SAUYIN RAYUWA

251 2 1
                                    

*Page: 41_42*

Ba komai bane ya jawo wannan murna ba sai kasancewar su suka fara irin wannan aikin a Nigeria sakin Sultan su kayi suna murmushi, amir ya ce, "masha Allah  we did it" gabaki d'ayan su murna suke sannan suka chanzawa Alhaji barau gado aka fito da shi ana fitowa da shi iyallan shi suka biyo gadon da sauri Dr amir ne ya dakatar da su tare da cewa, "ku d'an yi hakuri da shiga dakin yanzu yana buk'atar hutu," daga mashi kai hajiya ikilima tayi tana hamdallah gaskiya ko ta yadda da maganar Alhaji, Sultan babba likita ne  wanda yasan abinda yake, direct waiting room suka wuce da Alhaji barau  tare da sa mashi k'arin ruwa da manna mashi oxygen, sannan suka fito suna ta sakin smile.

Room suka shige kowa ya cire kayan theater dake jikin shi, bashir ne yace, "you guys ni fa banyin break ba  am hungary wallahi," Amir ya ce, ",Nima yunwa nake ji duk da madam ta bani break kafin na fito" Dan siririn tsaki Sultan yaja yana wanke hannu shi a zinc ya ce, "Ku dai kun fiye raki sai kace ba maza ba sai cin tsiya ko auki baku k'arawa, komai ci ci" Sister Naja ta ce, "kai ma ka gani yallabai sai ci ba auki" ta6e baki amir yayi ya ce, "Ni fa ban san surutu kowa ya samu guri ci zaiyi" bashir ya daga kafad'a ya ce, "aiko dai" Sultan yavce, "ok then muje muyi break din first sai kowa ya koma bakin aikin shi," a tare suka jero abin sha'awa suka  wuce gun cin abinci, suna isa suka samu seat suka zauna bashir da amir founded yam with egusi soup aka kawo masu, Sultan da Sister Naja  fish pizza da cottage pie with coffee, cikin natsuwa suke cin abinci, Amir ne ya katse shurun da cewa, "Sultan wai ina ammar ya je ne?  nayi missing nashi kuma ina kira wayan shi baya shiga,"
   "Ya tafi range har yanzu bai dawo ba nima na rasa me ya zauna dashi haka, kamar bai son ya dawo" bashir da amir ne suka had'a baki wajan cewa, "ko dai yayi new crush ne" hhhhhh,
    "I don't think so, kauye ne fa  kawai sai ya rasa ina zaiyi  new crush sai a kauye" Sultan ya fada yana goge bakin shi da tissue, dariya su bashir suka saki tare da cewa, "idan tayi tsami zamu ji" sannan suka tashi kowane su ya koma bakin aikin shi.

                     ****
    Yau ma kamar kullun yaya har kwanar gida ya rako Nihal, yana kallon ta har ta k'urewa ganin shi, dauke da sallama ta shigo gida gwoggo da dilaliya na zaune saman kojera tayani Gulma suna cinikin wasu kaya, har k'asa Nihal ta duka ta gaishe su, kallo daya dilaliya ta mata ta watsar gwoggo ko hannu ta mik'a alamar ta bata kudin ta kudin ta irgo cif ta mik'a mata har sai da ta hada da hannu Nihal wajan amsa dan masifa, hanyar daki Nihal ta nufa gwoggo ta daka mata uwar tsawa ta ce, "ina kuma zaki bayan ga wanki na jiran ki dalla malama wuce ki fara aikin gaban ki," kallon kayan wanki Nihal tayi tana mamaki irin yawan su tun daga na gwoggo har na baffa dana Sara zata wanke gobe kuma na mudi na jiran ta, bakin rijiya ta dawo tana jan ruwa kafin ta fara wankin.

