02

310 7 0
                                    


♡ ♡
_*🐘SAWUN GIWA...!*_
_(The Elephant's Foot)_


_★For How Long Will The Elephant's Foot Be Radioactive?_

*FInd out💥*

*WATTPAD*➖ _HAFNANCY01_

*°DEDICATED TO:-Mamina (Sis Nerja'art & Yayata (Ummudilshad)*

_*•SPECIAL GIFT TO:-Tawar (Maman Kausy)*_

__________________________________

*BABI NA BIYU♡*
___________________________________


↗0⃣2⃣

.............Tana fita ta tsaya awajen Ali me saida kayan itatuwa dake ah tsallaken gidansu, ta had'awa Hajiyar Abul kayan marmarin dubu d'aya sa'annan sauran dubu biyun ta b'oyeshi da nufin soma bawa Danlami kudin gyaran waya kafin cikon ya biyo baya, duk da cewa bata da tabbacin wayar zata tashi ammh ya zama dole ta jarraba watakila adace don batason ko kadan Abba ya farga da abunda yafaru don sosai za"ai tashin hankali agidan muddin ya sani, Zaman lafiya da kuma fahimtar juna shine abunda take buri akodayaushe duk da cewar su ba haka suke son ba, sunfi qaunar ata tashin hankali akowacce dakik'a dake tafiya arayuwa, ai kuwa Ali ya k'yauta mata don har kara mata lemu k'wara uku yayi, sosai ta cika da farin ciki tana mai k'ara yabawa halin kirkinsa, hannu biyu tasa ta karbi katuwar ledar tana sake jaddada kalmar godiya agaresa kan ta juya ta nufi hanyar gidansu Abul wanda yake abayan nasu gidan, doguwar katanga ce kawai ta raba tsakaninsu, akan idanun Najlat ta fara siyayyar har ta gama ta wuce ba tare da ita Ummin ta ankara da lek'en da take tayi daga kofar gida ba, kwafa tayi tace''Don iyayenki zaki dawo ki sameni ne, zaki gayamun koda dubu daya ne kacal dama zaki siyemun mutuncin da kuma soyayyar dangin mijin da kike ta hayagaga akai..''
Ta karashe maganarta gami da jan dogon tsaki, sakin k'ofar tayi bayan ta daina hangon bayan Ummin, ta koma ciki tana masifa rike da mafici ahannunta tana firfita kai kace ko matar wani sarkin ce, ga wani shegen iyayin tsiya da yanga kamar wacce bata kashi, sai wani jujjuya duwaiwai take gata bawai gadon uwarta tayi ba, don ita sambal take tamk'ar kara aka zurawa kaya, sai aukin k'yan d'an maciji, ita kuwa Ummi ba wani k'yan ne da ita ba don bazamu kirata da k'yakkyawa ba haka zalika bazamu ce ita d'in mummuna bace, sai dai ta tara package gaba da bayanta kuwa, da wannan kadai Najlat ke kishi da ita don ji take inama ace itace da jikin hutu irinna Ummin..?

........Wani irin wawan ajiyar zuciya Musa mai kati ya sauke wanda ya d'an tsoratar da Ali, kallonsa yayi yace''Kai Malam lafiyarka kuwa zaka sa mutum ya zura aguje da wannan wawan ajiyar zuciyar..?meya faru ne halan..?''

''Wannan yarinyar ce wallahi Ummi, wallahi yarinyar tana burgeni, ina masifar son kalar hankali da nutsuwarta...ba don za''ace na zage da yawa ba da sai ince kakaf unguwar nan babu mai irin kamun kanta...'' Ya furta da iya gaskiyarsa yana mai lumshe idanu, dariya mai kayatarwa Ali ya saki yana mai rike ciki kan yace''Anya mutumina wannan yabawar tayi yawa kodai kana ciki ne sai mu shirya zuwa dare amana sallama da ita...?''
Waro idanu waje Musa yayi yana fadin''Wah???dan Allah rufan asiri, Ka bari in mutu agida maza su binneni, Ummi ai ba kalarmu bace, zubinta kalar manyace irinsu Abdulhameed Tukura don yasin ni ina hangowa yarinyar nan kwanciyar hankali da jindadi nan gaba, kuma billahil azimu ba karamin murjewa zatayi ba idan tasamu gidan miji, Allah dai ya gaggauta had'ata dana gari tayi tabar gidan wahalan nan....'' Ali ya amsa mishi da Amin, daga nan suka bud'e faifan Najlat da Ummanta akan Zaluncin da Ummin take sha ahannunsu domin kuwa kakaf unguwar nan babu wanda baisan da labarin irin musgunawar da suke mata ba, Allah ya wadaran da kuma Allah ya saka mata shine abunda kawai kake ji na fita daga bakunansu...



.........Ah farfajiyar gidan ta hango Hajiyar Abul tare da k'anwarsa Nana zaune kan kujerun robobi, da alamun ma basu wani jima da dawowa daga unguwa ba sabida hijaban da suke saye dashi ya tabbatar da hakan, tana iya yiwuwa ma daga asibiti suke domin kuwa yamutsassiyar fuskar Hajiyar ya tabbatar da hakan, ga dukkan alamu jikin ne yadan motsa mata, Tunda tashigo cikin gidan duk suka zuba mata idanu cike da shauqin qaunarta, bama kamar Hajiyar wacce ji take inama ace Ummi Zainab d'iyar data tsugunna tayi kashi akanta ne, sosai hankali da natsuwar yarinyar ke burgeta, uwa uba tsantsar kulawar da take gwada mata, bata tsammanin ko uwar data haifeta ta samu irin kulawar da take samu awajen Ummin, inama ace itace sirikar tata ba Najlat ba d'iya wacce tayi hannun riga da mutunci..?Inama ace Ummi itace wacce Abul d'inta zai aura nan da kwanaki kadan masu zuwa...?inama inama.....
Ummin ce ta katse mata tunani da take gayar da ita, firgigit! ta dawo daga duniyar tunaninta babu shiri, cike da fara'ah ta amsa mata''Lafiya qalau baiwar Allah jiki alhamdulillah da sauqi yanzu ma muka dawo daga asibiti, kinga ma magungunan da suka tuttulo mun can ahannun Nana...'' ta fada tare da mata nuni da bak'in ledar dake hannun Nanar, baiwar Allah take k'iranta kamar yadda dai take k'iran Abul da bawan Allah, cike da tausayawa tace''Allah sarki Hajiya Allah baki lafiya, Allah yasa kaffarace..''duk suka amsa mata da ameen, tashiwa sukayi suka shiga ciki, ah kataran falon suka zauna akan tattausan kujeru na alfarma, sosai Ummi ta damu da wannan rashin lafiyar ta Hajiya, bayan ta kwab'e hijabi Ummin tasa hannu tana tab'a wuyanta, jikin yadan dau zafi, arud'e take fadin''Nana dan Allah taimaka ki dan zubo ruwa ah bowl da karamin towel ki kawo in mata wiping jiki watakila adace zafin jikin ya ragu..''

SAWUN GIWA...!🐘Where stories live. Discover now