♡
♡ ♡
_*🐘SAWUN GIWA...!*_
_(The Elephant's Foot)_
_★For How Long Will The Elephant's Foot Be Radioactive?_*FInd out💥*
*WATTPAD*➖ _HAFNANCY01_
*√WARNING🚫:Copycatting is not allowed! Don't transform my book in any means❌❌*
I think you'd like this story: "SAWUN GIWA...!🐘" by HAFNANCY01 on Wattpad https://my.w.tt/nqIZbSkz3bb
__________________________________
_*SHIMFIƊA*_
___________________________________*BABI NA DAYA♡*
↗0⃣1⃣
............Agogo ya nuna sha biyu saura mintuna ashirin na safiyar alkhamis aƙasar saudia ayayin da agogonmu na Najeriya ya nuna tara saura mintuna ashirin,adaidai wannan lokacin Abul-hassan wanda shine ke aƙasar saudia yake waya da budurwarsa dake Nigeria wacce zai aura nan da bayan sallah wanda wata daya ne cif kawai ya rage su zama ma"aurata,Najlat dake kwance saman gadonta tana juyi don dadin hira da masoyinta tace"My Abul wallahi na ƙosa naga na zama mallakinka na har abada,karkaso kaga yadda nake ji tamƙar na matso da bikinmu nan kusa..." lumshe idanu yayi yana jin yadda soyayyarta ke dukan naman zuciyarsa,cikin salon soyayyarsa yace"My Najlee wallahi nafiki ƙosawar son naga mun mallaki juna,ki sani wallahi _*ABUL-HASSAN*_ bazai taɓa iya rayuwa babu _*NAJLAT*_ ba,kamar yadda kowacce bishiya kanyi rassa asama,kuma tayi saiwa aƙasa,haka sonki ya mamaye dukkan jikina,idan na kalleki sai inyi farin ciki,idan naji tattausar muryarki sai nishaɗi da walwala tare da annashuwa gami da farin ciki su mamaye zuciyata,burina ayanzu bai wuci inga na mallakeki amatsayin matata ba,ki zamo tawa ni kadai....."
Fashe masa tayi da wani irin kuka mai tsuma zuciya tana fadin"My Abul ammh kana ganin burinmu zai kai ga cika kuwa...?wallahi acikin ƴan kwanakin nan munanan mafarkai kawai nake tayi akai akai wai wani al"amari mai girman gaske zai hana mana cikar burinmu ta mallakar juna amatsayin mata da miji...."
Ji yayi gabansa ya buga da ƙarfi don tabbas shima hakan ne yake faruwa dashi, wato acikin ƴan kwanakin nan ana nuna masa cewa kamar mafarkinsa ta mallakar Najlarsa amatsayin mata bazai taɓa cika ba, daurewa yayi yace"Najlat haƙiƙa mafarki na gari daga Allah yake, mummunar mafarki kuma daga shaiɗan ne, Wasu zaki samu in sukayi mafarki mara kyau toh sai kiga sun sanya kansu cikin damuwa da tashin hankali su rinka ganin kamar abunda suka gani a bacci gaskiya ne kuma zai faru dasu, Duk wanda yayi mafarki mai kyau Mai faranta rai toh ya godewa Allah, kuma yana da daman ya sanar da na kusa dashi, domin wannan mafarki daga Allah take, adaya ɓangaren kuma Wanda duk yayi Mafarki mummuna, toh Kada ya daukesa da wani mahimmanci ballanta har ya gina wani Hukunci akansa, domin wannan daga shaidan ne, abunda kuma ya dace yayi shine ya nemi tsari daga Allah, sannan Kada ya sanar da kowa shi, don haka next time karki sake gayamun kedai kawai ki nemi tsari daga Allah daga shaidan.sannan kiyi tofi a gefen hagunki, daga ƙarshe sai ki canza wajen kwanciya, inso samu ne awannan lokacin da kikai mafarkin ki tashi ki gabatar da nafila koda raka'a biyu ne.Sa"annan kuma kada ki baiwa kowa labari kuma kada ki sanya damuwa aranki ko kuma ki kullace wani a dalilin wannan mafarkin, ina fatar kin fahimceni koh...?"
"Na fahimceka sosai angon Najlat..." ta fada bayan ta sauke ajiyar zuciya tana mai goge hawayen fuskarta da tafin hannunta, har zata sake cewa wani abun sai kuma taji yace"And that reminds me of something, Najlat bazan ɓoye miki ba kinsa waswasi aranki agame da batun wannan auran namu, kina ganin kamar za"ayi kamar kuma baza"ayi ba, kinbi duk kin takura kanki kinsa damuwa aranki ai dole kita munanan mafarkai mafarkai akan al"amarin, ko baki san da cewa akwai wani ɓangare mai kama da mafarki amma ba mafarki bane...?shi ana kiransa zancen zuci....? Shine mutum zai sanya wani abu a ransa kyakkyawa ko mummuna yayi ta tunaninsa toh inyazo acikin baccinsa ma sai wannan abu yayi ta zuwar masa, Najlat izuwa yanzu yakamata ace kinsan kalar soyayyar dani Hassan nake miki, soyayyar danake miki irin soyayyar da uwa take yiwa ɗanta ne, kinga kuwa soyayyar tasu bata da ranar yankewa, toh ni shi nake miki,A lokuta da yawa, kalmomi sukan gagari furtawa, domin bayyanar miki da adadin yadda sonki yake kara mamaye zuciya ta a kullum. Bana fatan zuwan ranar da zan gaza wajen nemo kalmomin da zan furta miki cewa *INA SON KI* ,Kin zamo ta musamman daga cikin mutane na musamman da na taɓa haɗuwa da su a rayuwata, kin shiga zuciyata kin zauna ta yadda ba zan iya rayuwa babu ke ba, Najlat ki sani babu abunda zai iya hana mun auranki sai wani iko na Allah ko kuma idan ya dauki rayuwata kafin lokacin......."
Kuka sosai ta sake fashe masa dashi tana fadin"Hassan kabar fadin hakan zuciyata tana ƙuna domin kuwa bazan iya jure rashinka ba, ka sani da yardan ubangiji zamu kai ga ganin cikar burinmu, ammh Abul wani irin soyayya ne kakemun haka don naga har kamar naka yaso yafi nawa...?" ta ida magana cike da zolaya, wani kayataccen murmushi ne ya saki kan yace yana shafa kasumbarsa"Najlee bazan iya fassara miki irin son da nake miki ba don wallahi ba fata nake ba astagfirullah! koda ace ayau na wayi gari naga wani akanki kuna aikata saɓon Allah, nasan zanji zafin hakan sosai ammh ki sani bazan iya fasa auranki ba domin kuwa alokacin nema zan kara sonki....."
She was shocked for some couple of minutes, tama rasa abun cewa don gabaki daya wuta ne ya dauke mata,
YOU ARE READING
SAWUN GIWA...!🐘
Romance"Dallah gafara can malama, har ke kin isa ki mana abunda Allah bai mana shi ba? Akanki ne aka Fara irin hakan? Ko kuwa akanki ne za'a daina? Sai wani ciccika bak'in banza kike awurin kamar zaki iya tabuka abun kirki idan har mukayo gaba da gabanta...