                    *****
Sultan na fitowa harabar Asibiti yan' jarida suka mai cha kasancewa labari ya kai masu a kan aikin da yayi ma alhaji barau babba d'an siyasa mai fada aji, ganin haka ne yasa security's din sultan suka k'araso suna kare shi gudun kar a samu matsala har ya shige mota, a hankali motocin suke tafiya har suka iso gida mai gadi ya wangale masu gate shugowar motocin yayi dai-dai da shigowar motar Nazili 6ale murfi mota tayi, ta fito tare da k'arasawa bakin kofar motar Sultan 6ale murfin motar yayi ya fito, kallo d'aya ya mata ya watsar yayi gaba, riqe kugu Nazili tayi cikin siririyar muryata ta ce, "Sultan.! cak ya ja ya tsaya ta ce, "amma dai kasan haka nan ba zan zo na tsaya bakin kofar motar ka ba ko ina san muyi magana da kai ne," juyowa Sultan yayi ya watsa mata wani kallo na baki da hankali yace cikin honey voice din shi, "yanzu ne lokaci da ya dace muyi magana, ke makauniya ce? yanzu na dawo daga office idan ke baki gaji ba to ni a gajiye na dawo kin gane" jan dan siririn tsaki Nazili tayi tare da shigewa part din ammi da sauri, ammi dake zaune saman three sitar Nazili ta zo wucewa rai bace ko kallon inda ammi take batayi ba ta nufi bedroom din ta, ammi ce ta ce, "Nazili.! cak taja ta tsaya bata juyo ba, ammi ta ce, "waya 6ata maki rai naga kin shigo rai bace," Nazili tace, ba kowa,"
  "Amma shine sai ki shigo rai b'ace kuma ko sallama babu" juyowa Nazili tayi a hasala cikin daga murya cike da rashin kunya  ta ce, "Na ce maki ba komai amma sai wani tanbaya kike a'a tsohowa da ke amma sai san jin k'wak'waf" sannan Nazili ta juyo tana kallon baiwar ta Aziza ta ce, "sai nace ki bude min kofa zaki bude mtsww" da sauri Aziza ta bude mata kofa tare da bin bayan ta, ammi ko girgiza kai tayi ta rasa ranar da Nazili zata daina wannan zafin kan ko da yake k'uruciya ke dibar ta.

Rungume Sultan da kayi ta bayane yasasa sakin murmushi tare da jawo Basmal ta dawo gaban shi tana facing nashi ta ce, "yayana gabaki daya kamanta da little sis naka ko? ta ida zancan cike da shagwaba shafa cheek din ta Sultan yayi ya ce, "Sweetheart ba laifi na bane laifin aiki ne gabaki d'aya ya rik'e ni har yanzu ban samu hutu ba amma kin ga gobe weekend  muna tare kin ji" murmushi Basmal ta saki tare da cewa to yayana sannan ta mashi peck a goshi ta ce, "yayana lunch na jiran ka a main parlour nasa an dafa ma abinda kafi so," murmushi Sultan yayi har dimple din shi na lomawa tare da lumshe idanuwa sannan ya d'an ja cheeks din Basmal yana cewa, "shiyasa nake ji da ke little sis kin san favorite thing's d'in yayan ki, Allah ya baki miji na gari musha biki" rufe fuska Basmal tayi tare da sakin dariya ta ra6a ta gefen Sultan ta wuce, girgiza kai Sultan yayi sannan ya k'arasa shiga part nashi.

  "Ki zo ki cire min takalman nan sun isheni" Nazili ta fada cikin jan magana duk'awa Aziza tayi tana cirewa Nazili takalmi  bayan ta gama cire mata Nazili ta cire kayan ta tare da mik'a hannu Aziza ta bata towel, kwata-kwata Nazili bata jin kunyar cire kayan ta gaban bayi wani lokacin ma su take cewa su cire mata saboda tsabar sangar ta da mulki Nazili ta rai na kowa a gidan, Sultan ne ka d'ai ke gyara mata zama shima dan tana bala'in son shi kuma tana ganin k'warjinin shi sai kuma maimartaba su ka d'ai take gani da gashi toilet ta shiga tare da zura santala-santalan k'afafuwan ta cikin kwamin wanka tare da zame towel din jikin ta lumshe idanuwa Nazili tayi cikin ruwan tana tuno irin kyau da k'warjini na Sultan gabaki daya Sultan ya gama  tafiya da ita, hango irin yadda  Sultan yake smile dimple din shi na lomawa hakan ba k'aramin tafiya da imanin ta yake ba, gashi da bodybuilding kamar shi yayi kanshi, duk wata ya mace mai rai da lafiya zata so samun Sultan a matsayin miji ware idanuwa tayi tare da cigaba da wanka kusan wankan ta na yau duk da tunanin Sultan tayi shi sannan ta fito sanye da bathrobe kan ta nanad'e da towel  zama tayi d'aya daga cikin Royal chair's din ta, ta lumshe idanuwa ko bata fada ba Aziza ta gane massage za'a mata k'arasowa tayi ta fara yi mata massage a hankali gefe ga fruit ana mata tana sha, ware idanuwa Nazili tayi tana kallon Aziza ta ce, "Aziza ni da Sultan ko mun da ce? Washe baki Aziza tayi ta ce, "fadi barna baki, Gimbiya ai wallahi kun da ce musanman shi Sultan din shi za'a cewawa yayi dace  da samun zuk'ek'iyar budurwa kamar ki ga kyau ga ilimi, aiko shi yayi dace babba" far da idanuwa Nazili tayi tare da gutsara gwaba da ke hannu ta.

