SAUYIN RAYUWA

268 3 1
                                    

🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
   
     🕊 *SAUYIN RAYUWA*🕊

💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞

  *Story*
        *And*
             *Writing*✍🏽
                     *By*
*Salma Mas'ud Nadabo*

*Edit by*:
      *Aliyu Miko Muhammad*

*Follow me on wattpad: salmamasudnadabo*

🌲 *REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM*🐄
('''We are the best among the rest ''')

https://mobile.Facebook.com/Real-hausa-fulani-forum-RHFWF-17394973194167/?refid=52&ref=opera_speed-dial&-tn_-H-R

*Email*:realhausafulaniwritersforum@gmail.com
*Facebook*:www.Facebook.com/REALHAUSAFULANIWRITERSFORUM.com

*Free page:*

*Page: 37_38*

       Ba Alex ba hata bayin da ke bakin kofa sai da suka tsorata da irin kiran da Sultan keyi ma Alex da sauri Alex ya bude kofar part din sultan tare da fadawa suka shigo, turus suka tsaya suna bin gawar Asiya da kallo suna kallon Sultan da sauri Alex ya k'araso gaban Sultan yana taba jikinsa wanda a lokaci Sultan ranshi a bace yake ko ufan ya kasa cewa Alex ne ya ce cikin damuwa, "Sultan are you okey hope dai ba abinda ya same ka? Katse shi Sultan yayi ta hanyar daga hannu ya fara magana cikin sanyin murya da nuna gajiya ya ce, "ina anfanin ku? babu ace duk securities din dake bakin part dinna har kofar daki na babu wanda yamin anfani, wai me yasa baza a barni na huta ba why..! Wani irin d'aci ne ya d'arsu a zuciyar Sultan da tsanar mata ya cigaba da cewa, "tunda na taso da wayau na ake bibbiyata tun ina da 10 years na bar Nigeria saboda irin haka, an kaini inda ba wanda na sani sai  securities da na k'ara girma na fada ma yan'uwa na inda nake tunda na fadi ban k'ara samun peace of mind ba, har rana me kamar ta yau me yasa ake bibbiya tane why, me na aikata haka mai yasa kowa ya ra6eni burinsa ya ga bayana" Sultan ya ida zancan cikin sanyin murya  Alex ne yayi hugging nashi yana shafa bayan shi cikin nuna lallashi yana cewa, "relax Sultan everything will be ok" sannan ya zauna da shi saman kujera lumshe idanuwa Sultan yayi ya ce, "miko min wayana" iPhone din shi Alex ya mika mashi fadawa da bayin part din shi dake tsaye abin tausayi da securities Alex ya ce masu kowa ya koma bakin aikin shi sannan kada wanda ya kuskura ya bari cikin gida aka sani sannan kowana su ya koma bakin aikin shi, DPO Sultan ya shiga kira bugu d'aya ya dauka tare da sallama dauke a bakin shi ya ce, "Ranka ya dade yau kai da kanka kake kira na cikin daran nan Allah yasa lafiya" dan shuru Sultan yayi ya ce, "DPO Bilal ina san ganin ka ne yanzu a gida idan zaka ina so ka zo da yaran ka" ok kawai DPO yace, tare da katse kiran aje wayar shi Sultan yayi yana kallon gawar Asiya wadda ke kwance har yanzu cikin honey voice din shi ya ce, "Asiya me yasa zaki min haka bayan sai dana yadda dake cikin bayi na mata, har zuciya ta ta fara rayamin wani abu a kanki sannan zaki min haka me yasa mutanan da nafi yadda dasu suke cutata, idan zan iya tunawa Asiya ke ce mutum ta ashirin dana kashe da hannu na idan anzo kashe ni" yanayin maganar kamar wanda ya zautu, wasu hawaye ne masu zafi suka wanke wa Sultan fuska a hankali Alex ya dafashi yana mashi nuni daya kamata ya zama me dauriya kauda kai Sultan yayi shi kan shi yana ba kanshi tausayi yasan da cewa ko bayin dake gidan su da talakawan dake karkashin shi sun fishi kwanciyar hankali, yaushe ne zan samu *SAUYIN RAYUWA* yaushe ne? goge hawayan shi yayi ya cigaba da kallon kyakyawar fuskar Asiya tare da lumshe idanuwan shi, shi kad'ai yasan radadin da yake ji da lunar abinda ya aikata mata, shigowar DPO ce ta katse mashi tunani mik'ewa yayi  tsaye tare da yima DPO iso turus DPO yayi tare da kallon Sultan ko ba'a fada mashi ba yasan tatsuniyar gizo mata wuce k'ok'i zama yayi sannan Sultan ya zauna tare da mika mashi hannu suka gaisa ya ce, " Bilal na taso ka dadare ko,?
    "haba-haba Sultan ai ba komai tunda dama aiki nane" nuna mashi gawar Asiya Sultan yayi tare da yi mashi bayani d'aya daga cikin yaran DPO ya rubuta statement akan abinda Sultan ya fada gyaran murya DPO yayi ya ce, "to yanzu ya za'ayi da gawar tunda nasan baka so hankalin yan gida ya tashi,"
  "da na yanke shawara ku tafi da gawar gobe sai a mata sutura a kaita makwancin ta,"
      Hakan ma yayi Sultan Allah ya tsare ka daga sharin mak'iya"
    "Amin Bilal"
"Amma fa gaskiya ya kamata securities din ka su dage, ya suke sake irin haka na faruwa" cikin honey voice din shi Sultan ya ce, "ba laifin su bane laifi nane dana ba Asiya yadda ta shiyasa tayi anfani da wannan damar"
      "Toh shikenan kai ma ya kamata ka rage saurin yadda da mutane Sultan please, wallahi aka rasaka anrasa babba mutum" dan smile Sultan yayi ya ce, "k'aramin mutum dai"
    "Lalala kai ke ganin haka amma mu ganin babba mutum muke ma"
   "Toh shikenan"
"Nifa Sultan jiki na bani yake kamar wani a cikin gidan nan ke bibbiyar ka"
"I think so nima, amma har yau na kasa tabatarwa"
  "Toh Allah ya shige mana gaba" "Amin Bilal"
  "Bari na lalla6a na  wuce sani ku dauko gawar mu fita da ita" to suka ce tare da ficewa da gawar Asiya.

SAUYIN RAYUWAWhere stories live. Discover now