke da kayan zuwa gona, murmushi malam yayi ya ce, "haba malam Habu daga dawowa ba hutawa bare cin abinci zaka tafi gona, dawo ka zauna ka huta zuwa yamma ka je,"
  ba musu ya dawo ya zauna inna ta zubu masa tuwo da miya ya ci ya sha ruwa yana ƙoƙarin miƙewa ne su Hassan suka shigo da gudu gida, tare da ƴar ƙanwar su Haulatu da alama daga makarantar allo suke.

    Idi ne zaune da Tanimu saman tabirin mai shayi, Idi yace, "gaskiya Tanimu kayi ma kanka faɗa, na lura habu so yake ya ƙwace girman ka ya zama nashi, tun wuri ka tashi tsaye, in ba haka ba ka sha mamaki, nan gaba gonar malam sai ta zama tashi indai kana zuba ido, gashi har shanono yake zuwa makarantar boko  yake hudawa"
  wani bakin ciki ne Tanimu ya hadiye yace, "in dai ina numfashi a duniya zaka ga yadda zan mai da Habu sai ya zama marar anfani daga shi har ƴan uwan nasa da yake taƙama da su".
"ai ɗan kishiyar uwa ba ɗan uwa bane" inji Idi  ya da zancan yana afa ƙuli a bakin shi.

'''Taku har kullun Salma Mas'ud Nadabo'''

SAUYIN RAYUWAWhere stories live. Discover now