       Cikin shirin shi Sultan ya fito na Jean's n  t-shirt, t-shirt din black me d'an k'aramin  hannu jean's blue, ba k'aramin kyau ya zubaba kafar shi na sanye da Booth black, sai shek'i yake, direct garden ya wuce, ihu bayi maza ke tashi, iya kar haduwa garden din ya hadu ko ina malale yake da grass carpet, gefe guda kuma swimming pool ne da kujerin shan iska, gefe d'aya kuma kujeri ne na Alfarma, ihu da aka kuma sawane ya jawo hankalin Sultan wajan ya nufa inda fadawa da bayi ke shewa da alamar abinda ake na masu dadi, murmushi Sultan ya saki ganin Ashad ne ke wasa da wuk'a tare da fadawa majiya karfi duk wanda ya bige sai ya fadi ya cinye shi sai bayi da fadawa ke shewa, saboda haka aladar wasan  yake, suna ganin Sultan suka fara zubewa suna kwasar gaisuwa, hakan ne ya Ankara da Ashad kallo d'aya Ashad yayi ma Sultan ya watsar, gabaki d'aya bayin gurin suka dauka da cewa Sultan ya shigo suyi da Ashad daga masu hannu Sultan yayi ya ce, to murmushi Ashad ya saki wanda iyakar shi la66an shi, zaro wuka Sultan yayi ya nufo Ashad yana smile, fara wasan wukar suke cikin k'warewa wanda Ashad da gaske yake  binshi da wuk'ar ganin abin Ashad da gaske ne  yasa Sultan  wani irin juyi tare da dukan habar Ashad hakoran shi da lips din shi suka hade  ya tafi taga-taga Sultan ya kaima k'irjin shi duka da wuka ya fadi k'asa warwas, sultan ya bishi da wuk'a a wuya suna kallon juna ido cikin ido kowana su na maida numfashi  murmushi Sultan ya saki irin na rainin wayau ya ce,"aushh" ya ta6a gefen bakin Ashad wanda jini ya fara zuba, ihu fadawa ne ya dawo da su Sultan murmushi Sultan ya saki tare da mik'awa Ashad hannu ya mik'e, bubuga bayan Ashad yayi ya matso dai-dai satin kunnan shi kamar me rad'a ya ce, "har yanzu da sauran ka, tsakanin ka da *SULTAN SALIM* akwai tazara mai tsaho" sannan Sultan ya biki kafad'ar Ashad yana shu'umin murmushi ya k'ara gaba ya bar Ashad yana binshi da mugun kallo me cike da tsana .

                      *****
  Yau dai Nihal tasha wanki sosai dan kusan sai yamma likis ta gama tana shanya aka fara kiraye-kirayen sallah magrib, ruwan dauraya ta juye a maguji sannan ta shige dakin su, dakin ban da wari ba abinda yake da sauri ta k'araso kusa da umma, tausayin umma ne ya kama Nihal da kyar Nihal ta janyo umma waje sannan taja ruwa a rijiya ta juye abokiti tayi ma umma wanka, sannan ta shige dakin su ta gyara shi fes, gurin umma ta dawo ta dafa  jikin umma, zafi jikin umma yayi rau sakamakon ruwan da gwoggo ta shek'a masu ya haifar wa umma da zazzabi, hakan ne yasa Nihal rudewa tana cewa, "umma na zazzabi ke damun ki sannu kin ji" dakyar ta ja umma ta maida ta daki, sannan ta debo ruwa tare da b'alo panadol  taba umma ta k'ara tab'a goshin ta tace, "sannu umma na"
       sannan Nihal ta fita waje dan dauro alwala.

SAUYIN RAYUWAWhere stories live. Discover now